HAUSA ARAB💫💫💫BY CUTYFANTASIA PAGE TWENTY-SEVEN

963 58 5
                                    

"Ashsha! Ashasha!! Ashsha!!! Zainab meyasa zaki tashe ta bacci da ruwan sanyi?" cikin daurewar fuska Mami tace "Dada sau hudu ina zuwa tashinta akan ta shirya idan na futa sai ta koma baccin bayan tasan ana magrib akace za'a tafi" cikin nutsuwa Dada tace "Duk da haka Zainab kar ki kara tashinta a bacci da ruwa ko ba na sanyi ba! Na lura akan Zahra kawai hakurinki yake gazawa, idan da wancan tuzurun dan naki ne kinsan yanda zakiyi ki kareshi" bansan dalilin da ya sanya naji banji dadin kiran Ya Mahmud tuzuru da Dada tayi ba! Mami ce tace "Dada kiyi hakuri ba'a sake ba insha Allah" tace "yauwa! ke Zara ina haraminki kika saka wannan bakin kayan?" a sanyaye nace "Dada suna can kasan jakata ne kar na tsaya bincikawa na bata lokaci" Dada tace "Allah ya kyauta! jeki ki zuba abinci kici kafin motar ta karaso!" a ladabce nace "Dada bari nayi sallah idan motar batazo ba har na idar sai naci abincin" ta girgiza kai cikin gamsuwa! Nikuma na tashi na shiga daki!
sallar la'asar da magriba nayi cikin rashin jin dadin lattinsu da nayi da kuma ruwan da Mami ta watsamun! ina idarwa na sake nade kaina da mayafin abayar na dau yar jakata na zuba tarkacen da zan bukata da wayata na rataya na futo! har lokacin motar ake jira don haka na dira kasa na shiga kitchen na hada tea nasha raina duk ba dadi! ina futowa Ihsan da Faisal na shigowa! sai lokacin na tuna ma da ita!bayan mun gaisa da faisal nace "ke kuma kina ina?" cewa tayi "wallahi pharmacy muka je! babu irin tashin da banyi miki ba ko motsawa bakiyi ba kamar gawa" nace "ko? ai a karshe ruwan sanyi ya tasheni" cikin gumtse dariya tace "ba dai Mami ce ta zuba miki ruwa ba" na maka mata harara tare da fadin "Malama wuce mu tafi kafin na huce haushina akanki!"

karfe takwas lafiyayyar luxury bus ta iso ta kwashemu zuwa garin Makkah! kowannen mu ya nutsu da duk nutsuwar da yake da ita! Ya Mahmud na karanto "Labbaikallahumma labbaik,Labbaika la sharika laka labbaik, innal hamda, wan ni'iamata, laka wal mulk, la shari kalak" mu kuma muna bi a hankali! don haka babu batun surutu ko hayaniya!
hakika addinin musulunci addini ne na rahma da tarin baiwa da ni'ima da kwanciyar hankali! addini mai koyar da ladabtacciyar tarbiyya da jinkai da tausayi da karamci da hakuri da kaunar juna da hakuri da juna!
Tafiyar awa daya tak ta iso damu garin Makkah! dukanmu muka futo muka fuskanci masjidil haram da niyyar umra cikin kaskantar da kai ga Sarki mabuwayi wanda bashi da abun tarayya cikin mulkinsa! sai da muka tsaya marasa alwala suka jaddada tasu sannan muka dunguma cikin masallacin! Muna shiga Ya Mahmud ya wuce da Dada cikin wheelchair dinta don yi mata nata umrar! mu kuma muka dauki tamu hanyar!

karfe shabiyu duk mun kammala muna zaune a harabar masallaci muna hutawa! kasancewar gabatowar karshen shekara hutu ya samu garin ya zama a cike sosai don haka ba karamar wahala muka sha ba! sai da muka kammala hutawa muka shiga restaurant acikin Zam Zam tower muka ci abinci! daga nan muka dawo masallaci,
Bamu bar garin Makkah ba sai da mukayi sallar asubahi sannan muka dawo Jeddah! muna isa kowa ya nemi dakinshi ya sa hakarkarinshi a makwanci domin gajiyar da mukayi!
Nikam ina baccin ina farkawa domin ina fara baccin sai naji kamar Mami zata zubamun ruwan sanyin nan! kai wlh na tsorata da ruwan nan ba kadan ba!ganin bazan iya baccin mai tsaho in peace ba ya sanya na tashi nayo wanka nayi sallar azahar sannan na shirya!
Da na futo parlour shiru babu kowa sai na sauka kasa zuwa kitchen! Mami na hango tsaye tana hidimar girki, Ya Mahmud na gefe gaban tebur yana firar dankali! suna magana kasa kasa da alama wani abun suke tattaunawa!
da sallama na shiga dukansu suka amsa lokaci daya. da alamun tambaya Mami take kallona sannan tace "ke kuma meye ya taso dake yanzun?" a sanyaye na matsa gabanta nace "Mami na kasa baccin ne, ina rufe ido sai naji kamar zaki zo ki watsamun ruwan sanyin nan! nayi nayi baccin baizo ba sai na hakura" cikin tausayawa da nadama ta dafani tace "ayyah! I'm so sorry my dear!raina ne ya baci ganin sau hudu ina zuwa tashinki idan nadawo na tarar kina nan kwancen bayan an gaya miki zamu je umra jiyan bansan lokacin da na bude fridge na dauko ruwan ba " ajiyar zuciya nayi na kalleta nace

"Mami ba sai kin bani hakuri ba na fahimceki !Nima don mun kwana muna hira da Ihsan ne bansamu bacci ba shiyasa da na kwanta na kasa tashi! i'm sorry too" rungumeni tayi tana bubbuga bayana a hankali kafin ta sakeni!

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now