HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE FIFTY-ONE

668 59 10
                                    

Yooooo! It's my birthday🎈🎈
Here is an update❤




Halin da su Mami suka samu Mahmud a ciki ya daga hankalin su matuka. Domin idan ka ganshi ba zaka taba tunanin zaka futa ka dawo yana numfashi ba. Su kansu likitocin sai da suka tambayi wani irin mummunan labari aka sanar masa? Wanne irin bacin rai ya shiga Wanda ya girgiza shi haka? Rashin sanin amsar ya sake firgita su Daddy musamman idan suka tuna mummunan labarin da yake jiran sa idan ya farfado wanda babu tantama zai iya kashe shi ko ya mayar da shi irin halin da yake ciki a yanzu.
Har wannan lokacin Dada bata daukar wayar Daddy don haka komai ya sake jagule masa. Komai nashi ya tsaya cak! Don a yanzu duka farin cikinsa da walwalarsa da nutsuwarsa sun ta'allaka ne ga samun lafiyar Mahmud da warware matsalar da suke ciki. Bai ki ya rasa duk abinda ya mallaka akan samun lafiyar Mahmud ba. Wani irin so yake wa Mahmud irin wanda baya yiwa Sadik da Omar, wani irin so me tsanani da karfin da ba zai iya kwatantuwa ba. A tsakiyar ransa duk abinda ya shafi Mahmud yake,duk motsin sa yana nan cikin ransa kamar Wanda aka dasa don haka shi bai ga wani abu a duniya da zai raba shi da Mahmud ba komai girmansa. Bai ga mahalukin da zai iya shiga tsakaninsu ba don haka ne ya daura damarar fuskantar kowanne irin kalubale daga Dada da ma duk wanda zai shigo cikin wannan magana a shirye yake da shi.

Ta bangaren Mami babu abinda take yi sai addu'a da karatun al'kurani tun zuwansu. Tayi saranda ta tattara duka lamuranta ta mikawa ubangijin sammai da kassai! Kuma tayi imani da cewa Yana sane da su da halin da suke ciki sannan ta shirya karbar kowacce irin kaddara ce zata sake kutsowa cikin rayuwarta. Domin ita kam ta sare da yanayin da Mahmud yake ciki, tasan wani mawuyacin abu ne ya tashi domin tunda ciwon ya kama shi bai taba tsamari irin haka ba. Idan kuma wata zuciyar tace mata zaiji sauki hankalinta ya dan kwanta sai ta tuna bakin labarin da yake jiransa wanda ta tabbatar ba jinsa zai sake hargitsa lissafin zuciyarsa koma ya tashe ta daga aiki gabadaya. Wannan tunani ba karamun raunana ranta yake yi ba, tayi ta zubar da hawaye cikin sujjada tana neman alfarma wajen Allah tare da tawassali da Annabin sa akan ya bar mata Mahmud kada ya dau ransa a wannnan halin da rayuwarsa tafi komai muhimmanci a gare su.

Kwanaki uku muka dauka cikin wani irin hali na tashin hankali da fargaba. Tun su Mami na daukar waya ta har suka gaji suka daina saboda basu da abin cewa. Babu wani cigaba a jikin Ya Mahmud, likitocin sun tabbatar musu da cewa zuciyarsa tayi matukar weak. Matsalar da yake fuskanta a yanzu itace cardiogenic pulmonary edema, wanda matsalar ciwon zuciya ta haifar masa. Dalilin da ya sanya shi tari mai tsanani da jini kenan da kuma saurin daukewar numfashi. Gazawar jijiyoyin da suke kai jini zuwa zuciya yake sanyawa jinin ya dinga komawa cikin hunhun Dan Adam.
A yanzu dai abubuwan da ake so su kammala sune blood tests, echocadiogram, electrocardiogram da cardiac catheterization. Idan duk wadannan sun kammala ne za'a Dora shi kan cikakken medication din da yake bukata.

Prognosis din lalurar da take damun Mahmud ba mai dadi bane, domin cuta ce da take mugun kisa, duk da tsamarin ta bai kai yanda za'a futar da rai da samunsa ba amma likitan Mahmud ya yi wa Daddy cikakken bayani akan cutar da abinda yake haifar da ita, da kuma hanyar da za'abi a kubuta. Ya kuma yi masa alkawarin sai yanda karfin sa ya kare akan Mahmud. Gudunmawa daya suke bukata daga Daddy shine, su nisantar da zuciyar Mahmud daga damuwa da bacin rai, su hana shi lokacin tunani da lissafi mai yawa sannan a inganta abincin cinsa zuwa wanda lalurar sa take bukata. Ya rage stress din da yake dorawa kansa. Da wannan Insha Allahu za'a samu gagarumar nasarar cin galaba akan ciwon sa.

Daddy ji yake bai ki ya dau Mahmud su koma wata nahiyar daban suyi zamansu su biyu cikin kwanciyar hankali da farin ciki ba.
Duk wani babban Shehin malami da waliyyi da ya sani ya buga waya ya nemi alfarmar addu'a a wajen sa. Sannan a kwanaki ukun nan mutum Goma sha biyu mabukatan zuwa kasa mai tsarki wanda basu da halin zuwa ya diba ya biyawa Umra musamman suyi wa Mahmud addu'a. Addu'a daya ya gaza samu daga bakin da yafi kowanne tasiri a rayuwar shi wato bakin Dada. Hakan yake sanyaya jikinsa yake ganin kamar ba za'ai nasara ba domin shi bai ga wani abu a rayuwa wanda ya taba fuskanta bai same shi ta hanyar sa albarka da addu'ar Dada ba komai girmansa. Duk abinda ya zama a rayuwa albarka da jumurin addu'o'inta ne sanadi. Bai taba tunanin akwai wata rana da zata zo wadda zai bata ranta har ta daina magana da shi ba. Duka yan'uwan sa guda biyun Sulaiman da Badi'a zazzafan kishinsa ne a zukatan su da wata tsangwama ta babu gaira babu dalili, mahaifin Zara ne kadai babban amininsa kuma masoyinsa na haika balle yace zai kama kafa dasu a wajen Dada ta sakko daga fushinta.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now