Ranar Juma'a da misalin karfe hudu da rabi na yamma Daddy ne a babban falon baki na gidanmu tare da Ambasada, da Uncle Aliyu da Uncle Rasheed suka kammala tattaunawa akan maganar aurena da Imamu da makomarsa kafin zuwan waliyyan Imamu wanda aka shirya zaman dominsu!Sai karfe biyar suka iso aka tarbesu cikin mutunci da karramawa da kuma girmamawa! a tunaninsu sabon date za'a saka na biki tunda mutuwa ta shigo ta gibta akan wannan da aka sa na farko! basu san cewa mutuwar ce ta hana a aika musu sammacin kiran kafin ranar daurin auren ba!
Bayan sun nutsu sun taba abubuwan motsa baki da aka cika gabansu da shi Daddy yayi gyaran murya ya soma koro jawabin da ya rikitar da waliyyan Imamu ya jefasu cikin tashin hankali! Wasu acikinsu sun san kadan daga cikin halinsa wasu kuwa ma babu wanda yake masa kallon idan an saka masa yatsa a baki zai ciza. Amma dukansu sun girgiza da jin cewa wai Imamu na da Yara har biyu a waje! wa'iyazubillahi! Gashi manyan kwararan hujjojin da Daddy ya basu ba wadanda za'a musa ko a karyata bane! A karshe Daddy ya bukace da suke suyi bincike da kansu su tabbatar kafin a sake sabon zama inda za'a yanke hukuncin makomar auren namu!Da wata muguwar kunya da bakin ciki da haushi sukai sallama da su Daddy suka dau hanyar gidansu Imamu wajen mahaifiyarsa don mayar da mata da yanda suka yi a gidanmu! Shi Imamu kuwa yana Paris tun ana gobe mutuwar Aisha ya tafi! a cewarsa taron bikin cikar shekarar kamfaninsu za'ayi kuma kwanaki biyu rak zaiyi ya dawo! bansan yanda akai kwanaki biyun suke kokarin juyewa sati biyu ba! wayata na dade kasheta na jefa a drower don haka bazan gane ya kira ko bai kirani ba! Mamanshi da kannenshi dak duk sunzo mana gaisuwa har sau biyu! da manyan kulolin abincinsu da katan katan din ruwa da lemo kamar za'a bude shago! su a mutuwar ma sai sunyi karya sun nuna su masu kudi ne!
Bayan Daddy ya sallami bakinsa ne suka shigo cikin gida, su Uncle Raseed cousins din Daddy sukai wa Dada sallama suka wuce masaukinsu! ya rage daga shi sai Ambasada, sannan ya yayiwa Dada bayanin yanda suka yi da waliyyan Imamu! bayan sun gama tattaunawa ya kira Ya Nuratu taje ta kirani! lokacin ina dakina akan gado na kunna laptop ina kallon graduation dinmu na makaranta nida Aisha! kwanakina biyu kenan da soma wannan kalla kallacen a system dina! bikin Ihsan ne, prom night din mu da crazy vedios din da muke da Aisha! wani lokacin kuma na shiga images dina na saka slide view na koma gefe ina kallon hotunanmu! sallah kadai ke tadani! sai idan dare yayi a bani fura ko tea da maganin bacci na kwanta! Ina tashi da safe kuwa zan dora daga inda na tsaya a daren jiya! har yanzu bazan cewa ga duniyar da nake ba, bazan ita tantance ranar da muke ciki ba, bana gane safiya yamma ko dare, komai kallonsa nake a matsayin mafarki mai munin gaske! magana kuwa tsoron yi nakeyi ba wai kasawa nayi ba, gani nake ina yin maganar komai zai zama gaske, mafarkin zai zama zahiri! nikuwa na gwammaci zama cikin wannan rayuwar har lokacin da zan farka daga wannan mafarkin mai tsananin firgici da muni da masifa da bala'i! har yau kaya daya ne a jikina ban sauya ba, idan akwai kalmar da na tsana yanzu bai wuce naji ance nayi wanka ba ko brush ko taje hardadden gashina wanda ya koma kamar na tsoohuwar mahaukaciya ba!
Ya Nuratu ta dade a kaina tana kallona kafin tace "kizo Daddy yana parlour yana kiranki." sai da na danyi jimm sannan na dau hijab din sallah ta na saka na biyo bayanta! A hankali na zauna daga can gefen su Daddy ina muzurai, duka idanunsu a kaina suna kallona cike da tausayi da bacin rai.
YOU ARE READING
HAUSA ARAB PART 1
General FictionAlqalamin qaddara yana aiki akan kowa ba tare da zabin wance ko wane ba. Kowanne bawa da irin na shi salon rubutun, na wani ba irin na wani bane.