HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE NINE

968 72 0
                                    

Expression din da Eng ya gani akan fuskar Mahmud shine ya sage masa guiwa ya kuma shiga tsoro da zulumi amma duk da haka bai yi shiru ba.
"Mahmud lokacin da Shukra take gaya mana bamu dauki zancen da muhimmanci ba sai da Safna tazo ta sakani a gaba tana kuka ita lallai kai kadai take so. Tun ina mata nasiha ina kwantar mata da hankali har ta kai ta kwanta bata da lafiya. Babu yanda bamuyi mu shawo kanta ba mun gaza. Kullum daga kuka sai kwanciya. Ta koma aikin nata ma ya gagara. Ban shiga tsoro da fargaba ba sai da ta fara wani irin ciwon kirji muka dauketa mukaje asibiti. Likitan ya tabbatar mana da cewa idan bata bar damuwa ba lallai ciwon zuciya na gab da kamata. Hankalina yayi bala'in tashi domin ji nake idan wani abu ya samu Safna bazan taba iya yafewa kaina ba. A karshe nayi tunanin nayi kundunbala na nemeka na gaya maka amma tsoro da shakkar yanda zaka kalli zancen yake hanani. Nayi kokarin sanar maka ya kai sau hudu amma sai na kasa. Sai wannan lokacin nayi shahada Mahmud. Amma duk da haka ba wai inaso na tilasta ma bane, kada kayi abinda zaka takura kanka Mahmud idan bata yi maka ba ka gayamun bazan damu ba. Amma atleast nasan nayi kokari akan wannan al'amari. Kada ka dauka wai don Safna ce tawa nayi son kai dayawa, kaima naji tarihinka naji komai game da rayuwarka, naji yanda ka rasa matarka da dawowarka kasarnan da kuma rufe babun soyayya da kayi a rayuwarka. Na tausaya ma matuka sai dai hakan ba zai hana na baka shawarar cewa ka daure kayi aure ba. Ba don inaso ka auri Safna na kuma ba sai ita nake nufin ka aura ba! Mahmud duk wacce kasamu ko baka sonta kamar yanda kakeson marigayiya ka daure kayi aure domin farin cikin mahaifanka. Su iyaye daraja ce da su Mahmud ba zaka tana gane muhimmancinsu ba sai lokacin da ka rasa su."
Gabadaya zufa ce take karyowa Mahmud duk sanyin da ke ratsawa. Kansa yayi wani irin nauyi gabadaya tunaninsa ya tsaya cak. Komai na duniyar ya dauke masa wani irin yanayi yake ciki wanda ba zai iya fassarawa ba a dalilin famo masa tsohon mikin da yake cikin ransa da Eng yayi. Mikin da yake tunanin ba zai goge ba har ya koma ga Ubangiji.
Cikin sanyi Eng ya dafa kafadar Mahmud yace "don't worry Mahmud, kada ka tsanantawa kanka! Take everything easy kayi tunani a hankali ka nutsu. Ko text ne ka iya yimun daga baya. Ko daya kada kayi tunanin ka bata mun ko ka munana mun don kaki karbar wannan abu Mahmud. Nima a dole nayi ma wannan maganar domin wani nauyi ne mai girma a kaina wanda nake jin dole na sauke shi. Alhamdulillah nayi iyaka kokarina akan lamarin Safna na kuma barwa Allah komai shine zai futar dani daga wannan qangin. Ka tashi ka wuce kada dare yayi ma."

NIGERIA
Karfe shida na safe na bude idanuna ba dora su kan agogon dakin. Addu'a na karanto tare da mikewa zaune raina fari sol da murna da annashuwa. Mikewa nayi na yaye labulayen dakin haske ya keto ciki yana karamun wani farin ciki. Yau babbar rana ce a wajena domin mun kammala karatun secondary lafiya yau zamuyi graduation. Wayar Aisha na soma amsawa inda tace mun tana isowa zuwa karfe bakwai sannan na futa kitchen na futo da cake dina mai hawa biyu da na bata lokaci akansa jiya na hada wheaped cream na soma decorating dinshi. Sai da naga yayimun dai dai yanda nake so sannan na mayar dashi fridge na wuce dakin Dada muka gaisa. Ita ta soma tayani murna a yau ta kuma yimun addu'o'i akan rayuwa ta gaba.
Ina cikin breakfast Aisha ta iso da katuwar troley dinta ta zauna muka karasa tare sannan muka shige dakina.
Wanka na fada don ita tayi nata tun a gida. Ina futowa naga bakuwar tawa ta iso wato "GLAMDECK" make up artist din da Imamu yace zai turo mun tayi mana kwalliya. Cikin far'a na isa gareta muka gaisa. Sai tace bari ta soma da Aisha kafin na shirya.
