Ďandano daga Rai dai

554 15 15
                                    

Cikin nutsuwa ta sauka daga cikin babur ďin adaidaita sahun kanta na sarawa a hankali, ga wani zazzabi da yake nuqurqusar qasusuwanta da tsokar jikinta. cikin matukar dauriya ta biya mai babur kudinshi sannan ta isa kofar gidan, ta tura gate ďin a hankali ta shiga. Hannun dama tayi inda flat ďinta yake ta sake buďe ķofar madaidaiciyar barandar da ke gaban ginin sannan ta shiga a nutse ta buďe kofar da zata sada ta da madaidaicin falon mai ďauke set din kujeru masu saukin daraja daga fuskar falon akwai TV stand mai ďauke da karamar plasma da receiver da ýan tarkacen littattafai da films a shirye daga gefe guda.

Kallo ďaya za kaiwa wajen ka tabbatar da ingantacciyar tsaftar Wanda yake zaune a cikinsa. Babu wasu kayan kudi ko alatu amma komai ya zauna wajen da ya dace kuma an tsabtace shi.

Ýan step guda uku zaka taka daga karshen falon su sadaka da dinning area wanda bai samu tagomashin dinning table ďin ba sai lallausan dadduma da aka shimfiďa da tuntu daga kusurwoyin wajen. Daga gafen hagu Kofofi ne guda biyu, ďaya kitchen, ďayan madaidaicin bedroom. Gefen hagu kuma kofar toilet ďin baki ne. Iyakacin gidan kenan. Sai dai kasancewar ita kaďai take rayuwa a cikinsa ya sanya take zaune a yalwace babu takura babu kunci.

Akan 3seater ta zube tana maida numfashi tare da dafe kanta da yake tsananin sarawa. Ta sake nannaďewa cikin lafayan jikinta tana rawar sanyi kamar ana kaďata.

Mintina arba'in ta kwashe a haka sannan ta soma tunanin baiwa kanta taimako tunda tasan bata aje wani wanda zai leko ya duba ta balle ya taimaka mata. Da iya kacin dauriyanta ta miķe ta shiga dakin tana dafe bango ta isa first aid ďinta ta buďe ta ďauko paracetamol guda biyu ta miķa hannunta kan drawer ďin gadon ta ďauki ruwa cikin jug ďinta ta sha maganin sannan ta mirgina ta kwanta kan katifarta tana lumshe idanu.

Ta kai mintina ashirin kafin bacci mai nauyi ya ďauketa.....cikin baccin ne kuma ta ganta cikin wani irin lambu mai wadataccen itatuwa da kayan marmari iri iri. Yanayin lokacin kamar irin bayan sallar asubar nan gari ya fara haske amma rana bata futo ba.
Kallon ko'ina take da sha'awa tana murmushi, sai taji an dafa kafaďarta.
A hanzarce ta juyo, wata kyakkaywar mace ce fara sol doguwa cikin shigar lafayya lace fara sol, ba don ta cika ķuruciya da yawa ba, da sai tace Innarta ce. Ganin irin kallon ķurillar da take wa matar ya sanya ta murmushi sannan tace

"Safa! Tunanin me kike yi?"

Da mamaki take kallon matar sannan ta faďa jikinta cikin rawar jiki tana sakar kuka.

"Ammi! Ammina Kece?

Shafa bayanta ta shiga yi tana cewa

"Kici gaba da hakuri Aminatu, kici gaba da bin turbar da kike kai, kici gaba da mikawa Allah al'amuranki kada ki nema wajen kowa bayan Shi! Hakika ni na kasance mai alfahari da samun ďiya kamar ki Ameenatu! Allah yayi wa rayuwarki albarka! Ki daina yawan damuwa kinji Safa, ki saki a ranki ina tare da ke a kowanne yanayi a kowanne hali a kowanne lokaci........."

Firgigit sai ta farka daga baccin cikin wata irin zufa, alamar zazzabin ya sauka! Wasu irin siraran hawaye idanunta ke fiddawa na kewa da tunanin mahaifiyarta! Ķaunar da ke tsakaninsu is beyond explanation, don haka rabuwarsu wata irin musiba ce mai tsaurin da bata taba gani ba.

Addu'o'i ta dinga jerowa tana aika su kabarin Ammi kafin hankalinta ya kai ga agogon ďakin da ya nuna ķarfe bakwai na magriba. A sukwane ta mike zuwa toilet ďin ďakin tayo alwala tana istigfari don batayi sallar la'asar ba.

Cikin nutsuwa ta gabatar da sallolinta sannan ta ďora da nafila tayi addu'a mai tsayi a sakamakon yanda take jin ranta babu daďi a dalilin amsa tayin zama model ķarķashin HUZZARA fashion house da tayi. Bata da choice bayan wannan kuma tana fatan hakan ga zama alkhairi a rayuwarta, ubangijin sammai da ķassai ya tsare ta daga sharrin abubuwan cutarwa na fili da boye.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now