HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE TWELVE

879 63 2
                                    

A tsanake na dubi Ihsan "tsakanina da Aisha is a long story
amma abinda zance miki shine tunda muka taso muke tare kwana kawai ke rabamu. Duk inda zan gaya miki shakuwa da kaunar da ke tsakanina da Aisha sai na rage miki wani abu. Bama iya awa biyar bamu ji halin da juna ke ciki ba. Duka damuwarta ni take gayawa nima duka damuwata ita nake gayawa. Makarantar mu daya ajinmu daya komai na rayuwarmu iri daya. Sai bambamcin hali da kamanni kawai. Don ita tana da sabo da magana da barkwanci nikuwa ban cika son mutane ba.
To cut story shot Aisha is my sister from another mother. ita na fara na kira na gayawa mun hadu da Imam tayi matukar murna da jin hakan kuma! saidai ranar da suka fara haduwane naga wani irin tashin hankali mamaki da kuma tsoro a idonta amma kafin nayi wani abu tuni ta shanyesu ta aro nutsuwa da kamewa ta cike gurbinsu da su. duk yanda naso na fassara dalilinta na yin hakan na kasa har na hakura na bar abun cikin raina. haka rayuwa taci gaba Har akasa mana rana da Imam yanzu saura six months bikina dashi. Na dade da fara gano wani boyayyen al'amari a tsakaninsu. Amma sai na kawar da tunanin a raina ina ganin kamar kishi ne yaimun yawa. Idan muka zauna tare su kadai suke hirar kasancewar ni ba mai son magana bace. Kullum muna waya bamu da hira sai ta rayuwarmu da kuruciyarmu da Aisha. Kullum sai ya tambayeta. Ita kuma sai na soma observing ta sauya gabadaya bataso su hadu da shi idan zaizo na kirata muyi masa girki ko mu futa tare sai ta kawo wani excuse tun bana damuwa har na soma zargin wani abu. Amma yau kam Ihsan abun ya bani tsoro da mamaki. Na kirata fa yau da safen nan mace mata Imam zai dawo tazo gidanmu ta tayani nayi masa cincin tace mun ba zata samu dama ba tana da ayyuka. Toh a ina ta ganshi? A ina suka hadu ya dauko ta a mota? Meyasa zasu zo mun tare? I'm confused Ihsan i dont know what to do"  patting bayana ta shiga yi tana cewa "issokay Zara. Insha Allah zamu gano komai..zamu bi komai a hankali kuma zamu gane bakin zaren don Allah ki daina damuwa dayawa ki kwantar da hankalinki. Sannan ki yawaita addu'a akan Allah ya bayyana mana gaskiya" na daga kaina ina goge hawayen da yake zubomun.
Ihsan bata gushe ba tana ta lallamina da rarrashi da kalamai masu taushi har na samu nutsuwa sannan kowa ya tafi gida da alkwarin zamu hadu anjima. saboda bikinta saura 4weeks ne kuma jibi zasu wuce Dubai ta karasa abubuwan da batayi ba tunda tun watanni da hudu da suka wuce suka je shopping din kayan aure har kayan sun iso komai na bukin an tanada rana kadai ake jira.
kasancewar ta ba mai yawan kawaye ba ya bani damar zama babbar aminiyarta cikin kankanin lokacin da mukayi tare daman ance sai hali yazo daidai ake abota. kusan duka halayena irin nata ne har na fita son mutane da magana wannan ya sanya yan'uwanta suke mamakin son da takemun da yawan maganata da takeyi. sai nace kawai Allah ne ya hada jininmu.
ina komawa gida nayi wa Imam text cewa bazan iya zuwa gidansu ba ya baiwa kannen shi hakuri don bani da lafiya! ina turawa na kashe wayar na jefar da ita kaina na wani irin sarawa.
dakyar bacci ya daukeni. cikin baccin na dinga jin dariya ina bude idona na ga Ihsan da Baba Rabi a kaina nayi saurin tashi zaune ina murtsika ido."ihsan yaushe kika zo?" murmushi tayi tace "yanzun nan kina ta bacci" agogo na duba ga mamakina har karfe shida da rabi da azama na mike na shiga toilet na dauro alwala nazo nayi sallar la'asar. ina cikin sallah Aisha ta iso. a dan rude take tambayar Ihsan meya sameni?"ihsan tace kamar ya fa?" zama tayi a bakin gado tace "Imam ne ya kirani yace ta mishi text ba zata iya zuwa dinner din ba bata da lafiya kuma ya kira wayarta a kashe. ya nemi Ya Sadik yace baya gida. lokacin na kammala addu'a ta na shafa na mike ina cewa "zazzabine ya rufeni ina dawowa ga ciwon kai don haka na yanke kawai bazanje ba" Ihsan dai ta gano kan zancen don haka batai magana ba.
