Unedited
Tsayawa yayi sororo yana kallona ina zabga kuka kamar wadda aka aikowa da sakon mutuwa. Kuka bil haqqi irin wadda yake tahowa daga karkashin zuciya, irin wanda ba'a iya tsayarwa idan ba shi ya tsaya don kansa ba.
Sai ya shiga rudani! Mikewa yayi ya shiga dakin Dada ya yambayeta abinda akai mun, nan take bashi labarin abinda ya faru dani jiya da kuma gargadin likita akan a hakura da yimun fada ko tuhuma ta akan hakan sai naji sauki.
Cikin tausayawa Mahmud yake cewa "Dada ina tsoron kada depression ya kama yarinyar nan! Akwai strange abubuwa da suke bullowa daga gare ta masu yawa, tun bayan rasuwar Aisha bata koma normal ba" A nutse Dada tace "menene kuma difireshan? Kai dadi na da kai baka iya dogon zance ba sai ka saka yaren nasara" Murmushi yayi yace "ina nufin ciwon damuwa Dada! Shikuwa idan ya kama mutum da akwai matsala, akwai bakar wahala kafin a rabu da shi! Kuma naga alamun ciwon da dama a tattare da ita.
Na farko dai abubuwan da take matukar so ta rage son su ko nace ta daina son su. Kamar kwalliya mai yawa, saka turare, son girke girke. Wadannan duk abubuwan da take so ne amma yanzu sam ba zaki ganta tana abu daya daga cikinsu ba. Na biyu son mutane da Tsokane tsonanen ta ya ragu sosai, haka kawai zaki ga tayi shiru tana tunani, wani lokacin ma tana hawaye bata sani ba, ko da yaushe tafi son kwanciya ita kadai a daki ko kuma kuka. Ta rame sosai! Duk lokacin da zaki ganta murmushin karfin hali take yi bai kai zuciyarta ba........
Haka yaci gaba da yi wa Dada bayani tana girgiza kai cikin gamsuwa domin ta tabbatar da abubuwan da yake fada da idanunta.
"Toh yanzu asibiti za'a kaita? Daman lahadi ta sama zamu tafi Jedda ganin likitan kafata inaga kawai itama idan taje ta ga likitan"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Dada zai fi kyau taga therapist! Akwai mahaifiyar abokin aikina Dr.Ahmad tshohuwar therapist ce kuma ko bayan tayi retire akan kai mata cases irin wannan har gida. Mun saba sosai kuma zan mata bayanin da zata fahimta yanda ya kamata. Bana so a soma bata pills da abubuwa a shekarunta.
Dada tace "toh ai kaine ka san komai duk yanda kaga yafi haka za'ayi! Allah ya shige mana gaba!"Bayan na gama kuka na na tashi na shiga toilet na wanke fuskata nasa kwalli domin bana son Ya Mahmud ya matsa mun akan lallai sai na gaya mishi me yake damuna. A parlour na futo na same shi yana cin abincin da na rage, zama nayi ina cewa "Ya Mahmud ragowar kake ci? Ga cooler din abincin a dinning" girgiza kai yayi yace "na kin ne ya bani sha'awa a koshe nake" nayi murmushi na zauna ina bashi labarin twins din Ya Omar, ga mamakina bai sake mun maganar kuka na dazu ba don haka na sake sosai muna hira sai da akai kiran sallar la'asar ya futa masallaci.
Tare muka tafi gidan Ya Omar ganin babies! Lokacin da ya dauko su ya rungume wasu hawaye ya dinga yi kamar zai hadiye yaran. Scene din was soo emotional! In dai ka zauna da shi zaka gane yana son yara sosai musamman babies sabbin haihuwa.
Sai da ya gama jin duminsu sannan yayi musu addu'o'i ya kwantar da su akan gadajen su. Wani makeken daki aka mayar nursery. Komai na dakin blue and white ne yayi matukar kyau. Sai sassanyan kamshin turaruka marasa karfi ke tashi da wani dumi na musamman.
Bamu baro gidan ba sai bayan magrib sannan muka tafi har Mami zuwa gidanta. Bayan na shiga ciki ne yake gaya mata yanda suka yi da Dada! Itama Mamin tayi na'am da shawararsa domin ita kanta matsalar rashin walwalata yana damunta.Kwanaki biyu bayan lokacin aka kawo kudin aurena da Mubarak! Babu Wanda na gaya wa matar shi tayi mun waya balle barazanar da ta zayyana mun har shi kansa Mubarak din! Washegari kuma aka kai na Ya Mahmud gidansu Amina akai fixing date rana daya. Wato watanni uku dai dai. A ranar Ya Mahmud ya wuce London, da dimbin tunanin yanda zai bullowa Safna da kuma yanda zai tunkari shirye shiryen auren sa.
