HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE SEVENTEEN

821 62 1
                                    

Da hannu Mami ta kirani na dawo gabansu. cikin daure fuska tace "Zara bakiga Yayanki bane baki gaida shi ba? darajar Mami ba don halinsa ba na dube shi nace "ina wuni?" wani shegen kallo Mami ta jefe ni da shi cikin takaici tace "Zara?haka ake gaisuwa? a tsaye kike gaida shi?" mamaki ne ya lullube ni ganin yanda Mami ta fututtuke ta daure fuska kamar wanda na aikata sabo! raina yai bala'in baci amma sanin wacece takemun magana ya sanya na hadiye bakin cikina na risina sosai na gaishe shi! da murmushi ya amsa wanda na tabbatar na mugunta ne! raina ya sake baci. wayarshi ce ta soma ringing ya ciro ta daga aljihu yana cewa "excuse me Mami" nikam mamakin alakarsu nakeyi mai karfi haka!
bangama tunanina ba Mami ta sake jefomun wani hot glance sannan tace "Zahra kin bata mun rai! ashe haka kika koma baki iya girmama babba ba? Mahmud of all people na duniyar nan? kinsan matsayinsa kuwa a wajena? toh in baki sani ba wallahi ke da shi baku da bambamci a zuciyata. kin taba ji ance yazo garin nan tunda kikai wayo? kin taba ganinsa a Abuja? amma Zara kiyi masa wannan gaisuwar? babu ladabi babu sannu da zuwa babu ya hanya? haka aka koyar da ke? ba laifi!
Gabadaya hawaye ne cikamun idanuna nayi sauri na mayar dasu domin ganin yanda Ran Mami yayi tsananin baci a kaina musamman da yake bata cika mun fada ba balle ta kai ga fadamun wannan deep maganganun! don haka hankalina ya tashi sosai don idan akwai abinda nafi tsoro a duniya bai wuce bacin ran ta ko fushinta a kaina ba! don haka yana dawowa daga wayar da yayi na durkusa har kasa raina na zafin aikata hakan da zanyi ga wanda baisan darajar dan adam ba. cikin muryar kusa da fashewa da kuka nace "I'm sorry Ya Mahmud! kayi hakuri bazan sake ba" hannu ya saka ya dagoni cikin murmushi gabana ga soma faduwa! cewa yayi "Zara you are my sister! my blood darling sister!...so stop making me feel like i'm a stranger to you ok? feel free with me!"
Duk da dinbin mamakin da kalamansa na karya da yaudara suka bani ban kasa girgiza kaina ba kafin ya sake mun hannu! yace "good!
Mami na duba a sanyaye nace "I'm sorry Mami! I'm very sorry bazan sake ba! murmushi tayi sannan tayi hugging dina tana patting bayana! "it's okay my girl! ya wuce! yanzun kizo mu tafi nayi dropping ki" nace "Mami da Aisha zamu tafi" cewa tayi "Aishan guda nawa ce banda wadda ta yi mun sallama ta tafi?" cikin mamaki na kalli Mami nace "ita da wa Mami?" cewa tayi "bansani ba amma dai ta tafi".
Jikina a sanyaye na shiga motar su Mami ita ke driving Mahmud na gefenta nikuma ina gidan baya. Gidanta kawai ta wuce damu bance komai ba domin ina tsoron na sake wata magana Mami tayi fushi.
