Wani irin tsoro da tashin hankali nagani cikin idanunta yayinda hawaye yaci gaba da zirga zirga akan fuskarta! cikin sanyi na riko hannunta na fara magana cikin nutsuwa!
"Aisha na dade da sanin wani abu game da tsakaninki da Imam! Tun ranar da kuka fara haduwa a gidanmu naga halin da kika shiga da yanda kika kasa sakewa dashi duk alwashin da kika dauka akan tambayoyin da zaki masa da gwajin da zaki mai! na futo ne da niyyar nayi miki tambayar hakan sai naga cikin kankanin lokaci kin batar da wannan expression din kin dauko yanayinki nada. abun ya bani mamaki amma sai na zabi nayi shiru kawai! Ranar da zanje gidansu Imamu kika rakoni bakin mota naga irin kallon da kukewa juna wanda ya dau hankalina sosai na fara tunanin lallai akwai wani abu mai kama da so a tsakaninku! ban kuma gasgata zargina ba sai ranar birthday dina da na rokeki kizo gidanmu muyi wa Imamu cin cin kikayi zuwa! amma sai gashi kuzo school dinmu tare a mota daya! Duka yanda kike kaucewa idan na kawo miki zancen Imamu ina sane da shi da kuma rashin son haduwa da shi da kikeyi! tun abun bai soma damuna ba har na soma damuwa. da na tambayi Ihsan a ranar da kukazo school dinmu game da abinda ta fuskanta tsakaninki da Imamu sai tace mun da banyi introducing dinku a matsayin ke aminiyata bace shikuma fiance dina babu abinda zai hanata tunanin ke da shi babu soyayya a tsakaninku! tabbatarwar da nayi bani kadai nake ganin haka a tsakaninku ba ya daga mun hankali fiye da tunani!a hankali alakarmu ta soma sauyawa da ke ya zama muna wasan yar buya. idan kuwa har muka hadu mun dinga kokarin kawar da abubuwan da suke ranmu har mu rabu! watarana da baki da lafiya nazo gidan nan kuna asibiti da Umma baku dawo ba sai iky na samu na shigo dakin nan na zauna ina duba abinda zai tayani hira kafin ku dawo. kamar wasa naga diary dinki..abun ya ban mamaki don nasan tuni muka dena wannan shiryen rubuce rubucen! toh sai dai kuma cin karo da nayi da wani babban al'amari ya sanyani nutsuwa na karanta!"
Idanunta ta zaro gabadaya! tana kallona cikin mamaki da dimuwa! murmushi nayi naci gaba.
"Anan nagane kin soma son Imamu ne tun kafin nasan shi tun kafin nasan zan hadu da shi! acikin littafin nagane baki da burin da ya wuce samun Imamu toh amma kash! a ranar da kika fara ganinsa ganin ya zamto mummunan gani domin kin ganshi ne a matsayin wanda yake son aminiyarki! a take nagano dalilin sauyin yanayinki ranar da kuka hadu da Imamu da kuma dalilin da yasa kike gujewa maganarsa da ganinsa! na ga abubuwa masu yawa a diary din ciki harda text din da kika tura masa akan kin manta diary dinki a motarsa kina rokon kar ya bude miki!
Bansamu damar gane komai tar tar ba kuka dawo! in zaki tuna a gurguje na bar gidan nan don kar naci gaba da zama ina kallonki na kasa jure abinda nagani! tun daga ranar nake bibiyar duk wani motsinki da na Imamu. akwai ranar da na kira wayarki Iky ta dauka tace kinyi bako, bana mantawa ranar Mahmud ya dawo daga tafiya baizo wajena ba bayan al'adarshi duk sanda yayi tafiya ranar da ya dawo yake zuwa wajena. a jikina naji tabbas wajenki yazo don nasan baki da saurayi idan kuma dan'uwanku ne nasan gida zaki shigo da shi kuma Iky zata san ko wanene shi! Na tsani kaina Aisha a lokacin nayi dana sanin haduwa da Imamu nayi dana sanin kasancewa da abinda kika so a rayuwa sannan nayi damarar bar miki Imamu koda son shi zai mun illa.
sai dai na rasa ta inda zan bullowa abun, na rasa ta ina zan fara. ke kadai ce wadda take taimakamun idan na shiga damuwa mu gudu tare mu tsira tare mu samu mafita tare sai kuma ya kasance banida damar tarar ki akan wannan magana! da Ihsan muke tattaunawa kuma ita take bani shawarar nabi komai a hankali! Ranar dinner din Ihsan wani abu ya faru wanda ya daure mun kai ya sakani tunani domin bayan an tashi mami tace mun kunyi sallama kin tafi gida sai kuma da safe Umma take tambayata me ya sameki a gidan su Ihsan kin dawo ba lafiya. kafin na tambayi Ihsan din ita take cemun wai kin bar wayarki kafin mu tafi dinner kuma ta tabbatar mun baki kwana gidansu ba. ba zaki taba gane halin tunanin da na shiga ba Aisha! ban iya sanar da kowa wannan maganar ba sai yau da nake gaya miki amma wallahi bana awa ashirin da hudu abun bai fado zuciyata ba! tambayoyi ba irin wadda banyi zuciyata ba akan ina kikaje? da wa kuka tafi? a ina kika kwana? meye dalili? rashin sanin amsar ya sake dagula mun lissafi! Hakana kin rage walwala kin daina nishadi kin rage shiga sabga ta wannan ya sake sani tunani. a dai dai lokacin da nake tunanin neman Jidda naji ko zan samu wani karin bayani a wajenta domin acikin diary dinki naga kin rubuta kuna bukatar neman wadda zakuyi magana da shi kuma kika saka sunan ta don haka na yanke shawarar muna dawowa daga Saudi zan nemeta!
Game da Imamu kuwa na gama sarewa. don zuwa wannan lokacin bana yiwa kaina sha'awar aurenshi kamar yanda kema bana miki fatan auren mutum irinshi. naga alamomi masu yawa akan boyayyun munanan halayen Imamu. sannan akwai wani abu tsakaninsa da Ya Mahmud wanda na kasa ganewa. yana matukar kunyar Ya Mahmud kuma yana kaucewa magana da shi yayinda shikuma Ya Mahmud yake masa kallon "Nasan komai game da kai" sai dai daga haka bai sanar dani komai ba. bayan mun dawo daga Saudi mukaje Kano anan ne naga abinda ya daga mun hankali. wani mummunan hoto aka turamun ta email dina Aisha! Imamu da wata yarinya.........
abinda ya gigitani har ya sakamun wani irin ciwon kai!Ya Mahmud ne ya bukaci muje wellcare mu siya magani, shigata ke da wuya Aisha naga Jidda tare da Imamu, sai lokacin na tuna cewa ai hoton da aka turo mun Jiddan ce aciki!"
YOU ARE READING
HAUSA ARAB PART 1
General FictionAlqalamin qaddara yana aiki akan kowa ba tare da zabin wance ko wane ba. Kowanne bawa da irin na shi salon rubutun, na wani ba irin na wani bane.