HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE TWENTY-FIVE

826 70 1
                                    

Sabuwar tsokana Ya Nuratu ta samun tana dariya. A.Laila tace "Aw ba dai sirikin nawa ne yazo ba?" Ya Nuratu tace "shine mana A.Laila bakiga sai wani blushing take ba" A.Laila tayi dariya tace "kun dai sa mun yarinya a gaba don Allah ku kyaleta haka! Zara tashi kije kar ki barshi yana ta jira ba dadi"
jikina a sanyaye na mike na zura slippers dina zan futa! cikin daga murya A.Laila tace "ke meye haka? dawo nan!'" na dawo ina mata kallon rashin fahimta! cewa tayi "haka zaki tafi? wannan shigar batai mun ba koma daki ki sauya wasu kayan ki danyi make up mana!to look more presentable!" har zanyi magana Ya Mahmud ya kalleni tare da mun magana da ido! na juya a hankali na shiga daki! abaya kawai na ciro wadda aka watsawa swarosvki stones jajaye a jikinta samfurin Zara Couture na saka! na fente lips dina da red jambaki na fesa turare na futo! "yauwa Masha Allah! Masha Allah!! ko ke fa? oya! maza jeki!" na wuce zan tafi Ya Nuratu tace "kuma ki hawo mana dashi mu gaisa don nasan halinki sai ki iya barinshi ya tafi" ko juyawa banyi ba balle na bata amsa na wuce na futa suna sake mun dariya! sai da na shiga wajen Dada muka gaisa da ita da Mami sannan na futo na shiga lift na sauka reception!
A hankali nake tafiya kirjina yana ci gaba da bugawa har na isa bangaren da aka shirya kujeru don hutawa! zaune na ganshi cikin bakaken suit wanda sukai ainihin futo da kyawun sa! waya yake ta faman dannawa cikin sauri ya bada dukkan hankalinshi akai da alama wani abu mai muhimmanci yakeyi! sai da na karasa dab dashi kamshin turarena ya sanya shi dago ido!
gabadaya hakoranshi talatin da biyu ya wangale yana murmushin da kowa ya san shi da shi a mafi yawancin lokuta! "you are welcome beautiful!" ya fada yana mayar da wayar cikin aljihun wandonshi! zama nayi a kujerar da ke gefen tashi ina cewa "kai zanyi wa sannu da kazo yau! ba ka gayamun zakazo ba! daga Paris ta taho nan?" gyara zama yayi yace "daga Paris London na wuce nayi clearing wasu abubuwa sannan na taho nan! kinganni daga Airport fa na taho nan! dan zaro ido nayi nace "lafiya toh? meyasa?"
murmushi yayi yace "lafiya kalau! i just miss you!" kasa nayi da idanuna inajin wani irin rashin dadi! ban taba son wani ba a rayuwa! Imam ya shigo rayuwata dai dai lokacin da nake bukatar abokin rayuwa sannan yayi wata katuwar nasarar siye zuciyata da kyawawan halayensa da so da kulawa! ranar da na fara ganinsa na soma sonsa!daga lokacin kuma da na gano nagartarsa da saukin kansa sa kulawarsa da tausasawarsa soyayyarshi take ta karuwa acikin raina har nakejin babu wadda ta kaini sa'a a duniya! inason Imamu son da ni kaina nake mamaki don ba taba hasashen zanso wani haka ba! a dai dai lokacin da komai ya yi daidai magana tayi karfi soyayya tayi zurfi tsanina dashi a lokacin wannan babban al'amarin ya kunno kai! ashe wai Aisha na da irin burin da nake dashi akan Imam cikin ranta tsayin lokaci! Ita kuma Aishan wata mutum ce a rayuwata wadda banajin akwai abinda ba zan iya sadaukar mata ba komai girmanshi komai son da nake masa don nayi imani itama a shirye take! da taji ina neman abinda take da iko da shi ta dauka ta bani ko kuma ta nemo mun shi duk inda yake! ko kuma ta tayani nemanshi a ko ina yake! to ya zanyi da wannan babbar kaddara da kunno mun kai! inaji ina gani zan hakura da abinda nafiso domun farin cikin yar'uwata, aminiyata Aisha!