Muna isa na balle murfin motar na futa domin a bala'in gajiye nake! ga raina da ke a bace! dakin Mami na nufa amma ina murdawa naji a kulle sai da na jira tazo ta budemun! ina shiga na soma zage kayan jikina na shige toilet! Ruwan micella na Gievinne na dauka da cotton na goge make up din fuskata tass sannan na samarwa kaina ruwan wanka mai zafi sosai na shige cikin farin jacuzzin ina maida numfashi. saida Mami ta kwankwasa mun kofar na tuna cewa a toilet nake domin duniyar tunanin da na shiga. cikin sauri nayi wanka da alwala na futo. Mami na bakin gado cikin kayan baccinta da alama a daya dakin tayi nata wankan. "bacci kikayi ne a toilet din?" ta tambayeni cikin tsarewa da ido! murmushi nayi nace "I'm so tired ne wallahi ina zaune ina jin dumin ruwa!" cewa tayi "gobe dai za'a gama sai ku huta!" nace "wallahi kam! nagaji da wannan buki" mikewa tayi tana cewa "bari na hado tea ban wani ci abinci a wajen bukin nan ba zakisha?" girgiza kaina nayi ina shafa lotion. ta juya ta futa! ina gamawa na zura lallausan kayan baccin Panda bakake da na gani akan gadon ta futo mun dasu na kwanta! tsananin gajiya da bashin baccin da na ci na kwanaki suka hadu suka saukar mun. ko second goma banyi ba nannauyan bacci ya tafi dani.
bani na farka ba sai asuba. rabonda nayi baccin 4hrs ban farka ba tun kafin matsalar da nake ciki ta shigo rayuwata. Bayan munyi sallah da Mami na koma baccin mai nauyi kamar wanda na kwana a zaune.
cikin baccin naji tana tashina! dakyar na bude idanuna ina karanto addu'ar bacci! Mami ce tsaye a kaina har tayi wanka ta shirya! "zara 11 fa kike wannan baccin kamar wanda kika fara yanzu! tashi muyi breakfast" cikin sauri na mike ina mamakin yanda akai lokaci ya tafi haka. toilet na fada nayo brush da alwala na futo cikin sauri nayi sallar walha!sannan na futo parlour! dif! na tsaya cak sakamakon ganin Ya Mahmud kan dinning din cikin jallabiya baka wul! saida Mami ta dago ta dubeni nayi maza na taho kafata tana Sarkewa! i dont know why nakejin wannan awkwardness din duk lokacin da yake waje! saida na isa gefen kujerarshi na risina na gayar dashi! da murmushi ya amsa kamar jiya harda cemun how was my night! nace lallai wannan mutum ya iya duniyanci wato don a gaban Mami ne yake mun haka! zama nayi muka soma karyawa shi da Mami suna ta hirarsu yawanci ta family ce da abubuwan da suka faru wanda bata samu damar sanar dashi a kafar da take sanar dashi din ba wadda ban sani ba. why on earth bansan yanda akai akwai irin wannan shakuwar tsakanin Ya Mahmud da Mami ba? idan akwai abinda zan iya tunawa game da shi basu dayawa kasancewar bani da wayo lokacin da yake zaman gida. yana kammala secondary school kuma ya wuce Oxford zamanin banfi shekaru tara ba sannan daga lokacin ban sake jin duriyarshi ko ganinshi ba. sai dai labarinshi a bakin manya. labaran kuwa ba masu dadi bane a game dashi don haka babu amfani na mayar da hankalina ga sanin wasu abubuwa a tare dashi.
a hankali sautin wayana yake futowa daga daki wanda ya dawo dani daga hayyacina. aje cup din hannuna nayi na mike na shiga dakin na dau wayar!
number Ummansu Aisha nagani na daga da sauri. "Hello Umma ina kwana?" cikin sarkakkiyar murya ta amsa sannan take cewa "Zara daman jiya Aisha kun kwana bata da lafiya ne?" mamaki ya kamani! ina zanga Aisha har mu kwana tare bayan gida ta tafi???
kafin na gama tunanin ta katseni da cewa "Zara kina jina?! dazu ta shigo gidan tace kanta na ciwo nace ta shiga daki ta kwanta zuwa anjima na shiga na dubata sai zazzabi mai zafi ta dai sha paracetamol amma inaso nasan me ya faru ne tun farko kafin muje wajen likita na mishi bayani. kan nata ya hanata magana me tsawo!
