HAUSA ARAB💫💫💫BY CUTYFANTASIA PAGE ELEVEN

990 73 2
                                    

Yau litinin ce tunda nayi sallar asuba nayi karatuna ban koma ba. Yau Imamu zai dawo daga doguwar tafiyar da yayi ta wata daya wadda ko samun lokacin hira mai tsayi bamayi domin ayyuka suka tarar masa masu yawa. A dalilin wani sabon kamfani da suke son budewa na cement a garin Kano.  Inaso na mishi tarba ta musamman domin nasan kila yau a gidanmu ma zaiyi dinner. Kitchen na shiga na samu Baba Rabi tana ta kicimullin aiki. Na karasa ciki ina cewa "Baba Rabi wannan aikin fa da sassafiyar nan wane zaici duka wadannan abubuwan?" Murmushi tayi taci gaba da zuba kullin waina fara sol akan tandar waina ta zamani. "bakisan Daddy zaizo ba?" Wara ido nayi cikin mamaki nace "yau zai dawo? Ya akai Dada bata gayamun ba? Kice yau gidan nan zai dau harami kenan!  Tayi dariya tace "ba karami ba kuwa amma inaga ba dadewa zasuyi ba. Da abokansa zasuzo gaida Dada su karya. Su tafi.
Wainar guda daya na dauka na gutsira wani dadi malam ba'a magana. Akan cooker daga can gefe ga farfesun kan rago yana ta zabalbala. Daya tukunyar kuma miyar taushe ce da ta wadatu da naman rago da ganyen alayyahu.
Na bude manyan food warmers din da ke kan table duka kayan abincin gargajiya ne irinsu funkaso sinasir da tuwon nikakkiyar shinkafa.
Daga can kuma an feraye doya ne dankali ga kayan miya anyi grating birjik. Na jinjina kai ina cewa "yanzu Baba Rabi tun yaushe kika tashi don Allah kikai wadannan abubuwan? Kamar wata inji?" Dariya tayi sosai sannan tace "tun jiya da dare na kwaba kayan fulawar karfe hudu na futo na fara suya.  Na girgiza kai ina jinjina aiki da iya sarrafa abinci da wannan baiwar Allah. Ban taba ganin macen da ta iya lafiyayyen abinci kala kala irin Baba Rabi ba. Gashi bata gajiya kamar inji ko ance za'a kawo mai aiki a hadasu ta rage mata wani hidimar bata yarda sai tace iya tafiso tayi aikinta ita kadai. Kullum ba zaki ganta a zaune ba kwata kwata batasan ta gaji ba. Wannan ya sanya Dada take masifar ji da ita. Bama Dada kadai ba har yayan Dadan da jikokinta don kuwa in kana gidan toh cikinka baya maraici.
Daga kitchen dakin Dada na wuce na same ta kamar kowacce safiya tana nan sallaya tana karance karancen littattafan addu'o'inta. Ta saka tafkeken gilashin karatunta mai kara mata kwarjini. Cikin ladabi na gayar da ita ta amsa tare da tambaya ta yanda na kwana. "Dada ashe yau Daddy zai dawo?" Cikin murmushi tace "nima ban dauka yau bane sai jiya da la'asar ya gayamun wai anan ma zasu karya da abokansa inaga zuwa karfe takwas zasu sauka" murmushi nayi nace "Allah ya kawo su lafiya" tace "ameen ba zaki makaranta bane?" Nace "ina da test ma Dada amma fa sai na bari su Daddy sunzo zan tafi ko da zanyi missing test din kuwa" dariya na bata sosai domin ta gano abinda yasa zan tsaya. "Kudi" don in dai abokan Daddy suka zo gidan nan wata Don nake komawa in don ta naga Daddy ne ai shi yana nan gobe ma zai shigo gidan.
Nima dariyar nayi nace "Dada da gaskiyata fa bikin su Ya Sadik saura sati uku duk inda mutum yasan zai samu kudi ai ba zai wasa ba" ta girgiza kai kawai tana murmushi sannan tace "dan Allah ki futa sitroom din baban naki kiga su Ya'u sun kammala gyarawa?" Mikewa nayi ina cewa "yanzu kuwa Dada akwai sabon turaren wuta na ma shi zan dauko na saka musu" cewa tayi "Allah ya sauwake wa son kudinki Zara" futa nayi ina dariya.... banda abun Dada wanene bayason kudi a wannan marrar? Babu.
Kafin karfe takwas din tuni mun kammala komai gidan ya dau kamshin abinci da na turare kamar wanda za'a kawo amarya. Dada naji da Daddy ajin karshe duk abinda ya shafe shi bata wasa dashi. Duk wanda yake kaunar Daddy ya gama da zuciyarta!
Wanka nayi na futo nayi shafa na gyara fuskata da nude make up sannan na shirya cikin dandakekiyar doguwar riga kirar Oman kalar brown, balloon sleeves akai mata da wani yadi mai jikin damisa. Na nade fuskata da gyalen rigar. Da sassanyar farar humra nayi amfani tare da turaren Beyonce heat. Na hada tarkacen kayan karatuna da purse a babbar jaka na saka takalmana na futo. Kitchen na wuce nayi mana take away din abincin ni da Ihsan na kai mota na dawo. Ina kallon agogo basu suka shigo ba sai karfe goma.lokacin na kagu sosai domin ina da test ne by 11.
Ni da Baba Rabi muka shiga hidima da Daddy da abokansa guda hudu. Yayi matukar farinciki da abincin musamman yanda su Alaji Bala suke santi kowanne yana kwararo abarkacin bakinsa game da taste din abincin bani na samu kaina ba sai 12 na dau hanyar makaranta amma jakata a cike taf don haka ko a jikina banji rashin dadin nayi missing test dina guda daya ba.
Ina hanya wayata ta isheni da ringing nayi parking na dauka. "Aisha ina driving ne fa.. ke in kika fara kiran mutum bakya kakkautawa sai ya dauka" dariya tayi tace "ke malama ya isa haka tambayarki zanyi yaushe zakuzo da Ihsan din? Ohhps sai a lokacin  na tuna nayi mata alkawari zan kai mata Ihsan gidansu yau idan mun tashi daga lectures. Cikin low tone nace mata "ayyah I'm sorry my dear yau Imam zai dawo na manta ne ban gaya miki ba but insha Allah gobe zamu zo" da ihu  tace "kice yau prince charming yana hanya ba'a ta kowa sau tashi." Nayi dariya nace "toh ya kika gani? He worth the whole of today don ma ina da test ne da bazanje school din ba." Ta sake yin shewa tace " lallai su o'o anyi zurfi ba'ajin kira" dariya nayi nace "ai zaki shigo muyi masa cin cin din nan kinsan kullum sai yayi zancensa wai bai taba cin mai dadinsa ba." Cewa tayi "oh bestie I'm so sorry wlh ina da ayyuka dayawa yau i cant make it" sosai mamaki ya kamani don ban taba rokan Aisha wani abu ta gaza yimun ba musamman irin wannan. Gashi na uku kenan ina kiranta idan Imam zaizo ta tayani wani abu tana bani excuse. Zuwa yanzu na soma tunanin lallai akwai wani abu. Ba tare da na nuna mata komai ba mukai sallama na karasa makaranta raina cike da tunani kala kala.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now