A hankali na murda kofar falon na shiga cikin sallama!. Da wani kyakykywan saurayi nayi tozali.
Fari ne sol wanda ya cakude da hutu da jindadi da da kwanciyar hankali. Sanye yake cikin wani bakin Voil wanda ya sake futo masa da hasken fatarsa. Damtsen hannunsa daure da sarkar agogon "ROLEX" kwandalele sai walwali yake. Falon gabadaya ya gauraye da kamshin "Tamford"
Wani tsadadden murmushi ya saki a daidai lokacin nake zama kan kujerar da ke saitin tashi. "Sannu da zuwa" na fada cikin tatatusar murya! "Yauwa sannu beautiful" nima murmushin nayi mai kayatarwa. I cant resist smiling anytime ya kirani da "beautiful" din nan.
Cikin so da kauna me yawa muka gaisa tare da tambayar mutanen gida.
Sannan ya dora da cewa "Zara dafatan kin gayawa Dada cewa ba da wasa nazo ba...Allah yasa sun shirya yi miki aure yanzu!" Murmushi kawai nayi kaina a kasa bance komai ba. Ina "twins?" Na sauya maganar. Nan da nan ya wangale baki ya soma far'a a dalilin tambayar yayanshi da nayi. " twins suna lafiya suna kuma gaishe ki" nace "ina amsawa" "ina Mamansu?" Na sake tambaya cikin faduwar gaba don na kosa kwarai naji wani abu game da Maman yaran. Shikuma duk lokacin da na dauko maganar sai ya sukwane. Kuma shi don kanshi bai taba mun magana akanta ba. Wannan yasa na soma tunanin ko suna tare ko sun rabu?
Murmushi yayi yace "she is doing fine...itama tana gaishe ki" zaro ido na danyi kirjina ya buga da karfi har nayi dana sanin tambayar! Ko gane hakan yayi? Cewa yayi "Ai zamu je very soon ku gaisa da ita ne" a sukwane na dago na dube shi idona sun sauya kala don tsananin kishi.
Sai ya sake sakin murmushi baice komai ba.
Knocking din kofa ya dawo dani daga balaguron da na tafi. Aisha ce ta shigo dauke da katon tray wanda aka shake da kayan motsa baki ta iso a hankali. Sai dai tana karasowa naga annurin fuskarta ya dauke firgice, tsoro, mamaki, da tashin hankali ya maye gurbin sa. Mamaki ya kamani domin bansan dalilin faruwar hakan ba sai dai kafin nayi wani motsi tuni ta shanye su duka ta nemo nutsuwa ta dora akan fuskarta. Akan center table din dakin ta aje tray din sannan ta janyo shi gaban Imam a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a ciki.
Shine ya fara nuna ta yana cewa "i have finally got to meet our besty"
Da wani irin yanayin da ban taba sanin Aisha dashi ba ta soma gayar da Imam kanta a sunkuye. Duk yanda yaso ya jata da hira ta kasa sakewa kamar ba Aisha magadisu ba wadda take sabo da mutum ta mayar dashi dan gida cikin mintina kadan. Son tambaya, son jin abinda ya shafe mutum, son sanin komai Aisha ce kan gaba. Bata da kwauron baki ko kadan don hakane ma duk inda ta shiga sai tayi qawaye kuma duk inda ta tsinci kanta bata shan wahala don bata da bakunta ko jin nauyi. Sai gashi yau tayi ligib ta nabba'a a gaban mutumin da take ta cin burin ranar da zasu hadu tayi cheking shi from head to toe. Tayi masa duka tambayoyin da take ganin sun dace har sai ta gano in ya cancanta ya zama mijin aminiyarta.
Kaina ya daure tamau da mamakinta.
A karshe ma dai sallama ta mishi tace mun sai na shigo. Sai na fara tunanin ko bayan futowata ne wani abu ya faru ko wani abu akai mata.don haka hankalina ya rabu biyu. Mintina talatin muna zaune sannan ya duba agogon hannunshi. Cewa yayi "ya kamata na tafi kada Dada tace na rike ki dayawa. Kuma ina da family meeting after magrib! Am i permitted?" Nayi murmushi kawai tare da mikewa. Shima tashin yayi yana gyara zaman hularsa a kansa.
Kallona yayi a tsanake yace "ga wannan (ya nuna wasu manyan jakunkunan kwalaye masu tambarin Gucci da Chanel da kuma wata katuwar leda) na kine. Wannan kuma (ya nuna wata ledar fara sol me tambarin Rasasi) na Dada ne. Sannan ya saka hannunshi a aljuhu ya ciro sabbin bandir din 200 ya aje kan table din yana cewa "wannan na besty ne duk da taki tsayawa muyi hira tare"
Kyam na tsaya ina kallonshi har ya kai aya sannan nace "No gaskiya sunyi yawa ka barshi. Dada ma fada zatayi" tafiya ya soma yi yana cewa "a'a ko dai kadan sukayi Zarah. Kicemun Dada bata karbar karamar kyauta".
"Ba haka bane don Allah ka rage daga zuwa......" ban karasa ba yace "shhhhh. Its okay! Ki bayar sadaka idan bakyaso" ganin ranshi ya baci kawai na hakura. Har bakin motar na raka shi sai da ya bude ya shiga ya zauna sannan ya dubeni yana murmushi "i'm leaving...." cikin sanyi nace "sai yaushe?" Ni kaina bansan lokacin da maganar ya futo ba.
Da wani smirk a fuskanshi yace "will you miss me?" Na rufe fuskata ina yiwa kaina dariya.
"Lalala wato su Romeo hirar har a bakin mota ko?" Na juya da sauri don jin muryar Aisha! Itace ta iso tana ta faman murmushi wanda yayi confusing kwakwalwata domin dazun nan ba haka yanayinta yake ba.
Dariya yayi sosai sannan yace "bayan bestyn mu bata tsaya anyi hirar da ita ba? Amma kin dau bashi. Next time babu inda zakije!" Cikin dariya itama tace "gaskiyane ka biyoni bashi zan biya kuma" mun jima muna wasa da dariya kafin yayi mana sallama ya tafi.
Ganin ta warware sosai ya sanya kawai na kyaleta ban tambayeta game da abinda ya faru dazu ba. Ita ta kwaso kayan ta kawo su gaban Dada ta aje. Dadan tace ta bude mata. Manyan turarukan mata ne guda biyu yan gidan "Gucci" da kuma agoguna guda biyu kirar "Swatch" sai abaya hadaddu guda uku na Armani. Ita kuma Dada turaruka ne guda shida masu kamshi. Dakinta aka kwashi kayan aka kai aka aje muka koma dakina da Aisha don gabatar da sallar magrib!
YOU ARE READING
HAUSA ARAB PART 1
General FictionAlqalamin qaddara yana aiki akan kowa ba tare da zabin wance ko wane ba. Kowanne bawa da irin na shi salon rubutun, na wani ba irin na wani bane.