Tohh fa!!! wata sabuwa inji yan caca! Ya zanyi nasan me yake faruwa bayan ba gida daya muka kwana ba? na dai san Mami tace mun Aisha ta tafi gida kila gidansu Ihsan ta koma ta kwana a tunaninta nima can zan koma daga wajen bukin tunda ni banyi magana dasu ba! sai kawai na tsinci kaina da cewa "Umma bara kawai na nazo sai muyi magana" na katse kiran da sauri na lalubi layin Ihsan da tunanin ita tasan abinda yake faruwa! sai da na kira sau uku ta dauka! ita ta soma cewa "nagode da kikai tafiyarki gida Zahra ko sallama bakimun ba kika tafi daga ke har Aisha daga kwanan jiya fa shikenan" wait!! kaina ne ya sara na soma ganin duhu nayi maza nayi baya na zauna bakin gado! Aisha ba'a gidansu Ihsan ta kwana ba? bata kwana a gida ba? ina taje daga wajen buki? a ina ta kwana?! ji nayi jikina yana shivering zuciyata na bugawa. Ihsan ce ta sake cewa "hey! are you there? kinsan akwai budan kai da yamma ko Zara? danAllah ki iso da wuri! ki gayawa Aisha ta manta wayarta nayi mamaki ma da bata kira tayi confirming anan ta bari ba!" sulalewa wayar tayi daga hannuna na runtse idona ina karanto Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Aisha hali ta chanja? wani abu ta taka? wata rayuwar ta sauya? wasu kawayen ta samu? wani ra'ayin ta dauka? menene yake faruwa? A ina Aisha ta kwana? abinda yake ruri a kaina kenan yana amo kamar zai fasa mun kwakwalwata!
Sanin bani da amsoshin abinda yake faruwa ya sanyani mikewa na koma falon a sanyaye! Mami ce ta lura da yanayina tace "lafiyarki?" shikenan jimami nace "Mami Aisha ce ba lafiya yanzu Umma ta kirani" da mamaki tace "Aishar? kamar ba jiya na ganta tana harkokinta ba? me ya sameta?" na amsa "wai ciwon kai da zazzabi" Mami tace "Ashsha!Allah ya sauwake! kila wannan zirga zirgar ce da gajiya!
nidai sama sama na kammala shan tea din na mike ina cewa "Mami bara na shirya naje naga jikin nata na dawo" girgiza mun kai kawai tayi na wuce da sauri na koma daki. cikin azama nayi wanka na shirya cikin bakar abaya mai purple crystals! na feshe jikina da turarukan Mami. na dau jakata da waya na futo!Har lokacin suna kan dinning hirar bata kare ba! "Mami bani aron key dinki naje na dawo!" na fada cikin muryar tausayi! sai da ta dubeni tsab sannan tace "idan Aisha ta tafi makaranta zanga yanda zakiyi Zara" murmushi nayi nace "Allah Mami kullum sai nayi wannan tunanin nasani nima ABU nayi applying ko BUK yanda nima na tafi wani wurin daban." cewa tayi "yanzun ma zaki iya sauyawa ai" murmushi na sake yi kawai na wuce na dauko key da ke kan console din falon nace "Mami na tafi!" tace "toh ki gaishe ta kuma ki dawo da wuri"! na amsa sannan na dubi Ya Mahmud nace "Ya Mahmud sai na dawo" duk maganganun da muke kamar baya falon sai lokacin ya dago oily idanunshi yace "ok! drive carefully! na amsa ina futa daga falon!

Tunda na dau hanya kirjina yake bugawa don bansan me zancewa Umma ba kuma bansan halin da Aishan ke ciki ba! da na isa cikin gate din kuwa sai naji kamar na juya na koma! dakyar na samo dakiya da karfin zuciya na futo daga motar na zagaya na baya na dau jakata na nufi cikin gidan Ina amsa gaisuwar David mai baiwa flower ruwa!
A parlour na samu Umma tana waya na samu waje na zauna kirjina yana bugu! da hannu taimun alama na shiga dakin kafin tagama! na mike na hau yan steps din da zasu kaini dakin Aisha na murda kofar a hankali.