"hellooo! are you okay?" Imam ne ya katseni! da sauri na dago ina cewa "babu komai! ya kake? yasu Mummy?" yace "suna can Nigeria suna ta shiri" nace "shirin me kuma" murmushi yayi yace "Wanne shirin zasuyi bayan na aurenmu! yanda kikasan gobe ne auren kullum da abinda zasu futa yi! Visar Mummy ce ma bata futo ba da tuni sun tafi America" ji nayi cikina yace wani "kulululu" yaci gaba da cewa "programs din da suke shiryawa wajen kala nawa inaga sati biyu za'ai ana buki! tun daga Pre wedding dinner! tunanina ya za'ai abokaina suzo su kwashe wannan lokacin bayan kowa yana da abunyi" girgiza kai nayi ina sarawa hankali irin nasu Mummyn tashi bana ce hauka ba! kamar wanda ba'a taba biki ba sai a kanmu? suwaye suke da lokacin halartar biki har sati biyu? idan ma mutum ya rasa abinyi da kudi kawai sai ya soma almubazzaranci da su! a fili kuwa daurewa nayi na kalleshi nace "sati biyu ai yayi yawa ina laifin ma sati daya?" daga kafada yayi yace "kema dai kya fada! Mummy ji take kamar ba'a taba biki ba sai akan wannan! duka family ma kowa shiri yake don bamu cika buki ba sai an dau lokaci! bamu da yawa sosai! kusan kowa an mishi aure sai yara masu tasowa! sai su Yasmin!" girgiza kai nayi don naga alamar hakan!
muna zaune muna hira bayan nasa an kawo mana shayi da dan snacks! sannan nace masa ya hawo ya gaida su Dada! cewa yayi "Haba! da wannan shigar? bakisan ba'a zuwa gaban surukai da kananan kaya ba? surukai ma irin na Hausa Fulani" cewa nayi "me kake nufi toh? ba zaka je ba kenan?" fadada murmushi yayi yace "Gobe insha Allah zanzo mu gaisa! kinga yanzu ya kamata naje hotel na kai kayana na huta ko? driver na waje tun dazu yana jirana!" ajiyar zuciya nayi sannan nace "toh meyasa baka fara zuwa ka huta ba sannan kazo gabadaya?" cikin sauri ya amsa "saboda na kagu nazo naganki" nayi murmushi kawai! da haka na rakashi bakin mota ya shiga ya tafi! ina shigowa ciki na gamu da Ya Mahmud zai futo! cewa nayi "La futa zakayi?" kallona yayi a nutse yace "gani nayi shirun yayi yawa na sauko nagani" da murmushi nace "Ya Mahmud kamar wanda zan bata?" shima murmushin yayi yace "ba zaki bata ba! yana ina ne? daga ina kike?" cewa nayi "ya tafi! rakashi nayi" rage far'a yayi yace "meyasa baki hawo dashi sun gaisa dasu Dada ba? me yasa kike hakane Zara?" cikin sanyi nace "Laaa Ya Mahmud wallahi na gaya mishi ya hawo su gaisa yace ba zai iya shiga wajensu ba da manyan kaya ba sai gobe zai dawo" wani irin murmushi hade da smirk Ya Mahmud yayi sannan yace "Imam din ne yace ba zai iya wajen su Dada da shigar kananun kaya ba?" yanda yayi murmushin da maganar sai naga kamar akwai wani da ya sani akan Imam yake boyewa! a hankali nace "Ya Mahmud please me ka sani game da shi? na lura shima kamar yana boye wani abu a tsakaninku ko dai kunsan juna ne?" nutsuwa yayi yace "Ni da nake London shi yana Nigeria how do you expect me nayi mishi sanin da ke baki masa ba? a ina zan gan shi?" cikin zuciyata nayi tunanin kuma fa hakane! amma meyasa idan sun hadu Ya Mahmud ke mishi wani irin kallo! shikuma sai naga Imamun yana wani sunkuyar da kai yana basarwa wanda ke nuna alamun kamar akwai wani abu a tsakaninsu? ajiyar zuciya nayi na bar tunanin domin na kasa gano amsar tambayata! "tunanin me kikeyi?" girgiza kaina nayi! ya wuce gaba muka koma ciki!
kujerun da muka taso da Imamu muka koma muka zauna kafin order abincin da Ya Mahmud yayi daga restaurant yazo! sannan muka shiga lift zuwa suit din da muke!
gabadaya sun sake yin wata da'ira a falon harda Dada da Mami an baje kayan abinci a tsakiyar falon ba'a bude ba!
