A hankali na sulale na zauna a kasa ina maimaita "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" cikin zuciyata domin maķogorona ya bushe, lebbana sunyi nauyin da ba zasu iya sarrafuwa ba.
Sannan daga wadannan kalmomin ban sake gane komai ba, ban kuma jin me suke cewa ba illa kuwwar da kalaman Daddy suke mun akaina.
A hankali nutsuwa tazo mun, na samu kwarin mikewa tsaye sannan na salallaba na futo daga falon ba tare da nayi wani motsi mai karfi ba.
Allah ya taimakeni banga maganannen security din dazu ba a wajen nayi maza na futa daga gate din na bar gidan.
Ko daya ban sake tunawa da zancen daukowa Ihsan kaya ba na shiga mota ta na bar layin ina tunanin inda zan dosa.
Da Aisha tana nan gidansu kawai zan wuce na sauke nauyin da zuciyata tayi mun, ita kadai zata fahimceni ta kwantar mun da hankali ta rarrasheni.
Bayan ita ko Ihsan banjin zan iya budewa wannan sirrin balle kuma wani daban. A dalilin haka sai na samu waje nayi parking na kwantar da seat din motar kawai ina tunanin wannan irin gingimemiyar magana mai daga hankali da mamaki da tsoro da fargaba da tunani da razani. Duk yanda Mami da Ya Mahmud suka kai ga shakuwa kowa a family yasan cewa ba itace mahaifiyarsa ba amma da wasa ko tunani babu wata alama da ta taba nuna cewa Mahmud ba dan Daddyy bane. Kai!! Wannan magana ta daki kaina ta fatattaki farin cikina ta sanya ni cikin matsananciyar damuwar da bansan iyakacin ta ba.
Ni dai ina zaune a wajen na dinga jin kiran sallar magrib, amma ban iya motsawa ba, kaina wani irin sarawa yake yi kamar zai rabe gida biyu. Ko motsi bana son yi ga wayata sai ruri take yi amma na kasa samun kuzari da jarumtar da zan daure na dauka.
Haka naci gaba da zama har karfe tara, wani matsanancin zazzabi yayi gaba dani jikina ya soma rawa kamar mazari. Sai lokacin hankalina ya tashi domin wallahi bazan iya driving naje gida ba.
Dakyar na dauko wayata daga jaka, missed calls ne na Ihsan da kuma Ya Nuratu da Mubarak. Ya Omar na kira, tayi ta ringing bai dauka ba, na kira Ya Sadik shima bai dauka ba, dole na kira Mami. Bugu biyu ta dauka tayi sallama.
A sanyaye nace "Mami kina ina?" Cewa tayi "muna nan asibiti da Safiyya menene?" Cikin karfin hali nace "babu komai Mami! Me suka ce?" Cewa tayi "tana can dai tana fama amma sunce babu matsala! Ina Dada?" A tunanin Mami ina gida! Sai nace "tana nan Mami ina daki ne, Allah ya raba lafiya" mukai sallama! Ita kanta na fuskanci tana cikin wani yanayi ne, ba fargabar haihuwa ce kawai take damunta ba, da ba anan tambayoyin ta zasu tsaya ba sai taji me nake yi? Meyasa muryata haka? Ya akai bance zan taho asibiti ba!
Ina cikin wannan tunanin kiran Mubarak ya sake shigowa nayi swiping screen din a hankali na kara a kunnena tare da yin sallama. A maimakon naji muryar Mubarak ya amsa sai naji wata zazzafar masifaffiyar murya tana karaji cikin dodon kunnena."Ke babu sallama tsakanina da ke kina ji? Gargadi na kira nayi miki! Kyakkyawan gargadi ma kuwa kuma idan kunne yaji toh gangar jiki zai tsira!
Wallahi wallahi ki kiyayi shiga gonar mijina! Mijina nawa ne ni kadai bazan yi sharing din shi da kowacce yar iska ba kina ji? Wallahi duk wadda tayi gangancin tsomo kanta cikin rayuwar mijina sai tayi dana sanin zuwanta duniya gabadaya. Tun wuri ki janye kudurin auren Mubarak idan kuwa ba haka ba wallahi na lahira sai ya fiki jindadi sai na mayar da ke abar kwatance da misali l......Ina zaune da wayar a kunnena ina sauraren duka kalamanta cikin tashin hankali da tsantsar damuwa. Sai da tayi iya masifar ta da barazanar ta ta gaji don kanta sannan ta ajiye.
Wani irin nauyi naji kaina ya sake yi, zuciyata na bugawa da sauri da sauri.
Wayar Ya Sadik ta sake shigowa, amma Sam ba zan iya magana ba domin kalamaina sun yanke! Sai na kashe wayar na bude WhatsApp na tura masa location din da nake na cillar da wayar ina dafe kirjina da ya soma wani irin zugi kamar zai fashe. Tun ina iya gane halin da nake ciki har idanuna suka soma lumshewa.
------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------
KANO
A can kano kuwa cikin yammaci daya Mahmud da Amina suka fahimci juna suka kuma gamsu da hadin da iyayen nasu ke da kudurin yi a kansu. Kowanne ya gamsu da dayan dari nisa dari, musamman Mahmud da ya dinga tunanin ashe akwai irin wadannan matan masu tarbiyya da kamun kai har yanzu! Ya dinga tuhumar kansa akan yanda akai ya amince da Safna har yake shirin auren ta. Lallai gaskiyar bahaushe da yace duk Wanda ya bar gida gida ya bar shi. Zaman shi cikin turawa ko bai kowanne tasiri akan addininshi ba toh lallai ya gurbata wani bangare na tunanin shi da hankalin shi. Domin duk cikakken musulmi me tarbiyya musamman hausa fulani ba zai yi fatan ganin Safna ta zama uwar yayan shi ba. Ita kanta bata da tarbiyya da nutsuwa balle ta samu wadda zata baiwa yayan da zata haifa. Rayuwa kawai take yi kara zube kamar ta dabbobi babu kwaba babu gyara babu sanin ya kamata.
Idan kuwa ya tuno halin da take shirin sake jefa kanta sai yaji gabadaya ta sake fice masa a rai.
Washe gari ma da yamma ya sake komawa wajen Amina, har ya shiga cikin gidansu ya gayar da iyayenta mata da yake mata biyu ne a gidan da yan'uwanta. Sannan safiyar da zai taho ma sai da ya je sukai sallama ya aje musu himilin abun arziki kamar bai san darajar kudin ba sannan ya kamo hanyar Abuja ya baro Nuratu a gidansu da baudaddiyar Innarta sai next week zata taho.
ESTÁS LEYENDO
HAUSA ARAB PART 1
Ficción GeneralAlqalamin qaddara yana aiki akan kowa ba tare da zabin wance ko wane ba. Kowanne bawa da irin na shi salon rubutun, na wani ba irin na wani bane.