HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE FORTY

1K 70 11
                                    

karfe daya ne na dare! Amma sam bacci ya kauracewa idanuna, tun bayan tafiyar Ya Mahmud da yamma na dawo daki nake kwance ina tunani, sallah kadai ke tayar dani, bayan nayi shirin bacci kuma na kwanta baccin yace baisan hanyar gidanmu ba.
Tunanin daren da Aisha zata tafi Kaduna nakeyi, lokutan da muka dauka a wannan dare muna hira, kayan da muka shirya na bikina a akwatina, har ta daga kayan da zansa ranar kamu tace she can't wait taga kayan a jikina, ashe har abada ba zata gani ba, ashe mutuwa zatayi? Na tuna lokacin da muka tafi gidan Rabecca a mota da ita da Ihsan take ce mana tayi mafarki da aljanna, muka mayar da ita shashasha muna yi mata dariya har taji ba dadi, ashe wai dagaske mutuwarta ake hasko mata! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! hakika babu abinda ya kai mutuwa ciwo! ashe shikenan mun rabu da Aisha sallamar da muka yi? bazan manta wayar da na kira ta suna kan hanya ba, ta dauka tace mun sun kusa shigowa Abuja ashe ba zasu shigo ba sai dai a shigo da gawarsu?kalma ta da ita ta karshe shine "i love you" bata taba gayamun haka a waya ba sai ranar, ashe bankwana take mun. Na tuna yanda ta tsangwami kanta akan Ya Aslam bai mata komai ba, ashe wai shine abokin ajalinta! kai!! wayyo Allah rayuwa! ashe kuna tare da mutum cikinku baku san wanda zai riga tafiya ba, ashe amintar mu da Aisha ba mai dorewa bace.
ire iren wannan tunanin ne suka cika kwakwalwata taf, suka hanani ko runtse ido, kodayake 90% din memoryn cikin kaina Aisha ta cinye shi, babu wani fegi a rayuwata da bata taba ba, ko lokacin da tana raye bana rabo da tunaninta domin tana cikin duka sabgogina da mu'amalata da rayuwata. ta yaya zan iya goge wannan tarin abubuwan cikin kaina naci gaba da da rayuwa babu Aisha cikin sauki? ba zaiyu ba!wani abu ne mai matukar wuya mai bakar wahala! ban ankara ba naji an soma kiran Assalatu sai na mike nayo alwala na shimfida sallaya na soma nafila ina neman sauki da yardar Allah da amincinsa da tallafinsa a kaina.
bayan na idar da sallar asuba kuwa carbi na dauka na karanta kulhuwallahu kafa dubu hadiyya ga Aisha!
Daga haka kuma bacci ya daukeni akan sallayar sai farkawa nayi Ya Nuratu na tashina wajen 12 na rana. sannan nayi break sama sama na koma daki na kwanta naci gaba da tunanin Aisha! sai bayan sallar azahar sannan nayi wanka na zura plain gown da hijab nayi sallah! ina cikin ninke kayan sallar Amal ta shigo a guje tana "Aunt Zara i'm back" wallahi sai yanzu na tuna bana ganin ta cikin gidan! rage tsayina nayi nace "ina kikaje Amal?" cewa tayi "Abbu ne yazo muka tafi gidan Hajiya" oh sai lokacin nagane. gidan kakanninta suka tafi da babanta! hannunta na kama muka futo parlour dai dai lokacin Ya Mahmud ya shigo cikin shigar fara sol din shedda karamun dinki kansa babu hula. tuni falon ya kacame da kamshin "La NUIT" sai da suka soma gaisawa da Dada sannan muka gaishe shi!
" Zara! shirya ki rakani gidansu Aisha nayi gaisuwa"
sai da gabana ya fadi, jikina yayi wani irin sanyi kafin na mike cikin rashin kuzari na nufi dakina. abaya na dora kan rigar jikina,ko turare bansa ba duk da jikina har yanzu yana wannan azababben kamshin amarcin. na zura slippers dina na dauko waya na futo!
A hanya babu wanda yake magana illa karatun shuraim da ya karade motar cikin surat yunus! har muka iso gidansu Aisha! wani irin bugu kirjina keyi kamar wadda tayiwa sarki karya. lokacin da mukayi parking cikin gate din kuwa kamar na koma nace na fasa! A hankali nake tafiya Ya Mahmud na bayana har mukaje kofar falon na danna kararrawa. minti daya Iky ta bude! ina ganinta hankalina ya tashi, ita kuma kawai sai ta rungumeni ta rushe da kuka! sai da tayi kuka mai isarta sannan ta gayar da Ya Mahmud wanda ya nemarwa kansa wajen zama a daya daya daga cikin kujerun falon. cikin tausayawa yayi wa iky gaisuwa sai ta kama hannuna tace "ki shigo su Umma suna ciki!" hannuna cikin nata ta tunkari dakin Aisha! wani irin feeling na tasowa tun daga tsakar kaina har kafata! muna shiga na kwace hannuna na tsaya still! a sakamakon ganin yanda aka hargitsa dakin, Umma, Hajiyarta, da Yayarta ke ta aikin hada kan kayan dakin an zubo da duk kayan cikin wardrobe dinta ana sakawa a akwatina! idona bai tsaya ko'ina ba sai kan wata abaya yar swarosvki wadda ta saka ranar da ta rako Imamu school dinmu ran birthday dina! sai lokacin na tuna da Imamu da maganar aurensa da ke kaina! a hankali na isa gaban kayan na dago rigar na rungume, sassanyan kamshin Aisha ya doki hancina, wannan ba "Empire oud" bane kadai har da karin turaren oil na "AJMAL" wanda ni na siyo mata shi a Jedda na kawo mata.
