Sai da gaban Daddy ya fadi kafin ya tattara duka dauriyar da yake da ita ya hado kan hankalinsa da tunaninsa ya tara su waje daya. Sannan ya soma magana cikin taushin murya da ladabi.
"Dada cewa nayi na rubuta a rubuce da sa hannuna da na lawyer na da kuma cikakkun shaidu cewa na mallakawa Mahmud kashi sittin bisa dari na abinda na mallaka a dukiya ta. Kuma ko da na mutu ban idda wannan nufi ba toh na rubuta wasiyya akan haka sai an soma cire wannan kason kafin a raba gadon abinda na bari!"
Wani irin kallon (me kasha?) Dada take wa Daddy tunda ya fara magana har ya kai aya, shi kuwa baisan hakan ba don kansa a kasa yake maganar. Cikin kaushin murya tace "saboda kaine shugaban mara sa adalci na duniya ko kuma shugaban mahaukata? Na dauka jiya wani abun ne ya shiga kanka ko kuma wasu magautan ne suka kawo wa kwakwalwarka hari saitin ta ya hargitse, shine na sallameka nace ka dawo yau da niyyar zan kwana inai maka addu'a toh ashe abun naka bai shafi gushewar hankali ko tabin kwakwalwa ba sai tsagwaran rashin adalci da tunani da kuma rainin hankali! Ni za ka fuskanta da wannan magana? Kanka daya?"
Sake nutsuwa Daddy yayi duk da zafin maganganun Dada a gare shi bai bari ya nuna wata alama akan fuskarsa ba. Sai ma kara ladabta harshen sa da yayi ya dunkufar da kansa ya soma bayani a karo na biyu
"Kuyi hakuri Dada! Tsakanina da ku har abada babu raini ko wasa. Kuma wallahi ban sauya ko kadan daga yanda kika sanni ba, sannan banyi haka don na fifita Mahmud cikin yara ba. Akwai al'amura masu yawa Dada wanda nake rokon ki mun afuwa ba sai na gaya miki ba ki amince da bukata ta.
na kai shekaru goma ina son yin wannan yunkurin amma tsoron abubuwan da zasu biyo bayan haka ya sanya na ke fasawa. Lokaci tafiya yake kuma babu wanda yasan gawar fari shi yasa nake tsoron kada lokacina yazo ban idda wannan nufin ba. Kuyi hakuri Dada ki fahimce ni, wallahi banzo da rainin hankali ko son zuciya ba! wannan wani abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwata Dada ki yi mun wannan alfarmar"Wani irin shiru ne ya biyo baya kamar babu halitta a wajen! Dada ta tafi wani dogon nazari mai zurfin gaske, ta yarda ta tabbatar da amana da adalci irin na danta, ta yarda da kyawawan dabi'u da tausayi da jin kansa kuma tana alfahari da samun da mai irin zuciyarsa don haka lallai wannan batu da yazo da shi akwai wani babban al'amari a cikinsa mai girma. Toh menene shi? Wanne irin sirri ne wannan da ya boye mata bayan bai taba boye mata wani abu na rayuwarsa ba, cigabansa da gazarwarsa, dadinsa da kuncinsa, bai taba yin wani abu bai shawarce ta ba. Musamman wani abu akan Mahmud wanda tunda ya fuskanci son da take masa ya tattara ya bar mata duk wata ragamar rayuwarsa da jagorancin sa. Meye Wanda ya boye mata tsakaninsa da Mahmud? Wadannan tambayoyin Dada take wa kanta, sai dai kaf ta gama tunani bata da amsa. Hakan ya sake dugunzuma ranta hankalinta ya tashi. A karshe dai kawai cewa Daddy tayi
"Ka bani wani lokaci zanyi tunani akai, zanyi addu'a. Ni da kaina zan neme ka idan na kammala! Sai dai ina so kaima ka kara addu'a akan wadda kake yi kuma kayi tunani mai zurfi kafin lokacin"
Cikin ladabi Daddy yace "toh Dada insha Allahu! Allah ya kaimu! Nagode Allah ya saka da alkhairi Allah ya kara girma"
A sanyaye tace "Ameen" sannan ya dago daga sunkuyen da yake yace "Dada lokacin zuwa Jedda yayi fa, har ma munyi magana da likitan"
Ajiyar zuciya tayi a ranta tace "koma banje jedda don asibiti ba, ai naje Makkah da Madina nayi wa wannan lamarin da kazo mun da shi addu'a" don haka ga mamakin Daddy wannan karon batai musu ba tace "to ai sai a shirya lokacin tafiyar" cikin jindadi yace "ai tafiyar na hannunku, duk saboda kuka shirya jirge yana jiranku"
A nutse tace "to mu bari su Zainab sun dawo tukunna sai a san me za'ayi! Jibi ne dawowar tasu ko?" Yace "eh amma sai gata zasu iso nan Abuja, sai sunyi transit a Dubai kafin su iso" tace "Allah ya kawo su lafiya" daga nan kuma suka shiga hirarraki irin wanda suka saba yi idan sun samu lokacin zama tare. Sai gab da azahar Daddy yayi mata sallama ya koma gida, a yammacin ya wuce America zai halarci wani taro da za'ai akan yanda za'a habbaka tattalin arziki da bunkasa kasuwanci.
------------------------------------------------------------
ESTÁS LEYENDO
HAUSA ARAB PART 1
Ficción GeneralAlqalamin qaddara yana aiki akan kowa ba tare da zabin wance ko wane ba. Kowanne bawa da irin na shi salon rubutun, na wani ba irin na wani bane.