HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE NINETEEN

873 63 0
                                    

Hawayene suke gudu akan fuskata kamar an balle famfo! tsananin tausayin Mami ya kamani tare da haushin Mahmud wanda ya janyo mata duka wadannan bakin cikin! Nayi matukar jin bacin ran abinda Dada tayi! shin fushi hauka ne? in ka haifi mutane halittarsu kayi? kawai ta dinga batawa iyalanta rai? ina ruwan Mami cikin wannan laifin? meye sukayi mata me zafin da zata ce ta cire su cikin jininta? wannan ba daidai bane! wannan kuskure ne!
"yanzu meye abun yi Ya Sadik? ko Kawu Sulaiman zamu kira mu sanar dashi?" murmushi yayi mai ciwo sannan yace "kin manta wanene Kawu Sulaiman din kenan! idan har bai kara bata al'amarin ba na tabbatar sai dai ya kara lalata shi! sannan wa kike tunanin zai iya fuskantar Dada a wannan yanayin? kawai shiru za'ayi a kyaleta zuwa wani lokacin kafin ma a tare ta da ban hakuri ko wata magana!" girgiza kaina nayi cikin gamsuwa don nasan hakanne kawai mafuta! tare muka mike muka koma ciki! lokacin wani sabon scene ne yake faruwa! Mahmud ya kafe lallai sai ya tafi ba zai sake kwana a Nigeria ba yayinda Mami tace babu inda zaije! kowanne kuma kuka yake kamar ranshi zai futa! dukanmu tsayawa mukai muna kallonsu babu wanda ya tofa har Ya Mahmud ya saba jakarsa ya janyo troley da yazo da ita ya soma tafiya cikin fushi!
Mami tana daga zaune ta daga murya tace "Mahmud ka tafi kenan ka barni? zaka tafi domin ka nuna mun cewa bani ce na haifeka? ka tafi don ka nuna mun iyakata akanka? ka tafi don ka tabbatar cewa zaka iya rayuwa babu ni? kanaso ka nunamun cewa harda ni zakai fushi Mahmud? kaje! ka tafi! bazan mutu ba idan kwanana bai kare ba amma zan rayu da cikin tsananin bakin cikin iyakar da kayimun a rayuwarka!"
Cak! ya tsaya jikinsa har wani kadawa yake don tsabar fushi da bacin rai! kafin ya yarda da jakar hamnunsa ya dafe kirjinsa da sauri yana wani irin tari!lokaci kadan kwayar idanunsa ta juye ya soma futa hayyacinsa gabadaya muka rufu kansa Ya Omar ya tare shi jikinsa lokacin da ya tafi luuu zai fadi! Mami cikin kuka ta zari key tana cewa mu tafi asibiti mu tafi asibiti!
dukanmu muka dunguma muka futa! Ya Omar ke driving cikin high speed nikuma ina gefenshi yayinda Mami da Ya sadik ke bayan bakar Jeep din suna rike da Ya Mahmud da ke ta shure shuren mutuwa hannunsa rike da gefen kirjinsa na hagu! babu wanda yasa rai da Mahmud kafin muka isa Lima hospital ! cikin gaggawa likitoci suka karbe shi suka rufu akansa! dukanmu mu uku kuka muke ba me rarrashin wani sai Ya Omar ne kadai ke kai da kawo cikin asibitin! cikin ikon Allah kafin karfe uku sun shawo kan matsalar har numfashinsa ya daidaita sannan aka turo shi zuwa dakin da aka tanadar mana! Bacci yake yi har aka soma kiran assalatu Mami ta dubi su Ya Sadik tace "Sadik kuje gidajenku kuyi sallah ku dan runtsa da safe sai ku dawo tunda jikin nasa da sauki!" Ya Sadik ne kawai ya yarda amma shi Ya Omar cewa yayi sai ya farka tukunna bai kamata abarta ita kadai ba! sannan tace ya wuce dani ya ajeni a gida nasa su Aya su shirya breakfast na kuma debo mata abubuwan da zasu bukata nace "toh" muka baro asibitin!

Bayan na dawo gida sallah nayi na kwanta naji ko zan iya runtsawa amma sam baccin yace baisan wannan ba! daga baya na mike na shiga kitchen na soma aikin da kaina duk yanda Aya da Juliet suke mun magiyar na bari! kunun gyada na soma damawa sannan na hada chicken p.soup da dankali na soya doya na zuba ruwan zafi a flask na hada komai cikin babban kwando! sannan na koma daki nayi wanka na shirya na futo! Ya Sadik ne ya sake dawowa ya daukeni wajen 7:30 muka tafi! a hanya yake sanar dani Ya Mahmud din ya tashi kuma jikinda sauki! nayi hamdala! lokacin da muka isa a zaune muka same shi kan gadon yana sallah!
