HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE TWENTY-EIGHT

859 54 10
                                    

Shiru nayi kirjina yana bugawa gabadaya zuciyata ta kasa baiwa bakina kwarin guiwar da zai bude ya tambayi Aisha abinda ya faru! sai da taji babu alamun zan tambayetan sannan tayi dariya tace "ohh! Bestie! are u scared? shiyasa ban kira na gaya miki abinda yake faruwa ba wallahi nasan zaki fini shiga wani hali! amma daga hannu ki godewa Allah bestynki ta tsallake rijiya da baya" cikin shock na lashe busassun lebbana nace "Aisha don Allah jinina zai daskare kiyimun bayani ki daina dagamun hankali" dariya tayi sannan tace "kinsan na gaya miki tun ranar da results din asibiti suka futo naga hankalin Daddy a tashe ko? sannan shine dalilin da aka soke tafiyata school?" a kagauce na amsa "eh nasani" taci gaba "Zara ashe wai wani abu suka gani a jinina basu gane ko menene ba! kuma abun ya basu tsoro sosai! shine Daddy yace mutafi America kawai ba tare da ya bari nasan komai akai ba!" sai da mukazo naga an kawo ni asibiti! Zara kullum akwai abubuwan da za'ai mun! tun ina tambaya suna kwantar mun da hankali har na hakura nasa ido na saduda da rayuwa! Ranar da akamun CT scan test kuwa na shiga tsananin firgita da tunani! nidai Zara bansan abinda nake ciki ba sai bayan 2wks! duka result suka futo sannan likitan yake mana bayani dalla dalla abinda suke tunani bashi bane! shi kansa yayi mamakin yanda ma kubuta daga cutar Zara kuma yayi mana murna! sai lokacin da nagane abinda ake nufi, sai lokacin na fahimci ashe a tsakanin rayuwa da mutuwa nake! Sai lokacin nagano dalilin da sanya Daddy janye tafiyar da ya dora burinsa akanta yayi asarar kudinsa! sai lokacin nagane dalilin rashin nutsuwar Umma da kodewar idanunta mafi yawan lokuta! idan na kiraki a lokacin bansan me zance miki ba tunda nima bansan exact abinda yake faruwa ba! nasan hankalinki ne zai tashi sai kawai na hakura nace kila ba zamu sake ganawa ba Zara"

Hawaye nake wani nabin wani kamar an balle famfo! this time basu jamun rai ba suka dinga tahowa daga can karkashin karyayyiyar zuciyata! Rayuwar Aisha wata aba ce mai matukar muhimmanci a tare dani! i just can't imagine wani abu ya faru da ita balle ta kai ga mutuwa! innalillahi! Allah karka nunamun wannan bala'i! gaskiyarta da tace idan ta gayamun zan fita shiga tashin hankali! Aisha a rayuwata kamar jinin da ke makale jikin hanta ne! wata irin soyayya da shakuwa ce a tsakaninmu irin wadda ba zata fassaru ba! bansan cikinmu wanda yafi san dan'uwanshi ba, abinda nasani kawai anan duniya banga abinda bazan iya yiwa Aisha ba komai wahalarsa matukar bai sabawa shari'ah ba! Halin da na shiga bayan tayimun wannan bayanin ba karamar dimuwa da bugun zuciya bane! kawai hasashe nayi abun ya tabbata! sai naji zuciyata ta karye!

shirun da taji yayi yawa ne ya sanya ta busa wayar tana cewa "hello are you there? Zara kina jina?" kuka ne yaci karfina na aje wayar! na mayar da kaina kan pillow nayi kukan da ya isheni na kara harda na farincikin kubutar yar'uwata sanann na mike nayi nafila na godewa Allah tare da neman tsari da kariya akan duk wani ciwo da zai daga mana hankali!
Yayinda Aisha bata gaji da kiran wayata ba, tana katsewa zata sake bugowa! har na shafa addu'ar na mike naje na dauka!
"ohhh bestie kuka? ina dauriyanki da karfin zuciyarki?tun ma ban mutun ba? idan wataran na mutu ya zakiyi?" cikin bacin rai nace "Aisha this is not a joking matter! don Allah mu bar maganar nan! nayi sallah nagodewa Allah! kuma Shi zai ci gaba da tsaremu daga dukkan sharri da bala'i! chapter closed! "
Dariya ta saka mai sauti wadda take bayyanar da zallar farin ciki da nishadi! rabonda naji irin wannan dariyar ta Aisha tun kafin Imamu ya shigo rayuwarmu! sai naji wani sanyi da salama! hira mai dadi mukayi tare da tambayar lokacin da kowanne zai koma gida! suma daga America Saudi zasu taho amma lokacin mun tafi gida! don haka ba zamu hadu ba sai bayan 3wks idan sun dawo Abuja! da haka mukai sallama!

HOME SWEET HOME

satinmu daya a Makkah muka juyo Jiddah! su Ihsan sun rigamu tafiya gida da kwanaki uku sannan muka biyo su daga baya! Bamu koma makaranta ba don ana cikin hutun sabuwar shekara! a lokacin ne kuma su Daddy suka sake tambayar Ya Mahmud idan lallai dagaske yake akan maganar Safna domin asan abinda za'ayi! ko da wasa banyi tunanin Ya Mahmud da gaske zai iya auren Safna ba! nafi aje hankalina akan kawai tayata shirmenta yake yi akanshi! Ga mamakin kowa kuwa sai gashi ya amsa ya kuma tabbatar da yana sonta kuma zai aure ta! ban masa sha'awar mace irinta ba, bama ni kadai ba kowa ma, saidai matsuwar da akayi yayi auren ya sanya aka sa kafa aka take duk wani aibu na Safna aka je aka tambayo masa aurenta! Su Kawu Sulaiman basu bar gidan kakannin Safna da ke unguwar Lamido cresent a garin Kano ba sai da akace an basu!(toh who will say no to a man like Ya Mahmud?) take aka aje musu makuden kudade a matsayin kudin zance da na gaisuwar Iyaye!
sai da yaga komai ya kammala sannan ya soma haramar tafiyar domin hutunsa ya kusa karewa!
Asabar din da ta biyo baya karfe tara alarm ya tasheni domin zamuje da Mami Kano don ta kagu ta gana da sirikanta! ta gansu su ganta!(Yan' uwan Safna da Aunties dinta)
a gurguje nayi breakfast nayi wanka nayi nafilfilu na sannan na shirya cikin skirt and peplum blouse din super fara sol mai adon ganyayyaki purple! da pattern din atamfar aka kawata dinkin! na yane kafadata da karamin gyale fari! sannan na feshe kwalliyar da turaren Rasasi mai suna "while in love forever" cikin purple din katuwar jakar michel kors na hada duka tarkacena da wayoyina sannan na janyo karamar troleyn da na hada jiya ta kayana na futo!
Wajen Dada na shiga mukai sallama sannan na futa gate na shiga motata!

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now