HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE THIRTY-FIVE

836 59 8
                                    

Bayan mun kammala gyara dakin da muka bata munyi wanka tare da sauyawa zuwa kayan bacci ne muka shiga aikin futar da kaya! kayan buki, cikin katuwar box! kwalayen takalmana, purses, da sauran accessories din da zanyi amfani dasu duka wajen daya! daya akwatin kuma traditional attire dina ne kala biyu na ingantaccen sakin fulani, bayan tailolin Mami sun shirya masa tsararren dinkin iro and buba sai suka bi saman gaban rigar da adon gashin dawisu! yanda aka shirya dinkin dole ya baka sha'awa! wannan shi zan saka ranar Kamu sai dayan kuma kawataccen hand beaded ashoke ne gold colour wanda zan sauya bayan na cire wancan traditional fulani attire din da za'aimun kamu da shi! Cikin murmushi Aisha ta bude rigar tana cewa "Zara i can't wait naga kayan nan a jikinki! ban taba ganin kalan da yake miki kyau irin gold ba, musamman idan Banke tayi magic din nan nata akan fuskarki! Allah this year amare zasu sha kunya idan suka ga shirinmu" dariya nayi sosai sannan nace "Aisha tawa! ya kukayi da Banke din ne? ni ban tambayeki ba!" hararata tayi sannan tace "ke wa yake ta taki! tun ranar da aka saka date din bikinki nayi booking! i wanted it to be a suprise gift, amma kawai Ihsan ta ruguza mun shiri ta kama ta gaya miki!" wasu kwalla naji na niyyar tahomun na tausayin Aisha! bana mantawa a waya muka ga bridal looks na wata amarya wadda banke tayiwa make up ta saka a shafinta na instagram. nace Aisha In sha Allah da bikina matar nan ce zatai mun make up! i love her simplicity and uniqueness! wai ashe ta rike a ranta ta yi alkawarin in dai na tashi aure zatai suprising dina da ita! Duk da yanda auren yazo ba yanda muke buri ba Aisha ta tsaya tsayin daka wajen planning din komai yanda ake bukata! bata gajiya bata tuna kanta idan tana hidima a gareni! bansan wanne irin so take mun ba!

Murmushi nayi lokacin da na tuna nawa suprise din da na shirya mata wanda bazan nuna mata ba sai ana jibi a fara buki! mun dade muna wannan aikin kafin mu hada komai inda ya dace mu sake gyara dakin! sannan muka sa hakarkarinmu akan shimfida muka kwanta! mintina biyar bayan rufe idona naji Aisha tace 'Zara! Zara kinyi bacci?" a sanyaye nace "idona biyu!" itama a sanyaye tace "Zara will i continue to be the first person da zaki gayawa damuwanki ko matsalanki idan ya taso bayan kinyi aure? ina fatan ba zaki sauya mun wannan wajen ba, don Allah Zara komai kankantar matsala kada kiyi shiru, kada kiyi tunanin zaki magance ta ke kadai, kada ki barta a ranki, ki dinga tunawa cewa akwai ni! ki saka a ranki ko zaki gayamun damuwa guda dari kullum bazan gajiya da sauraranki ba, bazan yi kasa a guiwa wajen baki shawara ba, idan ma abun yafi karfina toh zan kai kukanki ga Allah wanda yafi karfin kowa da komai Zara, idan na kuka ne ki kirani muyi kukan tare, idan na dariya ne ki kirani muyi dariyan tare, dan Allah promise me you won't change my place in your
heart Zara! nasan ni naja miki komai, amma......." kukan da take hadiyewa ne ya fuzgo kansa tare da futowa da karfin gaske, har sai da ta bani tsoro! tashi nayi na zauna inajin me zanyi nima nayi kukan naji sanyi! oh!! My Lord! i just wanna cry out all the heavy loads i have been carrying cikin raina kaman yanda take yi, wata kila radadin da nake ji zai ragu!. ok but not this time,i have to be strong for my friend. A hankali na soma bubbuga bayanta cikin sigar lallashi kafin na soma magana!
"Besty meye haka wai? zaki karya mun guiwa ne kuma? ina kece support dina a yanzu? to idan kinamun kuka ni kuma me zanyi? ki kwantar da hankalinki tunda muna addu'a ni ina da tabbacin Allah ba zai kyalemu haka ba! Allah muka mikawa lamarinmu kuma shi ne kadai yasan yanda zaiyi damu! ni na karbi kaddarar auren Imamu ko ya yake Aisha da zuciya daya! kuma ina da yakinin cewa Allah zai sauya mun shi zuwa nutsatstse kuma shiryayyen nagartaccen mutum idan har Ya rubuta mun zama na dashi me alkhairi ne! addu'ar da muke Aisha da babu abinda Allah yake nufi akan aurena da shi da tuni maganar ta watse! kada muyi wa Allah shishshigi, komai yayi tsanani sauki ne zai biyo bayanshi! komai yayi zafi maganin shi Allah! please Aisha ki daina kuka, ki daina karyamun zuciya! i have made my mind, kuma ina rokon taimakon Allah! ke dai ki tayani da addu'a kawai shi nake so! And i will never ever replace anyone with you har karshen numfashina! zaki ci gaba da zama aminiya kuma yar'uwar da babu kamarta! I promise you! i promise!