Wani katon lump naji makoshina ya hada, wani abu kamar amai ya taho makoshina da gudu da karfin gaske yayinda zuciyata tayi wani irin yunkuri, kan na gane me yake shirin faruwa wani magigicin kuka ya subuce mun! Na kifa kaina akan kayan na shiga kurma kuka mai tsananin karfi da radadi da ciwo da azaba irin wanda ban taba yi ba a rayuwata! Hakika babu akwai radadin da ya kai na mutuwa babu ciwon da ya kaishi zafi da tsanani.
Bamu samu gaisawa da su Umma ba bamuyi sallama ba dakyar suka banbareni daga cikin kayan dana dinga bi daya bayan daya ina sinsinawa ina kara gunjin kukana, Hajiya ce ta dankawa Ya Mahmud hannuna tace ya tafi dani gida, Umma ta futo dakin idanunta jajawur da katon diary din Aisha ta iso gareni ta miko mun
"karbi wannan Zara! ke kadai ya dace ki aje shi a wajenki. Nasan kece kadai kikasan abubuwan da suke ciki, bazanso a kona ba, kuma bazan so na bude mata siririn ta ba!" kamar zan shide saboda kuka, haka muka futo ina layi ina rangaji muka shiga mota! Na kifa kaina kan cinyata naci gaba har muka iso gida! Nan ma cikin sauri na balle murfin motar na sunkuci diary din na nufi gida a guje, ban saurari su Dada da ke parlour ba na wuce Dakina na fada gado inajin kamar zan futo da zuciyata gabadaya nayi kukan da ita.
Ya Mahmud ne ya shigo falon cikin sanyin jiki, shima yana ta share hawaye da handkerchief dinsa. Dada ce tace "Meye ya faru Mahmud? wani abun ta sake ji?" a hankali yace "Kukan ne samun relief dinta Dada kada ku rarrasheta, rashin kukan yafi kukan illa. ku kyale ta tayi tayi zuciyarta zatayi sanyi" yana gama fadin haka ya juya ya bar gidan cikin matsanancin tausayi da karyewar zuciya! yana cikin tafiya ya samu guri ya tsaya, kifa kansa yayi akan steering wheel ya soma kuka mai tsuma rai, ba kukan Aisha yake ba, kukan nashi rashin da yayi shekaru sama da goma yake, wanda ya dawo mishi fresh kamar sabon yanka, rashin da har abada yake tunanin ba zai mayar da gurbinsa ba! Rashin Jawahir, mace guda daya wadda yayi wa son da ko a labari baiji irinsa ba, mutum guda da bacci kadai ke rabasu, aminyarsa abokiyar shawararsa at the same time matar da ya dora dukkanin burinshi a kanta! wadda lokaci daya mutuwa ta shammace shi ta dauke masa ita kwanaki biyu bayan daurin auren su!
ba zai taba mantawa da 25th april ba
wata safiya mafi muni a rayuwarsa. har karfe daya na dare suna kan waya da Jawahir suna tattauna yanda tsarin zamansu zai kasance, Shi yana so su tattara su koma London su dora akan karatunsu kamar yanda suka faro shi tare yayinda ita take son su zauna a gida. a karshe ta hakura tabi ra'ayinsa domin ita ba mutum ce mai gardama ba.
ba suyi sallama ba, batir dinsa ne ya mutu ya cillar da wayar cikin jin haushi. washegari da safe ya wayi gari da mutuwar ta, babu ciwon kai ba zazzabi, babu zato ba tsammani, ruwa take sha kawai ta kware, daga nan ta fadi, a lokacin akayi aka gama Allah ya karbi abar shi! Idan ya tuna halin da ya shiga a wannan lokaci, sai yayi ta mamakin yanda akai rayuwarsa ta saitu yanzu, har yake dariya yake kwalliya yake shiga cikin jama'a! A wancan zamanin da shi da mutum mutumi basu da bambamci, rayuwa ya dinga yi mara hope ko building future, babu goal babu target babu sa rai da wani jindadi a rayuwar gaba.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now