A can karshen gado na hangota ta cure wuri guda kamar jaririya gashinta ya bazu ya rufe fuskanta. gabadaya tausayinta da kauna irinta yar'uwa ta jini ta kamani. na karasa a sanyaye na aje jakata kan drower na hau gadon! kamshin turarena yasa ta dago fuskanta da ya kumbura yayi jajawur! yarr! tsigar jikina ya tashi! i cant remeber the last time naga Aisha cikin irin wannan yanayin! kafin wani abu ya taba zuciyarta tayi kuka ana dadewa. mace ce very with the most strongest heart. ba abinda yake bata tsoro babu abinda yake gigitata! sannan ina kallon kwayar idanunta na gano ba ciwo kadai ke damunta ba zallar damuwa ce wadda idan kowa ya kasa ganowa ni bazan gaza gano taba a dalilin yanda nayiwa Aisha sanin da ko yunwar cikina albarka!

Cikin nutsuwa na gyara mata gashin kanta na tattara shi na daure da ribbon din da ke gefenta! sannan nasa hannayena ina goge mata hawayen da yake biyo kuncinta! cikin murmushi na riko hannayenta in kallon ta! "Aisha it's me! your best friend! your favourite sister....! hankalina ya tashi matuka Aisha da ganin halin da kike ciki!na tabbatar ba ciwo ke damunki ba sai dai idan damuwan ce ta kawo ciwon! Aisha plaease ki gayamun meye yake damunki? mecece matsalarki mu warware ta? meye damuwarki mu magance ta? ki fadi ko menene yake cikin zuciyarki zan baki best listening ears kuma bazanyi judging dinki ba! and i promise you babu wanda zaiji halin da muke ciki kuma zamu zauna kamar yanda muka saba mu warware koma menene tare kinji besty?"
Duk maganganun da nake idonta kirr a kaina ta gaza ko kwakwkwaran motsi sai kirjinta da yake ta dagawa yana bugawa! ta kasa cewa komai!
hannunta na sake matsewa cikin nawa ina cewa "Aisha ko dai kin chanja mun matsayi ne? shin akwai ranar da zatazo wadda zaki kasa gayamun wani abu game da ke? akwai lokacin da zaki boyemun damuwar da kike ciki Aisha? karki manta fa mun saba sharing ma junanmu komai na rayuwa babu wanda yake boyewa dan'uwansa halin da yake ciki! don Allah Aisha ki taimakeni ki gayamun damuwarki!
cikin dasashshiyar murya tace "Babu komai Zahra! ba abinda yake damuna kawai bani da lafiya ne! kirjina na zafi kuma!" hannunta na saki cikin disappointment ina mata wani kallo sannan na mike daga gadon na nufi jakata na rataya! "fine then! nagode da sabon matsayin da kika bani Aisha! zan tafi Allah ya baki lafiya" na wuce da sauri zan futa! na kama handle din kofa naji an riko bayana! na juya ina kallonta! wani matsanancin kuka ta saki me ban tausayi wanda yai masifar sanyayamun jikina gabadaya! dakyar na mikar da ita muka koma bakin gado! a kafadata ta sake kifa kanta tana kukan kamar ranta zai futa nikuma nayi shiru kawai ina saurarenta domin na fahimci kila idan tayi kukan zata samu sassauci!

Helo dearis! people are complaining that i always post late! i am sorry, but i have alot of things i am taking care of! i can't post a new chapter everyday, nor every two days! but i promise you i will try my best and update as soon as i can!
so back to our Story, meye kuke tunanin ainihin abinda yake faruwa? Ai ina Aisha taje ta kwana? meye ya faru da ita? meye cikin zuciyar Zara? me yake shirin faruwa? shin me ya kawo Mahmud Nigeria? meye makasudin zuwansa gidan bayan bikin Faisal??
kuci gaba da bina cikin labarin!
Thank you all for your love and prayers!

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now