HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE FIFTY-FOUR

1.2K 68 22
                                    

A nutse yake shigowa cikin falon kai tsaye ya wuce kujerar da Daddy yake zaune ya rungume shi suka gaisa tare da yi masa ya jiki  sannan ya juya ga Eng. Garba Galadanci ya gaishe shi fuska a daure. Daga nan ya nemi kujera ya kame yana muzurai wanda zai sa kayi shakkar kawo masa wargi. Gane hakan da Daddy yayi ya sanya ya murmusa sannan yayi gyaran murya yace "Ahm wato Mahmud Baban Safna ne yazo da wata magana wadda ni bansan yanda aka yi hakan ya faru ba don ba kai mun wata magana da ta dangance ta ba." A kasaitance Mahmud yace "wacce magana kenan?" Yana kallon Engineer.

Sai da gaban Eng ya fadi saboda ganin yanda Mahmud ke cika yana batsewa. Cikin sanyi ya soma magana

"Mahmud sati hudu da suka wuce zuwa biyar mukai magana da kai a waya kake tambayata Safna nace maka tana Scotland wajen kawarta. Ka tambayeni me taje yi na gaya maka sannan ka kashe wayar. Sati daya dai dai bayan wannan lokacin Safna ta shigo da yamma cikin wani irin yanayi tana ta kuka kamar ranta zai futa, duk iya tambayar da zamu yi mata munyi taki bamu amsar dalilin da ya sanya ta kuka. Kwanaki uku tana cikin wannan halin kafin tace wai Mahmud ne yace babu shi babu ita. Maganar ta daure mun kai matuka, na tambaye ta mai tayi maka? Tace wai kawai saboda taje gidan kawarta. A lokacin ne nayi ta neman wayarka ban same ka ba, na kira Alaji yace mun baka da lafiya ne shiyasa amma idan ya nutsu zamu yi magana.
Tunda Safna taji ance baka da lafiya ta sake daga mana hankali... na rasa yanda zanyi da ita. Cikin haka tafiya ta taso mun zuwa Florida sai muka tafi gabadaya domin dai ta samu ta warware ta samu nutsuwa. Daga nan muka wuce Nigeria sai  Last week muka dawo, amma tace kullum sai ta kira wayarka baka dauka, nima bana samun layin Alaji idan na kira shi sai dakyar shekaranjiya na same shi na yi masa bayanin abinda yake faruwa yace idan yazo zamu yi magana."

Zama Mahmud ya gyara tare da bada hankali ga Eng da Daddy. Sannan ya soma magana a nutse yana kallon Eng.

"Tun farkon haduwar mu ba Safna ce ta hada mu ba don haka ba zata zamo dalilin rabuwarmu ba. Kai da kanka ka gayyaceni dinner gidanka a matsayin likitan da yayi nasara akan matsalar yarka. Ban cika amsa irin wadannan gayyatar ba saboda gudun mutane amma karamcin ka da girmanka ya sanya na kasa yin haka. A wannan zuwan da nayi ka bijiro mun da maganar da ta hargitsa mun lissafi da kwakwalwa. Wato maganar yarka Safna, bayan ka labarta mun rayuwar ta da maraicin da ta taso a ciki wanda yayi matukar girgiza ni. Ba soyayya bace ta kulla mu'amala tsakanina da Safna, tausayi ne da ganin kima da darajar ka.
A hankali muka saba muka yi wata irin shakuwa da Safna, sannan ne kuma nagano abubuwa da yawa a game da ita wadanda banyi hasashe ba.

Na farko dai I am sorry to say
Safna bata da tarbiyya, idan nace tarbiyya ina nufin rashin kamun kai da sanin addininta da yanda zata tafiyar da rayuwarta a matsayinta na musulma.
Na biyu Safna sangartacciyar yarinya ce da bata san menene rayuwa ba. Ta taso ne akan duk abinda take so dole zata same shi ta kowanne hali, bata san ta nemi abu ta rasa ta hakura ba.
Na uku duka mutane da kawayen da Safna take mu'amala dasu shaidanun turawa ne wadanda ko cikin turawan basu da kirki.

Wadannan abubuwan guda uku kowanne zai iya zama dalilin da zan raba da hanya da Safna amman banyi ba. Saboda na dauki damarar gyara Safna na shiryar da ita da yardar Allah na kuma daidaita mata rayuwar ta iya bakin iyawa ta. Nasan hakan ba zai mun wahala ba saboda soyayyar da take mun na tabbatar babu irin biyayyar da ba zata tayi mun ba.
A hankali na soma rabata da rayuwar club, da kawayen banza da kuma banzar shigar da take yi kullum. Daya daga cikin abinda ya bani wahala akan Safna Joyful ce, wannan kawarta ta da ke Scotland. Joyful shaidaniyar gaske ce irin wadda ko turawa tsoron sharrin ta da kaidin ta suke yi. Gashi sun matukar shakuwa da juna amma haka na dinga bin dabaru kala kala har na samu nayi musu iyaka da ita. Ban taba tunanin yaudarar Safna ba, duk da ba wai son ta nake ba amma akwai shakuwa da fahimta mai karfi tsakanina da ita wadda nake ganin zan iya zaman aure da ita.

Watanni hudu haka da suka gabata na fara ganin sauye sauye a wajen Safna. Ta rage yi mun waya, ta rage daukar tawa wayar sannan duk sanda na kira ta her voice is weak kamar mai bacci ko tunani ko mara lafiya. Nayi matukar kokarin naga ta gaya mun menene matsalarta amma sai kullum sai tace babu komai.
Kullum abu karuwa yake yi a dalilin zamana Nigeria bana tare da ita balle na gano abinda yake faruwa. Ranar da na kira ka abinda naso yi maka bayani kenan domin ka tambaye ta menene matsalarta, sai ka tabbatar mun da cewa tana tare da Joyful a Scotland babu wani kwakwkwaran dalili. Shiyasa ban ma tsaya cigaba da jin me zaka ce mun ba na kashe wayar.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now