HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE FORTY-THREE

814 63 20
                                    

Yuppy! Its another update😀😀 I'm too sweet right?💃😀😀
Ok if you are happy pray for me on this blissful day🥰
Don't forget to recite surat kahf if you are reading this today!
Jumua Kareem!

Ringing din wayar sa ne ya tashe shi daga baccin da ya fizge shi dakyar akan king size bed din dakin da Mami ta mayar mishi nashi! har wayar ta tsinke bai samu kokarin tashi ya dauko ta ba, sai ma sake mirginawa karshen gadon yayi yana ci gaba da tunanin damuwoyin da suka sanya shi gaba, da farko dai a zamanshi a gidan Mami wancan zuwan na bikin Faisal da wannan ya lura da cewa akwai babbar matsala tsakanin Mamin da maigidanta Alh Idriss kuma a dukkan nazari da binciken da yayi ya tabbatar duka matsalolin akan kudi ne, kudin Mami yake ci ita kuma ta rasa ta hanyar da zata bullo masa ta karba ba tare da sun samu baraka ba. Yafi baiwa kansa amsar cewa rantar kudin Alh Idris yayi sanadin tuhumar da EFCC take masa akan mukuden kudaden da ya handame lokacin da yake kan kujerar ministan tsaro na kasa. Rigingimu ne kala kala a kansa musamman da ya kasance wannan sabuwar gwamnatin ta abokan adawar su ce. Shi dai Mami bata bude baki tayi mai bayanin komai ba, kuma bayaso ya tare ta da maganar ba tare da ta yi masa ba. Amma yana tsoron kada Alh Idris ya durkusar da baiwar Allah don yana ganin tana da hakuri ba zata daga masa hankali ba. Amma ya rasa ta ina zai fara, me zaiyi? Lallai yana bukatar yin wani abu akai kafin wata matsalar ta faru. Sam mutumin bashi da kirki, kudin Mami kawai ya hanga yayi amfani da dangantakar yayansa da baban Zara ya auri Mamin ba wai don so ba. Ya tabbatar kuma bata jin dadin zama da shi.

Matsalar shi ta biyu itace Safna da halin da take son jefa kanta ciki. Gabadaya ta sauya ta chanja sauyi mai ban mamaki, ta daina kiranshi gabadaya sabanin da, da zata kira shi a kalla sau uku a rana ko tana wajen aiki ne kuwa. Sau da yawa shi yake kin daukar wayar don kar ta ishe shi da surutun ta. Amma yanzu Sam ta daina, sai ya kira sau goma bata dauka sau uku ba. Sannan her voice is always very weak, soo weak kamar mai magagin bacci, da ya soma tunanin ko bata da lafiya ne ko kuma wani abun ke damunta sai dai ya san ta a matsayin extrovert wadda bata iya boye feeling dinta ko sirrinta wani abu na rayuwarta. She is outspoken and straightforward, idan tana da matsala shi zata fara tunkara da ita su warware tare. Hankalinsa bai tashi ba sai jiya da ya kira ta dinga bashi amsar shirme, a karshe ya kashe wayar tasa. Zato zunubi ga Musulmi amma gabadaya ya kasa tsaida zuciyarsa ta daina tunanin me Safna take! "DRUG" kalmar da ta fado masa rai kenan! Wani irin dokawa kirjinsa yayi ya mike zaune yana fadin "innalillahi wa inna ilaihi rajiu'un" Allah yasa hasashen shi ba gaskiya bane!
Cikin sauri ya dauko wayarshi, ganin misscall din Daddy yayi amma tsabar rudanin da yake ciki bai fara kiran Daddyn ba ya shiga neman layin Safna. A kulle wayarta ta take. Ya furzar da huci mai zafi kafin ya lalubo lambar engineer babanta. Bugu daya ya dauka suka gaisa cikin mutunta juna, daga nan yake tambayar shi Safna cewa yana ta kiran wayarta a kashe. Cikin nutsuwa Engineer ke masa bayani
"Safna tana Scotland Mahmud taje gidan kawarta joyful" ji yayi makoshinsa ya bushe, dakyar ya sake bude baki yace "me taje yi wajenta har ta aje aikinta saboda shi?" Engineer yace "a yanda tace mun dai wai joyful din sun rabu da saurayinta tana kokarin aikata suicide shine taje ta zauna da ita ta kwantar mata da hankali....amma" kit Mahmud ya latsa madubin wayar ya kashe wayar ya cillar gefe tare da dafe kansa. Yau anyi Uban banza uban hofi. Bakar wahalar da yasha kafin ya samu nasarar raba Safna da Joyful ba ta wasa bace. Joyful shaidaniyar baturiya ce mai hadari, tun ranar da abokin aikinsa Dr.Ahmad mutumin Yemen ya ganshi da Safna ya gaya masa gaskiyar abinda ya sani game da ita, yace masa baisan halin Safna da tarbiyyar ta ba amma yana ganinta da Joyful, ita kuwa Joyful ko turawan tsoron sharrinta suke yi da shaidancinta. Daga nan Mahmud ya soma daukar matakin akan Joyful, Safna ya fara jawa kunne akan ba ita ba Joyful idan kuma bata yarda ba toh sai dai su rabu da shi, wannan barazanar ta sanya Safna shiga taitayinta ta hakura da hulda da Joyful domin tsoron rasa masoyin nata. Shikuma ganin taji maganar sa yasa yaji dadi ya sakankance cewa a Danny a hankali zai iya saita ta ya dawo da ita turbar da yake so tabi, sai akayi dace kuma ta zama kamar rakumi da akala, duk abinda ya sata shi take yi babu musu, wannan ya kara bashi kwarin guiwa wajen neman aurenta. Bai San cewa mata irinsu Safna sun zarce sanin shi da wayonshi da dabararshi ba, bai san san cewa gaula kawai ta mayar da shi ba.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now