HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE TWENTY-FOUR

814 63 0
                                    

A nutse ya soma magana! "Zara meye gaskiyar abinda yake zuciyar ki game da Imam?"
a sukwane na dago na kalleshi! domin tambayar ta mamayeni ban kawo wani abu mai alaka da Imamu zai tambayeni akai ba! ganin halin da na shiga yace "look! relax! muci abincin tukunna sai muyi maganar! girgiza kaina nayi na fara tura abincin da gabadaya sha'awarsa ta dauke a raina! tunanin me zan gaya wa Ya Mahmud nakeyi! abinda yake tsakanina da Aisha wani babban sirri ne da duk duniya babu wanda zan iya gayawa! plan din da nake shiryawa kuma tsakanina ne da Rabbul izzati don ko ita Aishar ba zan bari ta san komai ba! toh ta wacce hanya zan bullo? dakyar na dan tsakuri kadan acikin abincin na cire hannuna nasha ruwa! Shima aje spoon din hannunshi yayi ya dubeni "Ina sauraronki! kinyi alkawari tun da farko zaki gayamun gaskiya!"
Jikina ne sanyi harshena yayi nauyi sosai sannan kirjina ya soma bugawa!
sai da ya sake maimaita tambayarshi sannan na soma magana cikin tsananin sanyin jiki!
"babu komai Ya Mahmud kawai dai ina jin banason auren ne kwata kwata!bama da shi ba da kowaye! i'm not ready! i dont want to get married anytime soon"
murmushi yayi yana girgiza kai sannan yace "akwai alamomin tambaya akanki Zara! dole akwai abinda yake faruwa! ko dai kin daina son shi ne ko kuma yayi miki wani abun wanda kike ganin kamar ba zaki iya auren shi saboda abinda yayi mikin ba, ko kuma kin gano wani abu game dashi da bakya fata ga mijin da kike son aura, ta iya yiwuwa kuma shaidanu ke son miki wasa da hankali!! wannan sai nace ki dage da addu'a domin hakan matsala ce mai girma! idan duka babu daya acikin dalilan da na lissafa miki toh lallai ya kamata ki nutsu ki shiga hankalinki domin aure ba maganar wasa bane! abu ne wanda mutum yake tsayawa ya duba wanda ya dace da shi, wanda yake ganin zai dace da rayuwar shi, wanda zai iya rayuwa da shi ta har abada! tun farko kiyi nazari akan wanda kike so, mutumin kirki ne? kinason shi saboda Allah? zaki iya zama da shi a kowanne yanayi? yana da qualities din da ake bukata akan namiji a addinance ba son rai ba? sai kin gama duka wadannan tunanin sannan zaki zo kiyi addu'ar istihara akan Zabin da kikai wa kanki! idan alkhairi ne zakiji hankalinki ya kwanta da shi idan kuma ba alkhairi bane zakiji zuciyarki na miki wasi wasi!
duk wadannan matakan ana binsu ne kafin ace ankai ga kawo kudin aure Zara, ba irin wannan lokacin da ake shirin biki ba! ki nutsu kisan abinda kikeyi babu wanda zai zauna miki dashi ke kadai za'a kai don haka kada ki zabi abinda zaki dawo kina dana sani! zancen baki shirya ba bai taso ba domin duk wani abu a rayuwa ba shirya masa ake ba! idan yazo kawai karbarsa ake domin ta iya yiwuwa lokacin da ka shiryawa abun shikuma  ya dade da yi maka nisa! kin kammala secondary school kin shiga jami'a kuma kina da damar cigaba a gidanshi toh meye matsalarki? fadamun?!! meye exactly damuwarki?
Shiru nayi idona akan plate din abincina ina nazarin maganganunshi! kwarai duk abinda ya fada gaskiya ne toh sai dai abinda bai sani ba ni tawa matsalar tasha bambam da wadda aka saba gani! ni wasu irin kullallun matsaloline masu tada hankali da jefa kwakwalwa cikin rudani da tunani suke fuskantoni! bansan ta ina zan fara ba balle na gane ta inda zan kare wannan curarren al'amari mara kan gado! abinda nasani kawai guda daya ne!shine "BAZAN IYA AUREN IMAMU BA!" ko da kuwa shine autan maza! bazan iya auren mutumin da Aisha take masifar so ba! bazan auri mutumin da ban yarda dashi ba! bansan ta inda zan warware komai ba amma komai zai faru kowanne irin tashin hankaline zai bullo ba zan sauya ra'ayina ba! hajjoji kadan nakeson samowa na hada da wandanda nake dasu a hannuna na yaki auren da ake shirin yimun da Imamu to kowanne hali!
buga teburin gabana Ya Mahmud yayi kafin na dawo daga duniyar tunanina! cikin sanyi yace
"Na lura akwai abubuwa dayawa da ke cikin zuciyarki! ba lallai sai kin gayamun yanzu ba! amma ko yaushe kika shirya tattauna matsalarki dani toh kofa a bude take! ki nemeni a ko'ina nake zan zo na saurareki na kuma taimaka miki da karfina da shawarata da duk abinda zanyi amfani dashi wajen nemo miki yancinki! abinda kawai nakeso dake shine ki daina wannan damuwar da tunani domin kina tayarwa da Mami hankali! ba lallai ta futo ta bayyana miki ba amma zatafi kowa shiga wani hali idan ta gane bakyason auren nan ba tare da wani kwakwkwaran dalili ba! Dada kam kinfi ni sanin halinta  karki sake wannan maganar tayi zurfin da zata hadaku fada! domin abun bazai miki kyau ba ko kadan! idan har kina da matsala Zara ki gayamun tun yanzu ba sai lokaci ya kure ba! na miki alkawari zan tsaya naga cewa kin samu duk abinda kikeso indai ba son zuciya bane! karki sake Zara ki bar wani abu a ranki da niyyar zaki iya warwarewa ke kadai, saboda ke yarinya ce! bakisan rayuwa ba bakisan rikicin da ke cikinta ba don haka na dauko ki nan naji damuwarki saboda aure ba abun wasa bane!
Ajiyar zuciya nayi! sannan na dube shi nace "Nagode da kulawarka Ya Mahmud kuma insha Allah zanci gaba da addu'a kamar yanda kace! sannan idan akwai wata matsala zan sanar da kai da zaran hakan ya taso" murmushi yayi yace "very good!" daga nan muka bar maganar muka tashi muka futa daga gidan abincin!

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now