tare muka zauna muna hira Imam wayar Aisha ya kira ta hadamu mukai magana. ana magrib sai gashi da kannensa guda biyu sunzo dubani da uban birthday gifts dinsu kamar hauka.
ban samu kaina ba sai karfe goma da rabi sannan nayi wanka nayi  shaf'i da wutri na kwanta. a maimakon bacci sai tunani yabi ya maye gurbinshi na rasa me yake mun dadi. ganin baccin ba zai zo ba na tashi na dauro alwala na soma nafilfilu ina kai kukana wajen Ubangiji. bani na kwanta ba sai da akai sallar  asuba.
aikuwa ban iya tashi ba sai azahar.
wanka na soma yi na shirya cikin wata doguwar rigar plane voil pitch. na yane kafadata da bakin gyale na futo.
sai da nayi sallama da Dada sannan na shiga kitchen na dan tsakuri abinci don gabadaya raina da zuciyata a cushe suke. na dade a zaune a motata ina tunani shin wanne mataki zan dauka? ta wacce hanyar zan bullowa wadannan bayin Allah? meya dace nayi? sanin bani da amsoshin tambayoyina ya sanya na saka Cdn Maher Zaina cikin wakar "salam alaika" na kunna motar na soma tuki cikin sanyi a hankali wakar ke saukar mun da nutsuwa har na isa gidansu Ihsan.
yau muke meeting gabadaya kawayenta mu goma akan shirin bukin. order da mukayi na ashobin bukin daga Lagos duka sunzo. ganin su ya sanya na daure na saki raina mukayi abinda ya kawo mu cikin walwala da nishadi. cikin dabara ta janyo ni muka shiga dakin mummynsu muka zauna a bakin gado! a hankali ta soma magana tana gayamun tunanin da tayi da mataki na farko da ya kamata mu dauka.
bansan lokacin da na saki murmushi ba lokacin da ta kammala mun bayanin na rugumeta nayi mata godiya. sai shida na baro gidansu ihsan da niki nikin kayana na buki.
direct gidan Mamina na wuce. a kitchen na sameta bansan lokacin da na wullar da kayan ba na rungumeta ina ajiyar zuciya.
"toh ya isa dagani abinda nasa a oven ya soma kauri tunda ke ba zakiyi hankali ba har yanzu" dagowa nayi na turo baki nace "Haba Mami yaushe rabon da na ganki ina ta doki zanzo wajenki kuma zakimun haka? dariya tayi tana girgiza kai ta dauki gloves din tana sakawa tace "toh bari na kammala abinda nakeyi sai tasa ni a gaba kiyi ta kallo" nayi dariya kawai ina kallon abinda takeyi.
cikin ihu nace "wow!! beautiful" lokacin  da take futo da take futo da katon cake din mai shape din heart! juyowa tayi ta kalleni cikin mamaki "Zarah kina tunanin shekarunki nawa kuwa? meyasa kike abu kamar na yayan goye?" sulalewa kawai nayi na bar mata kitchen din na debi kayana na kai bedroom dinta domin na taho da su ne ta bayar a dinkamun. nikuma nabi lafiyar comfy bed din mami na kwanta. ban taba jin gado me dadin shi ba a duniya don haka ina kwanciyar bacci yayi gaba dani.
farkawa nayi Mami tana jijjigani anyi sallah. na sauko daga gadon na shiga toilet nayo alwala nayi sallar magrib.
