Unedited
Ina shiga gidan Mami tace mun na juya Driver ya maida ni gida wai gobe da yamma zamu tafi Jeddah da Dada an kammala komai! Baki na saki galala ina kallon Mami raina a matukar bace.
Cikin muryar kusa da fashewa da kuka nace "Haba Mami yanzu gobe za'ai tafiya sai yau za'a gayamun don Allah! Bayan ina da abubuwa masu yawa a gabana nima, an kama an saka biki wata uku kacal ni dai abubuwan sun yi mun yawa wallahi!"
Banza tayi mun ta mike ta futa daga dakin nikuwa na kwanta a gado na rusa kuka don wallahi tafiya wani yaje shine karshen abinda nake tunani a yanzu. Kuma nasan abinda tafiyar take nufi, a kalla muyi 3weeks idan kuma Daddy yaga dama yace mu wuce Dubai ko London Dada ta huta. Nikam kowanne minti daya a wannan lokacin amfani ne da shi a gareni bana bukatar na bata shi da kowanne abu da ba zai amfanar da rayuwar da nake shirin fadawa ba.
A hankali naji an dafa bayana ana bubbugawa, na dago da sauri don banji shigowar ta ba. Cikin sanyi ta soma magana
"Zara sau nawa kike so na maimaita miki cewa hakuri ake da rayuwa? Ba abinda kake so kake samu ba domin ragamar rayuwarka ba a hannunka yake ba! Allah shine mai komai kuma shine abun dogaro a kowanne yanayi mutum ya tsinci kansa! Ni ya kike so nayi da kaina? Da inada Wanda zanyi wa kukan nima zama zanyi? Abubuwan da suke kaina suna da yawa Zara ciki har da damuwar da kike ciki, bana son ganinki cikin wannan halin ke da Mahmud hankalina tashi yake yi! Sannan wannan tafiyar kin saba da ita kullum da ke akeyi to menene sabo? Dada ce fa Zara? Wa take da shi da zata dauka bayan ke? Ke kina nan kika kukan tafiya ita Badi'a yanzu tana can tana masifar an kare a kanmu kin zama jelar Dada kamar ke kadai ta mallaka ko ta manta ita haifi Nuratu ni ban sani ba. Yanzun ta gama zagina a waya! Toh ina zan sa kaina? Na mutu? So Kuke stress da tashin hankali ya kasheni? Wannan auren kuma da kike ganin kamar na damu lallai kiyi ba don komai bane ina gudun abubuwan da suka faru akan Mahmud su juyo kanki ne, Dada akan aure bata ragayya bata lankwasuwa kuma bata rangwame, tun kafin zama da ita ya zame miki matsala nake son kiyi auren a huta tunda idan kin zauna me zakiyi? Irin wannan tunanin da damuwar har ciwo ya kama ki? Ina sane cewa ba wai kina son Mubarak bane kawai kin amince ne saboda kinga na amince da shi! Addu'a kullum nake miki Allah yasa ya zama mafi alkhairin zabi a gare ki ya kuma baki rayuwa mai albarka. Please ki saki ranki ki kama harkokin ki!"
Ajiyar zuciya na sauke a hankali cikin gamsuwa da kalaman Mami tare da wani irin tausayin ta. Rungume ta nayi kawai ba tare da na iya cewa komai ba.Washegari ina tashi na shirya na futa. A super market na tsaya nayi siyayya sannan na dau hanyar gidansu Aisha! Duk yanda zuciyata take karyewa idan na shiga gidansu ban daina zuwa ba, domin ina ganin kamar kulla zumunci da kannenta da iyayenta shine kadai sakayyar da zanyi wa soyayyar mu. Ko yanzu da na iso cikin gate din sai da nayi kuka na na share hawaye sannan na futo ina amsa gaisuwar masu kula da gidan. A nutse na danna bell din shiga cikin gidan. Iky tazo ta bude! Tun rasuwar Aisha bata koma Ulul Albab ba. Babansu yace ta hakura ta samu makaranta a Abuja taci gaba ko don ta rage wa Umma damuwar rashin Aisha!
Tana ganina ta rungumeni tana mun sannu da zuwa! Duka iyalan suna parlour domin ana public holiday ne. Har kasa na durkusa na gayar da su Umma suka dinga amsawa cikin kulawa da kauna mai yawa, duk da suma idan sun ganni jikinsu mugun sanyi yake yi amma suna kokarin boyewa don kar su karya mana zuciya. Dai dai ne lokacin da zanzo mu rabu ba muyi kukan Aisha ba. Bayan mun gaisa nake musu sallama sukai mun fatan alkhairi sannan na futo hannuna cikin na Iky tana bani labarin sabuwar makarantar ta. Sosai take bani matsayin Yayarta, idan tana da damuwa ni take daukar waya ta gayawa, idan abun farin ciki ne ya same ta haka don haka munyi wata irin shakuwa bayan mutuwar Aisha ta ban mamaki. "Ya Zara kar ki manta ki siyo mun turaren don Allah! A Jeddah ake durawa suanshi Marwa!" Murmushi nayi ina mamakin kamanceceniyar halin su da Aisha! Komai nasu iri daya ne, kamanni ne kawai suka bambamta da su don ita Iky fara ce tas kuma bata da tsayin Aisha! Amma tafi Aisha kyau sosai! Sai dai duk wani hali na Aisha itace photocopyn shi! Shiyasa nake jin ta cikin raina sosai. Muna zaune a mota tana gefena muna hira har Daddynsu ya futo. Cikin mamaki yace "aww Zara yanzu daman baki tafi ba ke da kike da tafiya a gaba tazo ta saka ki a gaba da surutun ta ko? To maza futo ki kyaleta parrot kawai!" Dariya nake yi ita kuma tana bubbuga kafa wai ance mata parrot! Jaka na bude na bata kudi sannan ta futa suna daga mun hannu ita da Daddyn har na bar gate din.
Allah sarki rayuwa! Wai yau babu Aisha! An nannade littafin ta an rufe an bude wani sabon babin rayuwa a gidansu! Duk son da suke mata yau da gobe ta mayar musu da rashin ta jiki, sai dai a tuna ta ayi mata addu'a! Haka rayuwa take! Don haka bawa ya tsaya ya gyara dangantakar sa da Ubangiji komai son da ake maka mutuwar ka ba zata tsaida komai na rayuwa ba. wani abun ma sai baka nan zai futo.
CZYTASZ
HAUSA ARAB PART 1
General FictionAlqalamin qaddara yana aiki akan kowa ba tare da zabin wance ko wane ba. Kowanne bawa da irin na shi salon rubutun, na wani ba irin na wani bane.