Bayan mun gaisa da Mami na tashi na hada mata tea na zuba mata soup din a bowl na tashi naje gabanta na zauna na kai cup din bakinta idanuna a raunane dole ta karba! a hankali na dinga bata abincin har taci me yawa! murmushi tayi tace "i am okay haka Zahra bani ruwa!" na mike da sauri na dauko ruwa cikin fridge a dauki cup na zuba na bata! "Allah yayi miki albarka!thank you!" wani sanyi naji a raina! shin akwai abinda yafi farantawa iyaye dadi? babu!! mikewar da zanyi na ga Ya Mahmud yana kallona cikin murmushi! na aje kayan na matsa gaban gadonshi na soma gayar dashi! ya amsa cikin kulawa sannan nace "ya jiki naka?" yace "Alhamdulillah Zara! kinyi feeding Mami ga mara lafiya kina kallonshi ko?" murmushi nayi zan magana Mami ta taso itama da cup dinta a hannu tana cewa "kwantar da hankalinka bayan ga Maminka kusa kuma wacce Zarah ce zatazo baka abinci" sosai muka sa dariya gabadaya! ina kallon lokacin da Ya Sadik yake goge kwallar tausayi! Mami ta shiga bashi abincin! yanzun tambayata da akalar tunanina ya juya ga son sanin wacece ta haifi Mahmud? tana ina kuma yanzu? ya akai Mami ta maye gurbin uwa a gareshi?
Mami ce ta dawo dani daga tunanin da nake yi! "Zara kina jina?" na amsa ina kallonta! tace gaba "abinda nake so dake yanzu ki tafi gida ki hada kayanki ki koma gidan Dada. daman buki ne ya kawo ki kuma na kammala banason wata maganar ta sake shigowa kinga ba'a wajena kike ba Dada zata ga kamar nice na hanaki tafiya kinji?" duk da banso ba amma dole nabi umarnin Mami don banason a sake bata mata rai a kaina! da haka mukai sallama Ya Sadik ya sake daukata muka tafi nace kawai mu wuce gidan ai ba wasu abubuwa masu yawa ne a gidan Mamin ba!
ko cikin gate din bai shiga ba ya juya nikuma na iso cikin gida kirjina na bugawa don bansan me zanje na tarar ba nima! babu kowa a parlour na leka kitchen wayam! sai na tafi dakin Dada da sallama a bakina!
Tana zaune akan dadduma ta kammala addu'o'inta tayi shiru kawai!
sai da na daga murya nayi salllama sannan tayi firgigit ta juyo tana amsawa! a sanyaye naje gabanta na zauna na soma gayar da ita! cikin kulawa ta amsa kamar koda yaushe saidai ina iya karanto damuwar da ke kan fuskarta! "An kammala buki lafiya?" nace "lafiya lau Dada ina Baba Rabi ne?" cewa tayi "Baba Rabi taje Kaduna amma da yamma zata dawo" nace "toh bari na shiga dakina". kwanciya nayi ina maida numfashi! tunani na rasa wanne zanyi acikin damuwoyin da suke damuna! a yanzu babu abinda yafi dagamun hankali irin abinda ya faru tsakanin Dada da Mami! tunanina wacce hanyar zanbi na warware su? me zanyi? kaina yayi nauyi! gashi muna dab da fara exams! kai har makarantar ma ta futa a raina fa! komai ma duniyar baya mun dadi wallahi! mikewa kawai nayi na shiga toilet na futo na nufi kitchen na shiga girki! barzajjiyar wankakkiyar shinkafa na futo da ita na dauko steamer na hada komai na dora akan gas! albasa manya guda biyu na yanka da yellowbel pepper da sweet pepper! sannan nayi grating attarugu na daka spices cikin mini motar! bayan na kammala na ciro hanta da koda a freezer na yayyanka kanana na dora su a wuta su dahu!