ni kadai naci gaba da dube duben a dakin har yanzu Mami tana kitchen abinda yasa raina ya dan fara baci babu tantama cake din dana gani maigidanta take yiwa har ma da girkin gabadaya watakila ma bataso zuwana ba shiyasa take ta mun fada. sai naji zuciyata tayi babu dadi. mikewa nayi na gabatar da sallar isha'i na yafa gyalena na rataya jakata na futo. a corridor muka hadu da ita zata shigo cikin mamaki tace "ina zuwa kuma?" raina a hade nace "Mami dare yayi zan tafi gida" cewa tayi "toh meye amfanin zuwan ko gaisawa bamu yi ba sannan nasha gaya miki banason tukin dare ko? na riga na bugawa Dada in Sadik yana nan yazo ya dauke ki tace ki zauna kawai gobe kya taho" tabe baki nayi nace "toh Mami ba aiki kike tayi ba tunda nazo fa baki kula ni ba" dariya tayi tace "Aww abinda ya saki fushi kenan toh Allah baki hakuri na gama aikin muje ciki" juyawa nayi tabi bayana.
sai da tayi sallah muka gaisa sannan na janyo ledojin kayan ashobin na gaya mata dinkunan da za'ai mun.
kallona take baki sake "Zara nikam kaya kala nawa kika dinka tsakanin bukin su Sadik da na Ihsan ne? kinsan kuwa barnar kudinki ya fara yawa?" cewa nayi "Mami nasani wallahi amma kinga duka bukin nice akan gaba dole nayi kwalliyar da tafi ta kowa ko don ma kowa yasan Mamana fashion designer ce" na kare maganar ina dariya. girgiza kai kawai tayi. zatai magana wayarya ta shiga ruri.
ni na tashi naje na dauko mata ita daga kan drower. "HAUSA ARAB" nagani da manyan bakake a kan screen din. a raina nace wacece kuma Hausa Arab ana zaune kalau.? ni dai na mika mata waya na soma hada kan kayan ina maidawa. ji nayi tana cewa "anya kuwa hakan da kayi kana ganin ka kyauta sosai ka bar bukin shakikanka kazo na aboki?" shiru tayi sannan ta sake cewa "na fahimta amma duk da haka ka sake nazari in kuma ba haka ba duka ka hakura don Allah ka dinga ragewa kanka damuwa  " ta sake yin shiru sannan tace "toh insha Allahu ka kula da kanka" daga nan sukai sallama! cikin nutsuwa na dube ta nace "Mami wanene?" kallona tayi domin bata taba yin waya a gabana ta gama na tambayeta da wanda take wayar ba. yau dinma kawai ji nayi na tsinci kaina da sanin wanene din! a hankali tace "Mahmud" cikin yamutsa fuska nace "waye kuma Mahmud?" harara ta sakar mun tana cewa "Mahmud dinne baki sani ba? Mahmud din Daddyn?" wow! sai yau na tuna da wannan halittar tun dawowarmu daga saudi. "Mami ya ake kuke waya dashi bayan ance ya daina kula kowa?" ajiyar zuciya ta saki sannan tace "ke! kin taba ganin inda da ya daina kula uwarsa? ke zaki iya daina kulani?" cikin mamaki nace "Mami har matsayinshi ya kai nawa a wajenki?" daure fuska tayi tamau tace "shi na fara samu ma kafin nasan zan sameki" sosai naji haushin abinda Mami tace har na soma dana sanin zuwa gidan. "gaskiya Mami yau dai i am not welcome a gidannan" banza tayi dani ta mike ta futa.
ina nan a zaune ta saka Hajjo mai aikinta ta kirani na same ta a dinning room!.
tura kofar da zanyi na tsaya galala ina kallon ikon Allah. katon table din aka cika da snacks da lemuka da kuma zungureren cake mai shape din heart a tsakiya an rubuta "My baby is 22" Allah sarki Mami. ashe duka aikin da nake jin haushin ta akansa ni takewa. a sanyaye na rugumeta ina hawayen murna! buga baya na take tana cewa "Happy birthday Zara Allah ya karo shekaru masu albarka ya raya munke cikin aminci da albarkarsa" a hankali na dago fuskata shabe shabe da hawaye nace "thank you soo much Mami i love you" daga ni sai ita muka yanka cake dinmu muka ciyar da juna.
but i can say it is my favourite birthday wallah! bayan mun kammala cin abubuwan da tayi mana ta kuma dauko wani madaidaicin box ta bani. cikin doki na bude! duka idanuna na zaro a sakamakon ganin wata azababbiyar sarka da yarinta na gold masu nauyi. duk yanda naso na nuna mata farincikina kasawa nayi. har tausayi take bani domin bata da wani buri irin ta faranta mun.
har kafe biyun dare muna kwance akan daddadan gadonta muna hira ni dai bansan lokacin da nayi bacci ba.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now