HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE FIFTY

727 57 4
                                    

Da daddare muka sauka a Abuja cikin sanyin jiki da bacin rai. Wata irin tafiya mukai mara dadi ko kadan. Babu wanda ya siya ko tsinke balle wata tsaraba sai tarin bakin ciki kawai muka lodo. Acan muka baro Ya Nuratu duk da hutun ta bai kare ba gani tayi dawowan nata bashi da amfani tasan cewa tsuran bacin rai ne zai biyo bayan wannan fushin na Dada. Don haka mukai sallama rai duk babu dadi ta tafi gidanta.

Ya Omar ne yazo daukar mu fuskarsa a matukar daure kamar jakadan lahira! Ko me akai masa Oho! Ita kanta Dadan na lura sai da taji shakkarsa don idan Ya Omar ya hade babu sauki.
Su Ya Sadik ya soma saukewa a gidansu sannan ya wuce da mu gidan Dada. Muna futa ya juya motar sa ya bar gate din cikin fushi. Sosai Dada ta tsurawa hayakin da ya tayar ido tana jinjina kai sannan ta wuce cikin gida ina biye da ita hannuna janye da trolley din ta.
Toilet na wuce na watsa ruwa na sauya kaya sannan na futo falon, Baba Rabi na samu a zaune ta rafka tagumi cikin damuwa na zauna gefenta a nutse ina cewa "Baba Rabi lafiya?" Hawayen da take rikewa ne suka gangaro Kan fuskarta tace "ina lafiya uwar dakina tana cikin fushi Zara? Ko amsa gaisuwata bata yi ba ta shiga daki! Na bita da abinci tace na kwashe bata ci kunu kawai ta tsiyaya a Kofi ta kafa kai kwankwade ba tare da ko jin zafin sa ba. Ba dole hankalina ya tashi ba Zara"
Ajiyar zuciya na sauke a hankali sannan nace "Baba Rabi zuwa yanzu ya kamata ki gane halin Dada! Idan tana cikin wannan fushin nata bata dauke kowa ba. Ni yanzu bana damuwa da abubuwan ta irin da. Daga fushin sai me? Sai fada da zage zage sai kuma me? Ba sai tayi ta gama ba! Sai ma ka kula ta!" Ina gama fadar haka na mike a zuciye na shige daki na bar Baba Rabi baki bude don tsananin mamakin maganganun da nayi. A ranta tana cewa "lallai duk yanda ake tsoronka da shakkar ka, masifa da fushi na sawa yau da gobe a soma raina ka"
Kwarai hakane! Don yanzu wallahi babu kashi hamsin cikin kaso darin tsoron da nake wa Dada! Kawai dai sai dai biyayya amma zancen tsoron fadanta yayi matukar raguwa a dalilin sabo. Sai dai idan nasan ni nayi laifi toh a nan fa hankalina yake tashi don Dada karshen karshen ce. Idan kuwa ba laifina bane, nagano takanta da yanda zanyi takatsantsan kada fushin ta ya shafeni. Wannan shi ake kira zaman yau da gobe, duk tsaurin mutum idan ka karanci halinsa ka gane lagonsa toh zaku zauna lafiya, sai abubuwan da ba'a rasa ba Wanda ba'a
Sauya mutum da dashi. Domin ance hali rubutun dutse. Sauya kayana nayi zuwa skirt and blouse din atamfa. Na yane kafada ta da wadataccen gyale na fesa turare na futo. Sai lokacin na tuna motata na bukatar service! Tsaki nayi na koma daki na kira Ihsan! Bayan mun gaisa nace ta turomun driver dinta zan futa tace toh!
Na dade a bakin kofar Dada ina sauraren wayar sirrin da take yi da Malaminta Mallam Safiyanu da ke Adamawa. Karshen maganar naji inda take cewa "tun daga yau za'a fara! Zansa a turo maka gabadaya in anjima. kullum idan an tashi daga karatun a yanka raguna biyu a bayar sadaka. Sannan a duba kauyen da suke da bukatar ruwa a haka borehole a siya musu inji duk da wannan niyyar. Ka hada da wani acikin almajiranka ayi masa passport su tafi tare da su Mai sunan Malam" tayi shiru tana sauraren shi sannan tace "babu komai Malam nima nagode! Allah ya saka da alkhairi. Allah ya bamu nassara!" Daganan sukai sallama ta ajiye wayar.
Wani mugun gumi na share na murda kofar dakin ina sallama. A ciki ta amsamun fuskar nan a matukar daure tana zaune kan sallaya da alkur'ani a gabanga. Tuni na shiga taitayina. A ladabce na durkusa gabanta nace "Dada zanje Office din Mami, tailolin suna nemana akan dinkunan da Mami ta basu" a cushe tace "kayan biki?" Na gyada kai a hankali duk da nasan karya nake yi hanyar futar kawai nake nema. Kuma sai nafi samun dama idan nace mata futar akan harkar biki ce. Ilai kuwa sai ta amince harda cewa wa zai kaini tunda mota ta an dade ba'a hau ba. Nace mata driver din Ihsan! Ta amsa cikin gamsuwa nayi mata sallama na futo ina hamdala da bata balbaleni da masifa ba.
Ko da yawancin fadan Dada akan gaskiya take yin shi, bata fada da fushi sai an tabo ta, inaji a jikina wannan karon kamar akwai wani babban al'amari a cikin kowanne irin abu ne ya taso mata. Don naga kan me uwa da wabi take bi kawai! Tunda gashi har da Daddy cikin maganar.
Driver na isowa na futa muka dau hanyar gidan Mami. Ina zuwa na tarar itama ta taho gidan Dadan don haka nace mu wuce gidan Ihsan na dawo da yamma. Ashe ashe da Mami taje gaida Dada bata ko kalle ta ba. Cewa ma tayi ta tattara tabar mata gidanta kuma kada ta sake zuwa sai ta neme ta. Kuka, roko, magiya Mami ta zube a gaban Dada tana yi amma ta juya mata baya ta shige dakinta tana jaddada mata cewa kar ta sake zuwa sai ta nemeta kuma duk abinda suka kulla Allah ya tona asirinsu don haka tana nan zuwa daukar mataki akansu daga ita har Daddyn. Sai a lokacin Mami ta soma gane inda zancen ya dosa. Gabanta yayi mugun faduwa domin tasan babu wata magana da ta hada su da Daddy sai ta Mahmud wadda take ganin kamar abu me sauki ne su fahimtar da Dada ta aminta dasu sai dai ga madaukakin mamakin su ta dauki maganar da wani irin zafi da rashin fahimtar da kowanne balli zai iya tashi akan ta. Haka Mami ta bar gidan tana kuka, sai bayan ta koma gidanta ta nemo lambar Daddy don taji ba'asin maganar.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now