cikin mintina kadan na hargitsa wajen da kamshi! kafin azahar na kammala tattausan dambun shinkafa da sauce din hanta da koda! na samu coolers na zuba na asibiti na hada cikin kwando na rufe sannan na koma daki nayi wanka da sallah! sannan na shirya cikin maroon straight skirt na swade da armless top fara sai na dora short kimono akai! na nade kaina da farin gyale na saka farin sandal na dauko jakata na futo! a parlour na samu Dada tana cin abincin dana zuba mata tana korawa da five alive! "kai amma Zara dambun nan yayi dadi! yayi taushi sosai Allah yayi miki albarka!" cikin murmushi na isa gabanta na zauna nace "ameen Dada! zan shiga school ina da test!" tace "toh Allah ya kiyaye! sai kin dawo!" na mike na shiga kitchen na dauki basket dina na futo! kamar zatai mun magana kuma sai tayi shiru! na wuce na futa! asibiti na wuce kai tsaye! Mami tana sallah Ya Mahmud na zaune da alqur'ani a hannunshi yana karatu cikin zuci! na wuce na aje kwandon abincin kan tebur sannan nazo na zauna kan kujerar dake gefen gadon! rufe alqur'anin yayi yana murmushi! kin dawo Zara? nace "eh ya jikin?" cewa yayi "dasauki Alhmdllh" dai dai nan Mami ta shafa addu'a ta juyo tana cewa "Zahra me kika dawo yi nan? banason matsala fa? a ina kika samo abincin nan?" dan turo baki nayi cikin murya kasa kasa nace "Mami i wanted to cook your favourite! kuma makaranta nace wa Dada zanje! bata san ina gidanki ba ta zata daga gidansu Ihsan na koma gida! i am very careful Mami ba zata gane nan nazo ba" kada kai kawai tayi ta mike tana ninke abun sallar ta aje shi! "Mami check what i cooked for you!" na fada da wide smile akan fuskata! murmushi tayi ta wuce gaban tebur din ta bude babbar food warmer din nan da nan bakinta yayi forming O shape! "Zara dambu? kai amma naji dadi! Allah yayi miki albarka!" na lumshe idanuna ina cewa ameen! Mahmud ta kalla wanda yake ta murmushi tace "kaga Mahmud kamar ta shiga ranmu dazu kake maganar yaushe rabon da kaci dambu da danwake" sake fadada murmushinsa yayi beauty point din fuskarsa duka suka koma ciki! baice komai ba! shi ta soma zubawa ta mikowa! ya amsa ya soma ci! lomar farko ya tsaya ya dubeni "wait? did you make this?" na girgiza kai! "with your hands?" na sake girgiza kai! "are you sure?" dariya sosai ya bani yanda yake tambayan yana juya ido kaman wani mace! na dade inaso na gano cewa ko dai bashi ne mutumin da na gani a Saudi ba? wannan is soo caring and kind! wancan kuwa zalinci da mugunta kawai yasa a gaba! koda ke har yanzu ina tunanin kodai saboda idon Mami yake mun haka! cikin annashuwa muke hira suna cin abincin kowanne na yaba dadinshi! kafin ayi knocking kofa! Faisal ne ya shigo hannunsa rike da takardu! "ka dawo Faisal?" cewar Mami! cewa yayi "na dawo Mami an kammala komai inaga zuwa gobe zaku iya tafiya! tunda ya samu sauki!" sai lokacin na gayar da shi tare da tambayar Ihsan yace "ai kin kyauta da kika gudu tana nan zata hadu dake" nayi murmushi kawai! sai bayan ya tafi na dubi Mami nace "Mami ina zakije?" ajiyar zuciya ta sauke tace "London zamu tafi da Mahmud! asama mishi proper medication!" tabe baki nayi kamar zan kuka nace "Mami i will go with you!" dariya tayi tace "kin shirya tambayan Dada ko?" na hade fuska! ta sake cewa "lastweek ne ma take cemun tayi magana da Daddy yace a bari sai kinyi hutu zakuje shopping din kayan daki" duka idanuna na zaro! wanne irin shopping din kayan daki? "kamar baki san komai ba! bikinki saura wata hudu duk da wata dayan da aka kara! idan ba'aje yanzu ba kayan ba zasu zo kafin bikin ba" wani irin tashin hankali naji ya ziyarci kaina! noo! not me! i'm not getting married! not soo soon! infact na soma tunani daban akan auren Imamu! ina sonshi sosai amma na dena burin aurenshi! it can't be! lokaci daya na mike na hada jakata na dau key nace "Mami sai anjima na tafi" baki sake take kallona sannan tace "meye haka? daga maganar siyan kayan daki? toh haka za'ai auren ba'aje anyi siyayya ba?" cikin muryar kusa da fashewa da kuka nace "Mami bazan yi aure yanzu ba! na fasa!" na bude kofar na futa ban saurari kiran da take mun ba!

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now