HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE TWENTY-SIX

815 66 4
                                    

Cikin sanyin jiki na nemi bakin gado na zauna da wayar a kunnena! da tausasawa na shiga yi mata magana!
"Aisha calm down please!ki nitsu ki maida hankalinki! just go out and take a breath of fresh air! kina yi kina cewa Lahaula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem! zaki samu relief! kinga kin fara sarkewa kina magana numfashinki ya soma tafiya ba dai dai ba! relax don Allah! i will call back in 10mins!" cewa tayi "toh" ta kashe wayar! jingina nayi da jikin gadon zuciyata cike da tausayi da kuma tunanin dalilin da ya sanya Daddyn Aisha hanata tafiya karatu a dai dai wannan gabar! sannan me result din likita ya bayyana har ya janyo wannan sauyin ra'ayin cikin gaggawa haka! ko na kira Daddyn Aisha? toh nace masa me? kirana kadai ai ba zai sauya tunaninsa ba balle ya sanya shi ya fasa abinda yayi niyya! gaskiya na tausayawa Aisha matuka domin gabadaya hankalinta da tunaninta da burinta ta dora shi akan wannan tafiya!
wayata ce ta sake ringing na daga cikin sanyin jiki! "Hello beautiful! ina kasa" Imamu ne ya iso! don haka na tashi na yafa gyalena na futo! Dada ce tace "Yazo ne?" nace "eh yana kasa Dada" sannan na wuce na futa!
a reception na same shi cikin wata irin kwalliya kamar yau ne daurin auren! babbar rigar blue black din shedda hilton sai walainiya take! ya dora hular da ta dace! hasken fatarshi ya karbi kalar kayan ainun har ba zakaso ka daina kallonshi ba! gabadaya gefen ya cika da kamshin "Tomford"! cikin murmushi ya taso yana cewa "sannu da saukowa" sanan muka gaisa! daga nan muka shiga lift zuwa hawa na goma sha tara inda suit dinmu yake! daga bakin kofa ya tsaya na shiga! tararwa nayi Mazan duk sun hallara domin da zan futa babu wanda ya futo acikinsu! don haka nayi zamana Ya Omar ya futa ya shigo dashi! kansa a kasa ya shigo har ya zauna akan lallausan farar sallayan da akai spraying daga gefe saboda dashi!
cikin ladabi ya soma gayar da Dada sannan Mami sannan A.Laila wadda Ya Nuratu ta gabatar masa! shi dai ya Mahmud ya dora kafa daya kan daya yana kallonmu irin abun yana amusing dinshi! na rasa meyasa yake wannan abun idan yaga Imamu! duka pride din shi ne yake zuwan masa da wasu expressions masu wuyar fahimta!
mintina goma sha biyar ana gaisawa da tambayar shi wadanda suka kamata a tambaya da aikinshi da lafiyarshi kafin yace zai tafi! envelope ya zaro ya aje gaban Dada yana cewa "kiyi hakuri Dada ban samu tsayawa siyan turare ba" tayi mishi godiya domin ita a tsarin Dada ba'a bata kyauta ta mayar sai dai idan ta rainin hankali ce! Ya sake dauko wani envelope din ya baiwa Ya Nuratu yana cewa ita da su Ya Anis! ita kuwa dakyar ta karba! hannun Amal na rike muka futo dashi nayi mishi rakiya har kasa da cewa gobe zai koma Nigeria kuma ba zai samu daman zuwa muyi sallama ba don akwai abubuwan da suke gabansa masu yawa! nan mukai sallama ya koma mota ya dauko wani madaidaicin jakar kwali ya bani! na amsa nayi mishi godiya don nagaji na daina musu dashi idan ya bani abu domin da fada muke karewa kuma na karba dole! sai da driver yaja motar muka dawo ciki!
Ya Nuratu na ganina tazo ta karbi jakan tana surutu! "mugani! mai aka samo? wato ke bai baki a gabanmu ba sai da kuka sauka!to ai dai zamu ga ko menene" bar mata kayan nayi na koma kujera nayi zamana ba tare da na kulata ba! gabadaya hankalina na ga Aisha da halin da take ciki! sai da ta kwance kullin da akaiwa bakin jakar sannan ta ciro saitin zinare cikin wani irin karamin akwati mai daukar hankali anyi wrapping dinshi cikin jakar gift ja! sarka, dan kunne, bracelet, anklet da zobe! kowanne an sarke tsakiyarshi da harafin farkon sunana! alamun cewa domin ni aka kera su! bayan su sai wata katuwar envelope wadda aka shirya sankararrun yan 100$ guda ashirin! wato dala dubu biyu! "kai! this guy is classy wallahi! wai shin ma ba lefe suke hadawa bane yanzu yake irin wannan hidimar?" cewar Ya Nuratu! Ya Mahmud ne ya bata amsa da cewa "to ai kudin ba matsalarshi bace kila zuwa kasuwar ma yafi masa futar kudin wahala bakiga yace wa Dada tayi hakuri bai samu tsayawa siyan turare ba?" A haka magana kawai Ya Mahmud yake yi! amma nikam sai na dinga jin kamar maganar me harshen damo yake yi! gaskiya ina matukar yakinin cewa akwai wani abu a kasa tsakanin Ya Mahmud da Imamu! to meye shi? kuma meyasa yaki gayamun?kai anya kuwa Imamu bashi da wata boyayyiyar halayya da rayuwa?gaskiya zuciyata na riyamun akwai wasu abubuwa game da Imamu wadanda bansani ba! ji nayi kaina ya soma sarawa na mike na koma daki na kwanta kwakwalwata na zabalbalar tunanika iri iri!
ban samu kiran Aisha ba sai dare! hakuri nayi ta bata ina kwantar mata da hankali, dakyar na shawo kanta daga kukan da takeyi tayi shiru ta fuskance ni! sai wajen karfe biyun Nigeria muka aje wayar na tashi na dauro alwala na soma nafila kafin na maida sallar asuba!

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now