Bayan futar Zahra Mami ta juyo da ga Mahmud! sannan tace "ya kamata ka shirya mu tafi gidan Dada kar rana tayi kaga 12 yanzu! gabadaya mood dinshi ne ya sauya annurin fuskarsa ya dauke lokaci daya! a hankali Mami ta mike ta zagayo gefen da yake ta dafashi! "haba my son! be a Man please!! bansan ka da ragwanta ba! ka daure zuciyarka ka karfafa ranka kayi shirin tunkarar koma wanne irin kalubale ne yake fuskantarka! Allah yana tare da kai and your Mami is by your side bazan taba bari naga an kware ka ba! sannan na tabbatar ma tunda kazo da maganar aure to kayi maganin fushin Dada gabadaya! trust me she will be happy with you!"
murmushi yayi har kamutunshi ya lotsa don jin dadin kalaman Mamin tashi kafin ya mike a hankali ya shige dakin da tayi masa masauki a gidan! ita kuma ta Kira masu aiki su gyara wajen ta shiga daki!
mintina talatin ta futo parlour cikin shigar super shudiya wadda ta amshi farar fatarta! hannunta jakar Gucci ce babba da kuma key din mota! waya ta ciro tana shirin kiran Mahmud ya bude kofa ya futo! shigar da yayi ta burge babar tashi domin ya futo a babban mutum sosai! itace tayiwa Faisal transfer din kudi tace ya siyawa Mahmud kaya ya kai a dinka mishi a wurin dinkinshi!
Coffee shedda yar hilton yayi amfani da ita dinkin babbar riga ya aje hular kayan kan kanannadaddiyar sumar kansa da yau bai samu sukunin bata extra care din da ya saba ba! damtsen hannunsa daure da brown din agogon Luis Vuittun na fata da rufaffen talkami mahadin agogon! duka falon ya kacame da kamshin turaren LA NUIT na LV. saidai fuskarsa babu walwala ko kadan amma hakan bai hana kyawunsa yin tasiri ba. Mami ta tsaya tana gayawa Aya tayi wa Zahra lunch ita kadai su zasu dade basu dawo ba. sannan ta fada mata me zasuyi na dinner ta amsa cikin girmamawa Mami ta wuce gaba yana biye da ita.
Ita ke driving domin shi har yau ya kasa ko taba steering din mota tsoron ma driving din yake a garin da ya koma masa kamar bako! don haka yana daga gefen Mami tana sarrafa motar cikin kwarewa yayinda zuciyar Mahmud take faman luguden bugu musamman da suka shigo Garki! ya kalli gidan cikin tunanin wasu abubuwa da suka shude shekaru goma da doriya sai yaji hawaye na son kwace masa.
-----------------------------------------------------------
Sai da na kyaleta tayi kukanta ta gaji sannan ta mike ta shiga toilet ta wanko fuskarta ta dawo ta zauna! cikin tausayawa nace "Aisha are you ready to explain things to me?" kallona tayi sannan tayi murmushi kafin ta soma magana ciki karyayyar zuciya! "Zara kafin nace komai i want to you to know that babu wani mahaluki a duniya bayan iyayena da ya kaiki muhimmanci a gareni kuma har abada bazan sauya matsayin da kike dashi cikin raina ba! but then i also want you to do me a favour, ki hakura da jin damuwata a wannan lokacin nikuma nayi miki alkawari nan gaba kadan zan warware miki komai Zara! ba don baki cancanta na gaya miki ba! sai don kawai inaso na warware miki komai cikin sauki! ina fatan zaki fahimceni ki yarda dani Zahra! trust me, i will never disappoint you!" duk da ba haka naso ba amma jawabin da tayimun ya sanyani hakuri da gamsuwa da ita sannan na yarda da ita har cikin zuciya domin yanda take magana tana kallon kwayar idona na gane duk abinda take fada daga karkashin zuciyarta yake tahowa! nasan wacece Aisha kuma na yarda da ita!
murmushi nayi nace "well, tunda haka kika ce babu komai zan jira zuwa lokacin da zaki warwaremun komai, but you have to promise me something?" tashi tayi ta koma kan drower ta zuba mun ido tana saurarena! naci gaba "promise me zaki daina damuwa da matsanancin tunani kuma zaki daina mayar dani stranger Aisha, i hate the person you are becoming i dont like how you treat me these days" hawaye suka soma saukowa daga idanuna domin kwarai abun yana damuna sosai! rungumeni tayi ta sake sakin wani kukan! daurewa nayi na tsayar da nawa hawayen na shanyesu don banason nayi kuka a gabanta na sanyaya mata guiwa nida nazo rarrasshi! tana kuka take cewa "i promise you Zahra! i promise zanci gaba da kasancewa Aishan da kika sani kuma bazan taba juya miki baya ba! komai tsanani Zahra!" murmushi nayi na dagota daga jikina ina cewa "is okay tohm! ya isa mana kukan kar ki koma raguwa mana Aisha! bansanki da saurin kuka haka ba kuma banso ki koya! kici gaba da zama mai karfin zuciya da jarumtar da kike da!" hawayenta ta shiga gogewa tana kada kai! na sake cewa "oya i want my best friend back! smile!" sai kuwa ta kyalkyale da dariya! nima na tayata kamar wasu mahaukata! nayi iyaka kokarina na jata da hira har ta soma warwarewa muna dariya!
