Cikin tsananin bacin rai ya kalli kayansa da suka yi kaca kaca da cock. Sannan ya mike tsaye yana huci. Wani irin mugum kallo ya jefamun wanda ya sanyani soma hawaye domin irin wannan kallon da dabba ya dace ba da mutum ba. "I will break you into pieces if you dare let those tears out! Stupid girl!!
Yanda yayi maganar cikin temper ya sanyani shanye kukan da sauri cikin tsoro domin zai iya kakkaryanin dagaske. Wayarsa ya ciro daga cikin jakarsa ya soma danna wasu lambobi ya kara a kunne! "Hey.. Where are you?" Ya dan jima sannan yace "ok.ina nan zuwa" daga nan bai kalle ni yai fatali da abincin ya wuce yayi tafiyarsa. Bat!! Ya bacewa ganina.
Awana daya da rabi ina zaune ina jiransa amma babu alamunsa har aka kira sallar isha'i. Nayo alwala nabi jam'in sallar. Lokacin ne hankalina ya tashi na soma kuka don azabar tsoro! Ta ina zan tafi gida? Wa na sani anan? Ina zanje? Ganin kukan ba zai mun ba na goge hawayen na mike na soma safa da marwa tsakanin hotels din da ke jere opposite din masallacin. Nafi mintin arba'in ina wannan zarya ina kuka.
Ji nayi an fizgo ni da karfi na juya sai nayi ido hudu da shi. Ya sauya zuwa lafiyayyar blue jallabiyya sai kamshin turaren shi yake. Wasu matsiyatan rankwashi ya zubamun wanda suka sani kusan sakin fitsari a tsaye. "You're very stupid! Useless girl" abinda ya fada kenan tare da janyo hannuna da karfi yatsuna suka lankwashe suka ce wani "qas!qas!!qas!! Wata irin azaba ta shigeni na fashe da kuka. Na janye hannun da sauri. A zafafe ya kalleni cikin tsananin fushi ya sake damkar yatsun da ya jiwa ciwo muka soma tafiya ina kuka har ya samu mota ya cillani gidan baya. Shikuma ya bude gaba ya shiga. Wani irin kuka na saki har balaraben ya juyo ya kalleni. Cikin tsawa Ya Mahmud yace
" if you dont close this toilet i will disorganize you face" dif! Na shanye kukan naci gaba da yin na zuci hannuna kuwa wata irin azaba yake yi kamar zai cire. "Qilama ya karyani" na fada a raina. A wahalce muka iso gida. Na balle murfin motar na futa. Allah yasa kofar gidan ba'a hadeta ta ta kulle ba na wuce a guje na shige cikin gidan. Babu kowa a parlour don haka na wuce dakinmu na soma zarya ina rike da hannun ina kuka don tsananin radadin da nakeji.
A haka ya Nuratu ta shigo ta sameni.
Da sauri ta
Kamani tana cewa "ah Zara yaushe kuka dawo? Me ya sameki? Menene? Hannuna kawai na dago na nuna mata wanda ya kumbura sosai yayi wani lage lage yana lilo sai kyalli yake! Zaro ido tayi tace "how comes? Da me kikaji ciwo haka?" Bansan yanda akai na tsinci kaina da cewa faduwa nayi ba. "And where is Ya Mahmud?" Ta fada cikin fushi! A galabaice nace "please Ya Nuratu stop this questions and help me"
Tashi tayi ta futa suka dawo tare da Dada. Ta ballo pain killer guda biyu ta bani da ruwa nasha. Sai sannu sukemun. Dada ce ta sanya Ya Nuratu ta kira Auwal muka tafi asibiti. Hoto aka soma yimun sannan aka gyara karyayyun yatsun aka nannade mun su da tsumman bature akaimun allurai suka bani magunguna.
Bayan mun dawo muka samu Daddy a kofar gidan da wani mutum.
Da mamaki yace "ke meye wannan? Ma ya sameki Zara?" Cewa nayi 'faduwa nayi' yace mu shiga ciki yana zuwa.