Daure fuskata nayi tamau don kar su samu damar tsokanata amma sai da Ya Nuratu ta mike tana wani kalle kalle! ya Sadik yace "ke kuma leken me kike?" cewa tayi "sirikin namu nakeson gani? ko ba zai zo ya kwashi gaisuwa ba?" cewa nayi "gashinan hawowa ki shirya" ta zata dagaske nake tai maza ta dauko air freshener din "Aqua" ta feshe wajen da shi tana cewa "Ya Sofi ku taso mu tattara kayan abincin nan mu gyara wajen! Ya sofi da Ya Anis har da Ya Omar suka shiga tattara kayan abincin suna mayarwa dinning! Ya Mahmud ya koma gefe kawai yana murmushi! sai da komai yayi tas kowa ya kame a inda ya dace dashi sannan tace "toh ki koma kiyi masa magana mana" na juya ns futa kamar gaske! sai dai a maimaikon kiran nashi sai na shiga kitchen na debo mana plate da su lemo na dawo!
A.Laila ce tace "yana ina? " Ya Nuratu ta sake gyara zaman mayafin abayar da ta nade kanta dashi tace "Malama kice masa ya shigo kin barshi yana jira yau naga shashashar Amarya! haka akace miki anayi?" murmushi nayi na shimfida ledar cin abincin hannuna na aje paper bags na abincin mu nace "Ya Mahmud zai huce" Dada da ke can cikin falon daga gefe da Mami da A.Laila ce tace "bafa wani Imamu da zai shigo! tunda ta ba Nuratu amsa nasan karyane ba shigowa zaiyi ba! shakiyancinta ne kawai ya motsa" Ya Mahmud yayi murmushi yace "Dada kin lakanci halin tsokanar Zara da kyau" bansan lokacin da na kalli su Ya Nuratu na kyalkyale da dariya ba! da gudu ta taso zata kai mun duka na koma bayan Ya Mahmud ina mata dariya!
kareni yayi yana ce mata "Babu abinda zaki mata! kullum da dadi kuke sata a gaba kuyi ta tsokana? gashinan son gulma da sa ido ya saku aikin banza! shi Imamun ma ya dade a hotel dinsa yanzu!" ba karamun haushi na hadawa su Ya Nuratu ba! haka suka tashi suka sake kwaso kayan abincin Dada na bada labarin ranar da na daukarwa Ya Omar mota na futa bayan yasa an wanke mishi motar zai je wajen Safiyya!

Washe gari kam ban koma bacci ba! don Imamu yace da wuri zai zo kuma gobe zai tafi! wanka nayi na shirya! muka gyara ko'ina da Ya Nuratu bayan anyi breakfast! sannan Dada ta futo! duk muka hallara a babban parlour kamar yanda aka saba! wayata ce ta soma ringing na mike na shiga daki har Ya Nuratu na cewa gashinan yazo! A maimakon Imamu sai naga Aisha! da sauri na daga na kara wayar a kunne!
"heyy bestie! ya kike?" shashshekar kukanta ne ya fadar mun da gaba naji wani irin firgici! "me ya faru Aisha? me akai miki?" bata daina kukan ba kuma batai mun magana ba! "Aisha you are scaring me please! me yake faruwa?" dakyar na shawo kanta ta soma magana cikin kuka!
"Zara Daddy ya hana tafiyata school gabadaya yace bazanje ba" duka idanuna na zaro cikin firgici! domin aibabu wanda yafi kaunar tafiyar irin shi! tun muna JS1 yake cewa Aisha Harvard zatayi! yaci buri mai tsanani akan karatunta toh sai da ya kammala kashe wadannan makuden kudade tafiya saura kwanaki uku zai ce an fasa? dakyar na hadiye yawu nace "Aisha me kikai masa? meye ya bata masa rai? meyasa ya yanke wannan hukuncin?" cikin kuka mai tsanani tace "bansani ba Zara! amma komeye yana da alaka da result din da ya futo na asibiti! bansan me suka ce ba! tun jiya da mukaje karbar result din likita yace na basu waje da ya futo naga fuskarsa ta chanja! har mukaje gida bai cemun komai ba suka shiga daki da Umma! shikenan itama ta shiga cikin damuwa! sai dare Daddy ya kirani yake cemun wai zancen makaranta na hakura sai nextyear in Allah ya kaimu!A madadin haka ya shirya mana tafiya zuwa America! duk yanda naso nayi magana bai bani dama ba yace kawai nabi abinda yace bayason kowanne magana! Zara ya zanyi? meyasa rayuwa take mun haka?ya zanyi da raina? kinsan yanda nake dokin tafiya makaranta na bar kasar nan? wlh ji nake kamar akan kaya nake Zara! banajin dadin rayuwata!





HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now