daidai lokacin Umma ta murda kofar ta shigo! da mamaki ta kallemu tana salati! "ba dai ku Kuke wannan dariyar ba Zara? itace ta ware haka har ta samu bakin dariya? yarinyar da take shirin futa daga hayyacinta yanzun ma fa da Abba muke waya yace mu jirashi ya dawo yana meeting ne sai mu tafi asibitin" murmushi nayi nace "Umma ta samu sauki ne" itama murmushi tayi mai sauti tana girgiza kai da alama shakuwarmu ce take bata sha'awa! karasowa tayi ta kara hannunta a goshin Aisha taji temperature din jikinta tace "kan naki yayi sauki?" Aisha ta girgiza kai tana murmushi! sannan ta juya ta futa! Aisha ta dubeni tace "besty saura 5weeks fa tafiyana school kina lissafi kuwa?" bata fuska nayi nace "hey! banson wannan zancen yanzu kar mu sake wani kukan please wani lokacin zamuyi maganan! i got to leave yanzu Mami tace kar na dade kuma kinga anjima budan kan Ihsan!" a sanyaye tace "eh hakane! ki gaida Mamin kicewa Ihsan ina mata Allah sanya alkhairi! sai munzo ganin gida!" na mike ina girgiza kai! "af na manta tace mun jiya kin bar wayarki a gidansu ko?" lokaci daya ta rikice tana duru duru "wlh muna shirin tafiya dinner din nan ne na nemeta na rasa na zata ma a hanya ta fadi" nace "bata fadi a hanya ba tana wajenta zan karba sai na kawo miki" cikin sauri har tana hardewa tace "please kice ta kashemun ita kar ta kunna don Allah zan tura Malam lawwali ya karbo yanzu" murmushi nayi nace "tohm zan gaya mata" sannan mukai sallama zata rakoni nace ta barshi jikinta baiyi kwari ba. na futo nayiwa Umma sallama na taho gida!
Tunda na shigo mota tunani yake dagargazar kwakwalwata saura kadan na wuce gida! gabadaya hankalina ya tashi kuma damuwata ta ninku! bansan meyasa nakejin wani irin tsoro da fargaba ba! saidai maganar da mukai da Aisha da fahimtar juna ya sanyaya mun rai. atleast mun daina fargabar ganin junanmu!
Bansamu Mami ba nayi kiran ta wayarta bata dauka! don haka na koma daki nayi sallah sannan nayi kwanciyata ina abun da ya zamar mun jiki a wannan kwanakin wato tunani! wayar Ihsan ce ta isheni da na taho na taho dole na tashi na futa na dan tsakuri abincin da Aya tayi na dawo na sake wani wankan na shirya cikin bou bou ta leshi yellow! komai nayi keeping shi simple don nagaji da caba kwalliyar plus raina ba dadi yakemun ba! tuni nasan an fara taron don karfe biyu ne na rana! saboda haka kai tsaye na wuce international conference center inda venue din yake!
sosai event din yayi dadi kuma ya qayatar an kuma zuba kudi kamar ba'asan darajarsu ba! abokan ango kakaf na duba banga Ya Mahmud ba! nace ya akai yau baizo ba! oho masa! naci gaba da harkata! sai wajen 6 muka dawo gidansu Ihsan inda aka shiga shirin kai amarya dake Mississippi street! sai wajen karfe goma aka tafi! Amarya sai kuka dakyar aka bambareta daga jikin Mummynta scene din sooo emotional!
Daga nan aka wuce da ita wani American Villa me kayatarwa! komai na gidan me kyau ne kuma classy hakana jeren da akayi mata babu hayaniya ko kauyanci komai english ne! gargadin Mami na tuna na sulale na dauki hanyar gida ba tare da na sanarwa kowa ba don kar ace lallai sai na tsaya Angwaye sunzo! gashi Mamin nayi ta kiranta tun wayar tana ringing har ta daina daga baya a kashe ma take bayan munyi da ita zatazo kai amarya!