Karfe tara aka kammala mun tawa kwalliyar wadda za'a kira da "simple glam" ko "nude look" babu abinda zaifi daukar hankalinka irin kalar fatata wadda ta na dinga baiwa extra care ta hanyar amfani da face mask mud mask da kalolin toners masu inganci don wannan rana. Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu na futo fiye da tunanina. Sanye nake cikin gown wadda ta tsaya iya kwaurina mai dige digen black and white samfurin "Dior" sai na dora bakar graduation gown din kai. Gabadaya yala yalan gashina a gadon bayana na zubo dashi yana sheki. Na dora hular akaina ta zauna cif. Siririn yarin kunne na ainihin diamond sai kyalli yakeyi yana haska fuskata. Irin sarkar ce sak a damtsen hannuna da idon sawuna na kafar dama. Hannuna na hagu kuma agogo ne silver na "Kalvein Klein" sai kwalliyar tawa ta zama very classy. Ita kanta mai kwalliyar sai da ta tace "tabarakallah"
Lokacin da na tsaya a gabanta ina murmushi. Tayi mun pics masu kyau sannan ta tafi. Ya Sadik ya daukemu zuwa wajen taron da alkawarin anjima zasu taho gabadaya.
Karfe shadaya na safe tuni hall din ya cika taf da baki daga kowanne fanni. A lokacin ne kuma aka soma raba kyaututtuka ga dalibai a ranar ne amintar mu ni da Aisha ta tabbata domin idan aka kira best in science subject naje na karba toh ana zagayowa Art subjects ita zata mike. Ihu, tafi, mun sha su a wannan rana. Daga bisani head girl tazo tayi speech dinta aka ci gaba da gabatar da taro cikin tsari.
Bayan mun futo ne muka soma daukar hotuna da su Mami da Umman su Aisha da su Ya Sadik dukanmu cikin tsananin farin ciki. Saidai lokacin da muka tabbatar yaune final mun gama da zaman tare a makaranta sai muka barke da kuka. Tun ana mana dariya har muka basu tausayi suka shiga rarrashinmu. Dakyar babansu Aisha ya sata a mota suka tafi nikuma muka tafi da Mami gidanta. Sai bayan na dauko wayata ne naga tarin messages din Imamu na fatan alkhairi da tayani murna. Yaci burin halartar wannan rana amma tafiya ta taso mishi zuwa Paris dole ya tafi.
TWO MONTHTS LEAP
Zuwa yanzu alakar mu tayi matukar karfi da Imam babu wanda bai san tsakanina da shi ba da kuma irin son da nake masa duk kuwa da yanda nake kokarim boye hakan a fili. Yanayin aikinshi bai bari mu kasance koda yaushe sai dai kullum cikin kirana a waya yake da turo sakonni na so da kauna da sanyaya zuciya. Ba shakka Imam is a heaven sent. Domin duk wani buri da nake da shi akan mijin aure ya hada su. Matsaloli na da Imam guda biyu ne. Na farko matarshi da nake burin nasan wani abu a kanta shikuma yaki yayimun cikakken labari akan hakan nikuma jin kaina ya hanani yi masa tambaya a kanta kai tsaye. Na biyu kuwa shine banga Dada da Mami suna dokin da nayi tsammani zasuyi idan hakan ta faru ba kuma bansan dalili ba. Hakana Aisha aminiyata na lura ko zancen Imam bataso yayi tsayi a tsakaninmu. Wannan damuwoyin kadai nake fuskanta bayan haka bani da kowacce irin matsala.
Ana cikin haka iyayen Imamu suka zo tambayar aurena wajen su Daddy aka kuma amsa musu tare da bada izinin zasu iya kawo kudin aure kowanne lokaci. Daga ni har Imam din murnar mu ba zata lissafu ba. A ranar ne kuma ya gayamun zamuje na gaishe da Mamanshi domin ta matsa lallai tana so ta ganni. Cewa nayi ya tura Ya Sadik ya gayawa Dada don nikam bazan iya ba. Ina daki ta kirani ta gayamun cewa jibi na shirya zamuje gidansu Imam na amsa cikin ladabi na tashi na koma daki.
Mami na dau waya na kira bugu daya ta dauka. Bayan mun gaisa na dora da cewa "Mami yanzu ya Dada ta kirani take gayamun wai Imam ya turo ya Sadik ya gaya mata zamuje gidansu Mamanshi tana so ta ganni." Shiru tayi na seconni sannan tace "ita Dadan me tace?" Nace " cewa kawai tayi na shirya zamuje jibi" Mami ta sauke ajiyar zuciya muryar ta ta kara sanyi tace "ok.Allah ya nuna mana zan aiko miki kayan da zakiyi amfani dasu" jikina a sanyaye nace "toh Mami nagode" haka mukai sallama a sabule. Cillar da wayar nayi ina tunani. Menene yasa Mami bata dokin aurena? Meyasa? Meyasa jikinta yake sanyi take sauyawa a duk lokacin da hirar Imam ta shigo? Rashin sanin amsar tambayata ya sanya ni damuwa matuka domin ba haka nakeso Mami ta dau al'amarin ba. Inaso naga tsananin murnarta da farincikinta. Wayar da na cillar na sauka daga gadon na dauko na danna lambobin Aisha bugu daya itama ta dauka.
