HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE TWENTY

850 62 4
                                    

Cikin sauri nake tafiya har na isa parking space na shiga mota na zauna! numfashi nake futarwa mai nauyi kamar wanda nayi gudun shekara! kaina ya soma sarawa! aure? no! in this situation? bazaiyu ba! banajin zan iya auren Imamu yanzu gaskiya duk da ina bala'in sonshi! dawa zanyi magana? wa zan nemi shawararshi? God!! Aisha ce kadai zata saurareni ta fuskanceni ta gane me nake nufi! i have no option than to go and meet her! cdn motar na kunna na saka karatun al'qurani daga bakin Sheikh Abdurrahman Sudais cikin Suratul Ma'idah! a hankali nutsuwa ta dinga saukarmun har na samu sukunin tada motar na hau kan titi a hankali na dau hanyar gidansu Aisha!
Maigadi ya wangale mun gate na shiga ba tare da na sauke gilashin motar ba don banason ya cikani da unending surutunsa! bayan nayi parking na futa daga motar na shiga cikin gida! a parlour na samu Ikhram tana sakawa Abid junior brother dinsu kaya! cikin far'a ta soma gayar dani! "Iky ya Kano?yaushe kika dawo daga gidan Maman?(Aunty dinsu ta kano)" cewa tayi "Jiya Daddy yaje muka taho tare!" nace "hutu ya kusa karewa dai" ta sake murmushi sannan tace "saura 10days na koma Ya Zahra" nace "Allah ya taimaka ina Umma? ina Aisha? gidan shiru haka" cewa tayi "Aw ai Ya Aishan suna asibiti da Umma bata da lafiya" na zaro idanu cikin damuwa "meya sameta? yaushe suka tafi?" ta amsa da cewa "basu dade ba! kanta ne yake ciwo da jiri kuma in ta tashi kamar zata fadi" na girgiza kai cikin damuwa nace "Allah ya bata lafiya wanne asibiti suka tafi?" tace "Nisa ne amma na kira Umma tace yanzu zasu shiga ganin Doctor ba lallai admitting dinta zasuyi ba" na girgiza kai cikin gamsuwa! ina zaune muna dan hira akai sallar la'asar na mike na shiga dakin Aisha don yin alwala! direct toilet na fada nayo alwala na futo nazo na tada sallah! bayan na idar na mike zuwa gaban vanity table na tsaya! lotion na dauka na shafa na gyara fuskata sannan na dawo gaban gado na zauna! na kai hannu na janyo drower sama ta jikin gado! albums dinmu ne na grad! nan na shiga dubawa ina murmushi tare da kewar makaranta da kawayenmu! drower ta kasa na sake janyowa! babu komai sai katon diary da macbook dinta samanshi! mamaki nayi domin ai mun dade da daina wannan shirmen na aje diary da rubuce rubuce a cikinsa! well bari mugani! na fada a raina! ciro shi nayi na zauna a kasa na bude page din farko! da manyan baki aka rubuta "This is my personal diary! do not open my diary without my consent!!" nayi murmushi ina cewa 'i am exempted' abubuwane game da ita da wadanda suka faru tayi farinciki mostly an dade sosai har zan rufe na aje sai na bude wani shafi da ya tafi da hankalina! "how he changed my life" rubutun shekaru uku da suka wuce akayi shi cikin harshen bature!

"ban taba tunanin haka so yake ba! ashe lokaci daya yake shiga jikin mutum ya fada zuciya? ashe dagaske akwai love at first sight? ban taba gasgata wannan hashashe ba sai da yau ya faru a kaina! mujallar Ovation ba wadda zan manta nan kurkusa bace domin ita tazo mun da hoton matashin da tunaninsa ya zamo mahadin rayuwata! hakan ya faru ne lokacin da na shiga motar Baba naga mujallar na dauka ina kallo! ciki harda bukin yayan shahararren dan kasuwan nan Yusif Kashim kyaree na Maidiguri! bayan hotunan ango da amarya na idanuna suka dallaromun hoton wani dogon farin gaye mai kama da balarabe wajen kyau da haskenfata! sanye cikin bakin kaya yana murmushi!! tundaga lokacin zuciyata bata daina bugawa tana amo da hoton shi akanta ba! tunanina ya tsaya cak har muka isa da Baba gidan abokinshi bansan inda hankalina yake ba! bayan mun dawo ban iya aje masa mujallar ba na taho da ita cikin gida! tun daga ranar rayuwata ta chanja ya kasance bani da abun yi illa na kurawa hoton wannan bawan Allah ido nayi ta kalla ina hawaye don azabar da nakeji akan soyayyarshi ba yar kadan bace! abun ya soma shallake hankali har Umma ta fara ganewa a karshe da ta rutsani ina kuka nace mata gabana ke yawan faduwa! umma ta bani addu'o'i wanda da taimakonsu na samu relief din damuwa! daga ranar ban sake kwanciya bacci ba tare da na kalli wannan hoto ba! ban sake daga ido na kalli wani bayan shi ba!"

Murmushi nake ina karkada kai! lallai ma Aisha ashe ta taba fadawa tarkon so amma duk surutunta bata sanar dani komai ba! kodayake an jima kila duk shirmen kuruciya ke dawainiya da ita lokacin! bayan na wuce wasu shafukan da duk yawanci rubutun aka irin son da take mishi ne da wasu abubuwan da suka shafi rayuwarta! banyi nisa ba na sake tsintar abinda ya kadamun yan hanji har na runtse ido na bude don ganin shin gizo idona yakemun ko gasjiya ne?"

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now