cikin nutsuwa nake driving har na iso gida! na dade ina danna kararrawa kafin Aya tazo ta bude! cewa nayi "Is Mami home?" tace "yes Ma. they are inside" na wuce cikin corridor din ina9 cewa "kome yasa bata neme ni ba har yanzu?" zuciyata ta amsa "tunda wannan dan London din yazo ta mayar da duk hankalinta da kulawarta kansa bata ta Zahra! in banda haka ya za'ai na kai shadaya na dare a waje Mummy bata nemeni a waya taji inda nake ba" haushi ya turnikeni naci gaba da tafiya ina kunkuni! A hankali na tura kofar falon na shiga! cak! na tsaya cikin zaro idanu! ganin abinda yake faruwa! Mami zaune kan kujera ta kifa kanta hannun kujerar tana rera kuka a hankali yayinda Ya Mahmud ke tsaye rataye da jakar laptop dinshi da akwatin Versace a jingine gefe shima idanunsa kamar an kada jini aciki! tsayawa nayi still kirjina na mugun bugawa! a slow motion na isa gaban Mami na durkusa "Mami meya faru? wanene ya mutu?" gabadaya bata ce komai ba kuma bata dena kukan ba! mikewa nayi na dubi Ya Mahmud duk da yanda mood dinshi ya tsoratar dani ban fasa mishi magana ba! "Ya Mahmud me ya faru? me ya samu Mami? waye ya mutu don Allah?" shi dinma shiru yamun wasu siraran hawaye na bin kuncinsa kamar an balle fanfo! kaina ne naji yayi mun nauyi juwa ta soma daukana! stress din da nake shiga kwanan nan yamun yawa! kaina ba zai dauka ba! kakwalwata zata fashe! bana iya kuka balle naji sanyi da rangwame sai tsabar radadin zuciya da tashin hankali! wajen Mamin na sake komawa na dago fuskarta da hannayena guda biyu "Mami kuna son zuciyata ta fashe ne? ya za'ai na ganku kuna kuka kuyi mun shiru? kuyi mun bayani don Allah Mami kirjina kar ya buga" kawai janyoni tayi jikinta ta rungume ta sake fashewa da wani kukan matsananci!
karar kofa mukaji alamar shigowar mutane! nayi sauri na dago daga jikin Mami! Ya Omar ne da Ya Sadik dukansu babu walwala! kowanne ya nemi waje ya zauna! da gudu na bar jikin Mami na koma kujerar Ya Sadik! hannunsa na rike cikin gigicewa ina cewa "Wai Ya Sadik ya kuke so nayi da rayuwata ne? Mami da Ya Mahmud suna kuka tunda na shigo gidan sunki cemun komai! kuma kun shigo da alama kukan kuka gama a waje please! tell me what's going on! please Ya Sadik!" sai lokacin na samu sa'ar da hawaye ya soma bulbulowa daga idanuna! mikewa ya Sadik yayi yaja hannuna muka futa daga falon zuwa can garden din gidan! zaunar dani yayi a kan farin lilon da ke wajen shima ya zauna a gefena! sannan ya soma mun bayani! "kinsan Zahra Yaya Mahmud shekarunsa nawa rabonsa da gida??" na girgiza kaina a sanyaye! yaci gaba "Shekarunsa goma da watanni uku cif rabonsa da gida Zahra kuma bai sake waiwayowa koda sau daya ba koda menene ya faru! saidai idan ta kure Dada taje Jeddah yayi kokari yaje Umrah su hadu! Daddy kuma da kansa yake tafiya London ya ganshi ya dawo! dukanmu idan muka matsu da son ganinsa garin da ya mayar gida muke tattaki muje! sai wannan karon! bai gayawa kowa yana shirin zuwa ba sai Mami kuma da ya tashi zuwa bai sauka ya biya ta ko'ina ba sai gidan Mami sai da ya kwana sannan ta raka shi gidan Dada yau! kinsan me Dada tace tana ganinsu? na girgiza kaina cikin kaguwa da jin karshen maganar! yaja numfashi "cewa tayi ta cire Mahmud daga cikin jikokinta tun ranar da ya cika shekara goma bai nemi gida ba! babu shi ba ita kuma tunda ta gano duk tsayin shekarun nan da yayi Mahmud na communicating da Mami tasan duk halin da yake ciki, itama Mamin ta tafi ta cireta daga lissafin jininta tunda har da ita za'aci amanarta! sannan taji labarin silar zuwan Mahmud ba don su bane bikin abokinsa yazo wannan ne abinda yafi komai bata mata rai ta yanke wannan hukuncin! kinsan halin Dada Zarah idan ta hau fushi abun baya yin kyau masu tsayawa su tunkareta daman Mami ce ko Daddy toh yau da su take fushin don naga alama shima Daddyn ransa yayi bala'in baci ko sallama baiyi ba ya tafi Riyadh! abun gabadaya baiyi dadi ba! ta tsaya ma suyi mata bayani Zahra bata basu wannan damar ba zagi da cin mutunci babu wanda batai ba a gidan nan har da tura Mami waje ta rufe kofar dakinta!Am dedicating this chapter to Hausa Arab supporter from day 1, A.Rabi'a A Ladan. I really appreciate your love and support!love u loads💘💘💘
CZYTASZ
HAUSA ARAB PART 1
General FictionAlqalamin qaddara yana aiki akan kowa ba tare da zabin wance ko wane ba. Kowanne bawa da irin na shi salon rubutun, na wani ba irin na wani bane.