Bazan iya kayyade lokacin da na dauka cikin bayanai da nasihohi irin wadannan ba kafin na samu Aisha tayi shiru ta daina kukan da take yi!
"Yanzu tashi muyi alwala muyi nafila, karfe uku ne na dare, Allah baya mayar da bukatar da aka mike aka fuskance shi aka roka a wannan lokacin! babu musu ta mike ta shiga toilet tayo alwalan sannan nima na shiga nayo tawa! in takaice muku ranar nan bamu runtsa ba ko na mintina, muna having sisters time! Wasu maganganun ma tsakaninmu ne kawai ko ku masu karatu bazan iya bayyanawa ba!
bayan munyi sallar asuba mun kammala azkar dinmu bamu koma bacci ba! wata hirar muka sake daukowa ta daban akan makowar karatun mu! Daddyn Aisha na nemar mata wani gurbin karatun a Middlesex University zata karanta medical science and technology! nayi mata matukar murna domin karatun zai debe mata matukar kewa! nima mun fara magana da Imamu akan The American University of Paris da yake mun sha'awar tafiya! tunda shima akwai babban reshen su a Paris din, zama can ba zai masa wahala ba! Amma bamu zo matsaya akan maganar ba, balle kuma mu saka manya ciki! nice ban baiwa maganar muhimmanci ba don a tunanina hakan na daya daga cikin shiryayyun plans dinsa! Inajin tsoron Imamu kuma bana mamaki ko tantama akan duk abinda akace zai aikata akan kowa ma!
Mune nan zaune har lokacin breakfast hirar bata kare ba kamar yau muka soma ganin juna inji Mami! cikin dakin Aya ta biyomu da breakfast mukayi, ni kaina ina mamakin wannan hira tamu ta yau da taki karewa kamar wanda zamu rabu zuwa nahiyoyi daban daban! Muna gama wannan maganar zamu dauko wata. sai da Jainaba mai mun gyaran jiki ta shigo har dakin ta tasa keyata sannan muka hakura!

Bamu kammala ba Ihsan ta iso gidan, lokacin kuwa babu kowa sai mu don su Mami wataran basa break din suke futa wataran kuma suna kammalawa! kamar akaina za'a soma buki a garin Abuja.
Dakyar na kwato kaina daga hannun Jainaba na shigo daki inda Ihsan da Aisha ke ta magana kasa kasa wadda na tabbatar akaina ne! banza nayi da su na shige toilet nayi wanka na futo daure da towel! still na tsaya gabansu ganin irin kallon da suke mun! "Lafiya  bayin Allah?" Ihsan ce tace "kinga kuwa yanda kika koma Zara? do you look at yourself cikin mirror kuwa? kinga yanda skin dinki yayi? tabdi! ai wallahi nima matar nan sai ta ganni ko na kwana daya ne! gabadaya kin koma wata kamar ba ke ba!" tsaki nayi na girgiza kai don na tabbatar idan na tanka shakiyanci zasu shiga yi mun wanda zan kasa kwatar kaina daga hannunsu! Duk tsokanar da suke mun ban tanka musu ba har na kammala shirina cikin gown din yellow voile mai manyan pattern! na nade kaina da karamin fashmina. sannan na dauko jakata da key nazo gabansu na tsaya! "Idan kun gama ku taho, idan kuma kuna nan ni na tafi" cikin dariya Ihsan ta mike tana cewa waye yake fada da amarya ai sai mahaukaci! lallabaki zamu dinga yi kamar kwai har sai mun kaiki  gidan gilashi lafiya(sunan da suka sakawa gidan da zamu zauna da Imam kenan, domin kusan rabin gidan da glass akayi shi) bance komai ba nayi gaba suka biyoni.
"Ah! ina motar ki Ihsan?" na tambaya ina duba parking space; din babu alamar motarta! a sanyaye tace "Faisal ya hanani driving! shi ya aje ni idan na gama zai dawo ya daukeni" murmushi nayi bance komai ba na danna luck din motata da remote din hannuna ta bude! baya ta bude ta shiga Aisha ta zagaya gefena sannan na tada motar muka futa!  ina barin gate din na dau titi Aisha ta soma magana "kunsan kuwa jiya wani mafarki da nayi?" Ihsan ce tace "ina fa zamu sani baki gaya mana ba" ni ban ma yi magana ba don nasan watakila wata tsokanar zata mun! cikin nutsuwa tace "ba zancen wasa ba Ihsan wallahi mafarkin da nayi jiya ya bani mamaki sosai har yanzu ina tunanin shi" sai lokacin na dube ta tsaf sannan na maida hankalina ga tukin da nake nayi nace "Ki gaya mana toh kin tsaya jan rai! mafarkin me kikayi?" cikin muryar mamaki ta sake cewa "mafarkin Aljanna nayi" Nida da Ihsan muka kyalkyale da dariya lokaci daya! Aisha ce ta hade rai tace "aww mahaukacciya kuka mayar da ni?" Ihsan ce ta guntse dariyarta tace "su wane mu zamu mayar da ke mahaukacciya? bamu musha don Allah labarin gidan aljanna!" tsaki tayi ta juyar da kanta muna ci gaba da yi mata dariya! mintina arba'in da biyar muka isa gidan Rabecca! wadda muka baiwa order ta shirya mana souvenir din kawayenmu! Aikinta kenan wanda ta kware akai sai sai bala'in tsada.