Ranar a gidan Mami na kwana, tun jiya da Ya Mahmud yaje yi wa Dada sallama na biyo shi don na samu raka shi airport da asuba. Mami gabadaya jikinta yayi sanyi, kamar tace ya hakura da tafiyar yayi ta zama tare da ita. Da daddare ina dakin Mami ina duba kayan da nayi order ta hannun A.laila wanda suka zo da yamma. Ware na Ya Sofy nake a akwati na ihsan na barsu cikin wannan akwatin da aka kawo kayan a ciki, kowacce bayan kayan babies na saka mata turmin super guda biyu da laces guda biyu. Babyn Ihsan na hada mata da bangles masu kyau na gold guda uku. Sai da na kammala shirya komai na rufe akwatinan sannan na shiga gyaran dakin don Mami ta hargitsa shi sosai wajen nemo mun laces din da na saka wa su Ihsan a kayan su. Sai da na hada komai cikin wardrobe na gyara sannan na kula da wata drower da ke cikin wardrobe din. Kullum a kulle take amma yau ga mamakina sai ga mukullin a jiki, ta bude ta manta bata zare mukullin ba.
Zama nayi sosai na murda mukullin na janyo ta na bude. Hotuna ne da littattafai da takardu a shirye reras.
Cikin nutsuwa na soma ciro hotunan ina kallo, dadaddun hotuna ne tun Mami na yarinya na da na kuruciya da kuma na aurenta. Cikin wani envelope na ciro wasu hotunan guda shida, daya Mami ce da ABBA mahaifina kenan, ranar daurin auren su! Na dade ina kallon hoton cikin sanyin jiki da tausayi , kyakykyawan karshe ne ABBA don yafi Daddy kyau sosai! Ko kadan banyi kama da shi ba kamar yanda ban dauko Mamin ba, sai abubuwan da ba'a rasa ba wadanda dangantakar jini ke gadar da su. Kana ganin shi kaga bafulatani usul. Mami an cakare cikin wata atamfa Holland ire iren wadanda ake dawowa da yayinsu yanzu. Duk da hotunan black and white ne bai hanani ganin kyawunsu da dacewar su ba.
Hoto na gaba Mami ce zaune a bakin gado da jariri a hannunta an nade shi cikin shawl.
Daya hoton kuwa Mami ce da ABBA da Daddy da wata mata wadda babu tantama Mummy ce mahaifiyar su Ya Sadik. Sauri nayi na wuce hoton don sai da gabana ya fadi a sakamakon mugun tsoron da nake wa wannan matar muguwa!
Zan ciro wani hoton kenan wata yar envelope karama ta fado, na tsaya na aje hotunan na dauka na bude. Rubutu ne aka yi da bakin biro wanda ya soma dan cakudewa saboda ajiya. Sai wani karamun hoto na wani dan saurayin da ba zai gaza shekaru sha bakwai zuwa sha takwas ba da baby katotuwa a hannun shi wadda za ta kai kamar shekara daya. Da na duba sosai sai nagane cewa nice, sosai nice ina yarinya.
Takardar na bude na soma karantawa cikin tsoron kar Mami ta shigo ta riskeni ina mata bincike! Nasan tabbas ranta zai baci don bata so ta aje abu ka taba ba ta saka ba balle wannan wannan asirtacciyar drower da ke kullum a kulle. Haka naci gaba da karatun dakyar, Da nazo layi biyun karshen rubutun ne na zaro idanu a sukwane gabana yayi mugun faduwa yayinda wani abu ya soma yawo a jikina kamar kiyashi. "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" na ke furtawa a fili cikin tashin hankali. Babu shiri na hada komai na tarkata su na mayar cikin drower hannuna na bala'in rawa, yayinda kirjina ke bugawa a lambar karshe. Ina ji ina ma abinda na karanta shima zai koma ma'adaninsa ya bar cikin zuciyata.
Sai da na tabbatar na maida komai kamar yanda na same shi sannan na mayar da drower na kulle kamar yanda na ganta na rufe wardrobe din ina sauke nunfashi. A guje na mike na shiga toilet na sakarwa kaina shower ba tare da na cire kayan jikina ba don tsananin kaduwar da nayi da abinda na karanta wanda Mami ta rubuta da hannunta.
Na dade cikin ruwan sanyin kafin nayi wanka na dauro towel. Har na futo nayi sallah na shirya cikin kayan bacci tunani bai bar kaina ba.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
HAUSA ARAB PART 1
Genel KurguAlqalamin qaddara yana aiki akan kowa ba tare da zabin wance ko wane ba. Kowanne bawa da irin na shi salon rubutun, na wani ba irin na wani bane.