HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE FIFTY-THREE

792 54 9
                                    

Wani irin tuki nake yi bana ganin gabana don tsabar takaicin da Mubarak ya hada mun. Cikin ikon Allah na isa gidan Ihsan, ko amsa gaisuwar mai gadi ban tsaya yi ba na figi motar a guje zuwa cikin gidan. A tsakiyar harabar filin nayi parking na balle murfin motar na futo. Sai dai ban ma kai ga shiga gidan ba na ga maigadin ya sake wangale gate din, motar Mubarak ta danno kai wanda ban San lokacin da ya biyo ni ba.
Tsaki nayi na fasa shiga ta ainihin fuskar gidan don kar na tsaya danna bell yazo ya taddani na zagaya na bi ta kitchen na shiga ainihin babban falon Ihsan. Ina shiga suna saukowa daga bene ita da Faisal yana dauke da Amani a hannunsa. Ganin halin da nake ciki ya sanya su karasa saukowa da sauri Ihsan ta nufo ni tana cewa "Zara! Lafiyarki kuwa? Me ya faru?" Kawai rungumeta nayi na sa kukan da ya sake basu tsoro! Faisal ne yace "kinga ku zauna! Calm down Zara! Ki nutsu dan Allah ki gaya mun me yake faruwa?" Dakyar Ihsan ta kaini kan kujerar da ke gefena muka zauna shikuma Faisal ya dora mata Amani akan cinyarta sannan ya zauna akan kujerar dake saitin mu yana kallona cikin damuwa. Ban samu sukunin yi musu magana ba mai rainon Amani tayo sallama ta shigo, sannan ta durkusa tace "Alhaji kana da bako a waje" cewa yayi yana zuwa ya mike ya futa cikin sauri.
Ihsan ta sake matsowa kusa dani ta dafa kafadata tace "Zahra don Allah kiyi shiru ki gaya mun abinda yake faruwa kin daga mun hankali wallahi! Ko jikin Ya Mahmud ne?" Girgiza kai nayi a hankali ta sake cewa "toh menene?" Cikin sanyin murya nace "Ihsan gaskiya na hakura da auren Mubarak! Idan na aure shi ciwon zuciya zai saka mun" na sake fashewa da wani kukan, takaicin abinda yayi mun yana dawowa kaina daya bayan daya.

Shiru tayi na wasu dakiku tana kallona kafin ta mike ta nufi hanyar kitchen. Mintuna biyar ta dawo dauke da madaidaicin tray a hannunta tazo ta aje a table din da ke gefen kujerar da nake zaune sannan ta dauki kwalin fresh milk ta girgiza ta cika mun karamun glass cup ta miko mun.
Babu musu na karba na kafa kaina na soma kwankwadar madarar sanyin ta yana ratsa zuciyata da jikina yana saukar mun da salama. Ban tsaya numfashi ba sai da na shanye tass na aje kofin.
Zanyi magana kenan Faisal ya shigo, daga kofa ya tsaya yace wa Ihsan "saka gyalenki Mubarak zai shigo" kallona tayi ta saki murmushi sannan ta mike taje ta dauko gyale ta dawo ta zauna tana kallona cike da tsokana. Ni kuwa na daure fuska tamau kamar ban taba dariya ba. Faisal ne ya sake turo kofar ya shigo Mubarak na biye da shi yana wani munafikin murmushi. Sai da ya soma daukar Amani da ke kwance akan kujera sannan ya dawo ya zauna a gefen Faisal yana cewa da Ihsan "Madam Sannu da kokari ban samu zuwa ganin baby ba sai yau"
Cikin tsokana Faisal yace "ah toh gashi nan ai biko ya kawo mana kai" sukai dariya gabadaya sannan suka soma gaisawa da Ihsan sai wani sunkuyar da kai take yi kamar wani surikinta. Nidai ko kallon inda yake banyi ba.

Sai da yayi gyaran murya sannan yace wa Faisal "toh tunda ga Magistrate sai a karanto mun laifina na kare kaina kafin a yanke mun hukuncin da ya dace" Dariya sukai gabadaya, Faisal yace "wai Ihsan ce Magistrate din?" Cewa yayi "ah! itace mana tunda kaga an dauko mota an taho gidanta a fusace ai matsayin da take da shi kenan!" Ihsan tayi murmushi tace "to ai ni har yau banji komai ba zaman rarrashi da ban baki nake yi tukunna! Taki gaya mun abinda ya faru"

Mubarak ne ya gyara zama yace "watakila tasan bata da gaskiya ne shiyasa! Ihsan kiyi alkalanci na tsoron Allah da gaskiya! Tun daga Lagos na bar ayyukana na taho kawo mata surprise visit amma kawai sai zuwa nayi na ganta da wani kodadden mutum kamar albino sun tsurawa juna ido kamar masu acting movien soyayya. Da yake shakiyancin shi ya kai ya kawo wai har miko mun hannu yayi muyi musabiha, sa'ar sa daya gidan surukai muke tsaye da sai na zubar masa da hakora. Bai isheta ba wai yace zai tafi zungui zungui ta kama hanya ta raka shi ga Gaula a tsaye wanda zuwan shi ya kawo cikas....
Amma ita duk wadannan bata karanta su a laifi sai kawai don nace mata zamu je hado lefenta da Surayya ta birkice ta soma masifa kamar idonta da bakinta zasu fado har da cewa wai a ina na taba ganin kishiya ta hado lefe....."

Gabadaya falon dariya suka kwashe da ita wadda ta kular dani na mike tsam zan bar musu wajen Ihsan tai maza ta fuzgo hannuna na dawo na zauna. Wata muguwar harara na watsa mata nace "tunda na zama mahaukacciya meye ruwanku da zamana anan?"
Faisal ne yace "haba Amarsu ai ba'a haka! Hakuri zaki yi a yankewa mai laifi hukuncin sa don gaskiya bai kyauta ba! Ihsan kinji fa ruwan da ya ballo kuma yake zaune hankalinsa kwance" zama ta gyara tace "toh gaskiya wannan laifi ya kai makura wajen girma saboda haka Ango sai ya bada hakuri"

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now