Lokacin da ya shigo ina gaban Dada tana kallon yanda suka like hannun yazo ya zauna yana cewa "garin yaya haka ta faru? Ina Mahmud din ya barki da wannan hannun kuka taho?" Cewa nayi "Daddy bamusan zai kumbura ba sai bayan na dawo gida nagane naji ciwo ne"
Da dabara nayi wanka Ya Nuratu ta hadamun tea nasha ta bani magani sannan na kwanta. Ban dade da yin baccin ba hannun ya matsa mun da ciwo na mike ina sintiri. Kukana ya tada Ya Nuraru ta mike da sauri tana cewa "Zara hannun ne?" Sannu! Haka muka kwana ina shan azaba sai wajen asuba na samu nayi bacci. Bayan kwanaki buyi na soma samun sauki. Lokacin azzalumin jikan Dada ya tafi Madeena don haka naji dadi sosai. Domin yanzu na tsane shi tsana me tsanani har bana kaunar ganinshi.
Dada ta koma asibiti an karbi result din hoton guiwar sunce aiki zasuyi mata a qoqon guiwar bayan kwanaki uku. Ranar da za'ayi aikin duka a sibitin muka wuni sai da muka ga ta farfado munyi magana da ita sannan muka taho gida don basa bukatar me jinya.
Sati biyu bayan wannan lokacin aka soma azumin Ramadan. Tuni an kwance mun hannun saidai ba komai nake iya yi dashi ba sunce sai a hankali sun koyamun yanda zan dinga exercising dinshi lokaci lokaci.Yau mun kai azumi na goma sha biyar. Babu kowa a gidan daga ni sai Amal sai Hajiya mai abinci. Wannan shekarar kam visa tayi matukar wahala don haka babu kowa a gidan. Dada tana da appointment da likitanta. DR.Mansur mijin Ya Nuratu ne yazo da kansa suka tafi asibitin tare. Daddy ya tafi Riyadh wajen babban amininsa ambassador Ahmad kibiya. Auwal kuma Daddy ya aike shi Makkah ya kamawa abokinsa Dr.Ilyas masauki yana tahowa gobe. Da yake Daddyn daga baya tafiya yayi sai shekaranjiya ya dawo.
Shara nayi mai kyau na goge ko'ina sannan na kunna burner na zuba sandal woods bayan na karo karfin Ac. ko'ina ya dau kamshi mai dadi. Daki na koma na shiga toilet nayi wanka na shirya cikin three quarter baki da jar tea sanin babu wanda zai shigo gidan.
Kitchen na sauko na soma taya Hajiya aikin abincin muna yi muna hira tana bani labarin yan'uwanta da ke jihar katsina a kano. Yau shekararta goma sha hudu kenan bata taba zuwa gida ba sai dai tayi musu aike. Duk mamakinta ya cikani. Na dube ta nace "danAllah Hajiya ki taimaki yaranki ki koma gida kada da su manta ki" dariya tayi kawai tace "Zara baki da dama. Ya za'ai su manta ni? Ai muna waya koda yaushe kuma idan na samu ina turawa wani kudi yazo da Hajj sai na gansu." Kai na girgiza ina tunanin wannan karfin hali nata. Salad din da na kammala hadawa nasa a fridge sannan nasa parker na kwashe sharar da na tattara na futo corridor domin na zuba a dustbin.
Baya nayi da sauri!!..Kadan ya rage na fadi saboda tsoratar da nayi a sakamakon ganin mutum a tsaye.
Sai da na sake kallonsa nagane Ya Mahmud ne cikin shigar da yafi kauna tun saukarshi garin. Wato jallabiyya. Wannan blue black ce mai shaking sai kyalli take. Hannunsa rike da kwaton kwalin inibi.