"Aisha jibi zamuje gidansu Imamu din Allah kizo gida da wuri" shiru kamar ba za tai magana ba sannan tace "Allah ya kaimu, Insha Allah Zanzo"
Kaina na dafe cikin tsananin bacin rai! Itama Aisha irin sanyin jikin Mami nakeji a tare da ita. Na rasa dalilin da ya sanya Aisha bata sakewa muyi maganar Imamu kuma ko da wasa ita bata sako zancenshi idan muna magana. Kasa hakuri nayi nace "Aisha wai me ke faruwa ne? Gabadaya bakwa nuna murna ko doki akan alakata da Imamu. Daga Dada, Mami har ke bakwa farinciki kamar yanda nake tunani ko dai bakwa sona da Imam ne? Ko yana da wata matsala ko aibu da bakwa so wanda kuka gagara sanar dani?" Cikin shaking voice Aisha tace "haba Zara ba haka bane wallahi...idan da akwai wani abu ai kinsan dole za'a sanar da ke kuma da yana da wani aibu kinsan su Daddy ba zasu amince da shi ba ko? Nidai Zara ganin abun nake kawai kamar mafarki mun rabu zan tafi makaranta zakiyi aure shikenan rayuwa zata sauya mana"
Duk da ban karbi uzurin da tazo dashi 100% ba na dan samu relief. Amma lallai inaso nasan menene a cikin ran su Mami da Dada da yake sagar musu da guiwa akan wannan lamari. Mun dan dade muna hira daga bisani mukai sallama na kira Ya Nuratu sai dai wayarta bata shiga. Na koma gadona na kwanta ina tunani duk raina babu dadi. Da naga tunanin na neman yin yawa sai na makala earpiece a kunnena na nemo kira'ar Juhany cikin Surat Yusuf na soma ji ina bi a hankali. Take wata nutsuwa ta dinga shigata raina yana sanyi bansan lokacin da bacci ya lalubo ya saceni ba.

Ranar asabar da yamma nida Aisha ne a dakina tana tayani shiryawa cikin kayan da Mummy ta aiko mun da su jiya da daddare.
Leshi ne mai tsananin kyau da tsada fari sol mai ratsin peach da gold. Style din simple skirt and blouse ne sai wani yadi mai shara shara da akai ado dashi a jikin wuyan rigan da hannun da wasu totoci.
Fuskata tas da ruwan hodar "merrycay" na fente lips dina da pink din jambakin "Mac" da saitin gold dina kirar "Dubai" nayi amfani. Na yafa mayafin kayan peach. Takalmina da jaka gold duka samfurin "Michel kors"
Nayi kyan da nake tunanin kamar ban taba yin irinsa ba. Don ba kasafai nake kwalliya mai nauyi haka ba idan ba wani occasion zan halarta ba.
Karfe biyar dai dai Imam yayi parking a cikin harabar gidanmu ya ciro wayarsa ya danna lambobina ina gaban Dada tana mun addu'a da nasihar cewa na kula na kame kaina wayar ta soma kara.
"Shine yazo?" Dada ta tambaya! Nace daga kai a sanyaye domin jikina ya fara sanyi ganin dagaske fa shirin aure nakeyi.
Har bakin mota Aisha ta rakani.
Tunda muka nufo motar yake kallona with alot of feelings acikin idonsa.
"Bestinmu ba zaki rakamu ba?"
Abinda ya soma fada kenan yana kallon Aisha! Murmushi tayi tare da cewa "a'hh wa yake shiga tsakiyar masoya ai sai kun dawo kawai...ka isar mun da tawa gaisuwar!"
Shima murmushin yayi yace "au hakane?" Ta gyada kai tana murmushi.
Ina daga gefe ina kallonsu.... abubuwa na yawo a raina. Duk lokacin da Imam da Aisha suka hadu sai na dinga jin kamar akwai wani boyayyen al'amarin da kowanne yake kokarin boyewa akan fuskarshi....sannan basa gajiya da magana ko don halinsu daya? I dont know! Wata zuciyar tace "kishi?"
Nooo! Ba kishi bane! Bazan taba zargin Aisha akan Imam ba. It cant be. Nayi maza na kawar da wannan tunanin acikin raina. A hankali na dago na dube shi jin rufewar kofar motar Aisha na daga mana hannu har muka futa daga gate din.
Murmushi yayi mun mai sanyaya rai. Nima na mayar masa tare da sunkuyar da kaina. Yana sanye cikin kaftan ruwan toka wanda ya amshe shi sosai. Muna tafiya gabana yana faduwa babu wanda yace da wani kala. Na lura yau kamar akwai abinda yake damunshi. Ya rage magana sosai.
Lokacin da muka iso Asokoro kirjina ya tsananta bugawa har sai da ya dubeni yace " ki nutsu Zarah,,kisa a ranki kamar kamar gidanku zakije"
A hankali na daga masa kai. Kafin nayi magana har maigadi ya wangale gate din tafkeken gidan
Bayan yayi parking ya bude ya futa sannan ya zagaya ya budemun na futo a hankali.
Yana gaba ina biye da shi har muka iso babbar kofar gidan ie.the main door. Zai danna bell kenan aka bude kofar.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now