Awan mu daya a gidan tana nuna mana abubuwan da ta hada tare da bukatar shawarar mu akan yanda muke so ayi packaging dinsu! Ta bude computer tana nuna mana samples muka zazzaba sannan Ihsan tayi mata transfer din ragowan kudinta! Ihsan ce ta dauki nauyin wannan bangaren, da aljihunta! Tabbas na samu aminai kawaye masu kaunata tsakani da Allah!har rige rige suke wajen faranta mun da abubuwan da suke tunanin zasu sakani farin ciki! Tunda bikin nan ya karanto babu me zama acikinsu, babu me lokacin kansa, da karfinsu, da kudinsu da lokacinsu duka sun sallama a kaina don ganin komai ya tafi dai dai kuma sun fidda ni kunya! babu abinda zancewa Allah sai godiya!

Bayan mun futo daga gidan Rabecca ne Ihsan tace mu wuce "Tulip Bistro" muci abinci! a nutse na danna signal din shan kwana ina cewa "a'a ku idan kuka liqewa waje guda daya sai kowa ya tsane shi! Toh Gidanmu zamu je zanga Dada, koma me kike so Baba Rabi zatai miki" cikin murna Ihsan tace "kin tunamun wallahi, danwaken Baba Rabi tashin hankali ne! dariya nayi tare da duban Aisha wadda yanayinta ya sauya tun lokacin da tace tayi mafarkin Aljanna muka yi mata dariya! sai naji banji dadi ba, amma nasan halin kayata, ba zata fada yanzu ba tunda bamu saurare ta lokacin da takeson fadin ba!
ana kiran magriba muka shiga gida. don haka sallah muka soma yi, bayan na gayawa Baba Rabi tayi wa Ihsan danwake, nida Aisha kuma faten doya! a dakina na barsu na isa dakin Dada, tana bakin gado tana waya, don haka na nemi wuri kasan lallausan shudiyan rug din da ke gaban gadon na zauna!
"wannan maganar mai muhimmaci ce a wajena don haka abar ta sai na ture hidindimun da suke gabana, sannan ko da wasa bana bukatar ka sanya wani cikin maganar! kuma inason kwakwkwarar hujjar da kake da ita akan abinda kake shirin yi? saboda muna son shi ba zaiyu mu tauye wa yan'uwansa hakki ba tunda dai bashi kadai bane ," A hankali na juyo na kalli Dada don jin furucin da take yi cikin tsananin nutsuwa da maida hankali ga maganar, ko wacce magana ce wannan? akan wa kuma akeyi oho!" tunanin da na tafi ne ya hanani jin karashen maganar sai da ta dafani tana cewa "Zahra'u tunanin me kikeyi?" ajiyar zuciya na saki a hankali kafin na ce "babu komai Dada! Mami tace kina nemana"

Do you smell something coming up?
ok! crack your brain, me zai faru ne ga wannan aure? za'a yi ko kuwa?
Note maganar da Dada take yi a waya domin mai matukar muhimmanci ce nan gaba! This is just the beginning!
stay tuned!!

Ma'assalam!

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now