Habawa! Kifar da sharar hannuna nayi na bi ta gefensa na haye sama a guje ina haki domin zuwa yanzu tsoronsa nake ji bayan tsanar da nayi masa. I hate him with passion!! Bashi da kirki ko kadan kuma bashi da tausayi. Haka kawai ya kama ya balla mun yatsuna saboda an hadashi tafiya dani ba'ason ransa ba. He is soo selfish and arrogant! Kyawun da Allah ya bashi da dukiya su suke zugashi yake butulcewa rahamar ubangiji. Ya manta cewa wataran rami za'a haka a saka shi a ciki tsutsotsi su cinye. A duk lokacin da Daddy yake nunamun extra care sai na dinga tunanin inda shi Mahmud ya samo nashi halin? Meyasa bashi da kirki ko na cikin karamun cokali? A duniya ban taba samu mutumin da ya tsaneni lokaci daya ya gwadamun zalinci kamar Mahmud ba idan aka cire Mummy! Toh ko itace mamanshi? Ahh no!!! It cant be!! Mummy ba zata zama mahaifiyarsa ba. Ya fita kirki! Kuma ko babu komai ai shi yana son Dada kuma yana da addini da girmama nagaba da shi. Kuma baya shiga abinda babu ruwansa! Ba ita ce mamanshi ba! Duk tsanar da nayi masa bana so hadashi da wannan mata ba.
Bayan kwanaki biyu muka tafi Madeena lokacin da muka isa karfe biyar na yamma Kai tsaye "daruq taqwa" muka wuce domin tuni an mana booking. Wanka mukayi muka shirya domin mu samu shan ruwa a masallaci. Ni ke tura Dada akan wheel chair dinta Ya Nuratu na rike da hannun Amal.
Kwanakinmu takwas a madeenatul Munauwara. Gari mafi soyuwa acikin zuciyata. Babu abin da nafiso kamar naganni cikin Rawdah nakanyi ta zama ina kallon "green throne" ina salati ga Shugaban Annabawa saw. Ina addu'a sosai musamman ga mahaifiyata da mahaifina kafin nayiwa kaina.
Sallar farilla bata taba wucemu a masallaci ba hakana Asham da tuhajjud damu akeyi kullum . Wani lokacin kuma mukan shirya mu shiga manyan malls muyi siyayya. Hakana muka kammala zaman garin Madeena muka taho makkah cikin kewa da shaukin garin.
Ashirin da biyar ga wata muka taho Makkah ambasada ne yayi mana masauki a Intercontinental wato daral tauhid!! Masaukin da sai kasaitattun mutane kadai ke zama aciki. daren sab'a wa ishirun. Daren ashirin da bakwai ga watan Ramadan! Daren da musulmi daga kowacce nahiya suke tururuwa su taho saboda shi. Sheikh sudaith ya dinga kwararo addu'o'i muna amsawa da ameen. Masu kuka nayi masu hawaye nayi kowa ya mika kansa ga Ubangiji.Anyi azumi an kammala daren asabar aka buga bindigar ganin wata. Nan da nan gari ya kacame da shirin sallah kowa yana murna. Washegari da safe akayi sallar idin sallah karama. Su Dada tun karfe uku suka tafi masallaci da YA Nuratu sai ni da Amal kadai a gidan.
Tun jiya Daddy ya sanar damu cewa zasu shigo da manyan aminansa su gayar da Dada. Don haka muka tafi da Ya Nuratu Bin dawud muka siyo royal coolers na alfarma da flasks din ruwan zafi da plates da sauran tarkacen abubuwan bukata. Daga jeddah Hajiya tayo tuwon sallah Auwal ya kawo shi da sassafe. Mu kuma mukayi su P.soup din naman rago aka soya kaji suyar gida aka hada kunun gyada da sauran dai kayan abincin gargajiya wadanda zasuyi marmarinsa.
Ina cikin aikin naji kararrawa. Na wanke hannuna naje na bude kofar su Dada ne suka dawo nayi musu sannu da zuwa. Cikin sauri Ya Nuratu ta wuce kitchen tana cewa "Zara muyi sauri mu kammala Daddy yace anjima kadan zasu shigo.......'" mamaki ne ya kamata ganin na kammala komai sai suyar kajin kawai "wow!!weldone my girl!" Ta fada tana murmushi. Sannan ta dubeni tace "oya je kiyi wanka kiyiwa Amal nikuma na kammala ragowar abinda ba'ayi ba. Nace "toh" na wuce daki.
YOU ARE READING
HAUSA ARAB PART 1
General FictionAlqalamin qaddara yana aiki akan kowa ba tare da zabin wance ko wane ba. Kowanne bawa da irin na shi salon rubutun, na wani ba irin na wani bane.