HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE FIFTEEN

837 69 3
                                    

                 LIVERPOOL LONDON
-----------------------------------------------------------
Yau kwanakin Mahmud biyar a gadon asibiti yana karbar kulawa ta musamman. likitoci sunyi iya bakin kokarinsu wajen ceto rayuwar Mahmud a lokacin da numfashi ke mar barazanar yankan kauna. cikin ikon Allah sun shawo kan matsalar sun kuma yi masa abinda ya dace.
Ciwon sa ne na tsayin shekaru tara ya tayar masa wato ciwon zuciya wanda tsananin damuwa da tashin hankali suka haddasa masa. tun bayan lokacin ko sau daya ciwon bai sake waiwayarsa ba a dalilin matukar kokarin da yake yi wajen bin doka da ka'idojin ciwon da kuma gudunmuwar babban amininsa Faisal da Uwar da babu kamarta Mami da kuma girma da darajar Addu'ar da mahaifinsa yake yi babu ji ba gani a kansa. a wannan karon ba wani abu ne ya tada ciwon ba illa tsundumowar Safna cikin rayuwarsa a lokacin da bai tsammani ba ko a cikin mafarki. Bai taba tunanin nan kusa ko nesa wani abu mai kama da soyayya zai shigo cikin rayuwarsa ba domin yasan tuni ya tattara abubuwan masu kama da soyayya ya haka rami
mai zurfi ya binne! rayuwa yake mara hope ko buliding future sai dogara da Allah da kuma bin abinda duk ya shigo masa ba tare da neman zabi ba.
A dai dai lokacin da ya saisaita rayuwarsa ya dau damarar cigaba da rayuwa cikin wannan yanayi ya sadaukar da duk lokacinsa da gabarsa da zuciyarsa da aljihunsa ga ceto ran bayin Allah da taimakawa na kasa da shi sai wani babban al'amari ya bullo wanda yayi masa gingiringim a kai a ranar da ya kai ziyarar amsa gayyata ga Eng Garba Galadanci.
Labarin da ya gaya masa game da Safna ya girgiza shi ya wujijjiga shi ya kuma tsaya mishi rai. ba wannan ne na farko da ya samu mace tace tana sonsa ba ba shine na biyu ba ba kuma na uku ba. hakan ya zama jiki a tare da shi tun daga kan turawa hausawa indiyawa harda larabawa mazauna London babu kalar budurwar da baiyi ba. illa iyaka dai su suke kidansu suyi rawarsu akansa sai kalilan da sharrin tarkon shaidan ya yi tasiri akansa ya dan basu lokacin yin waya da shi na wasu makonni ko watanni daga haka kuma sai ya barar da su ya fuskanci wasu. a karshe ya tattara su yayi holi dasu kwata kwata don ya gano suna bata lokaci ne da surutan banza da na hofi.
Ga Safna har ga Allah tausayin maraicinta da halin da ta tsinci kanta aciki ya ladabtar da zuciyarsa ba wai so ba. domin ya dade da sanin cewa So guda daya ne tak! kuma yayi shi ya gama. sannan ita Safnar wata gwana ce wajen janyo hankalin dan'adam da duk abinda ta fahimci yafi so. da wannan damar tayi amfani ta janyo hankalin Mahmud har ta samu burbushin matsayi a gefen birnin zuciyarsa kuma da alama kofar shiga ainihin zuciyar tashi tana dab da bude mata ta shiga daga ciki. Duk sati take tattaki da kanta ta taho daga cikin garin London tazo Liverpool wajensa ba kuma zaman banza take ba tunda ta fahimci son da yakewa abincin gida musamman na gargajiya ta ware kwanji tana yin abinda bata taba zaton zatayi din ba. wato girkawa wani mahaluki abinci. sai gashi a dalilin soyayya har kalolin da bata sani ba take nemowa ta koya ta sarrafawa Mahmud. wadannan abubuwa suka taru suka hana Mahmud yi mata korar da ya saba yi wa yan matansa. suka kuma hana shi gwale ta. Domin irin so da kulawar da Mahmud yake samu daga Safna babu mahalukin da zai ture su duk iyaka bakin halinsa. balle Mahmud mutum ne mai sanyin zuciya da nagartattun halayen kwarai sai dai kafin ka fahimci hakan sai ka zauna da shi kayi mu'amala da shi.
kwanakin da yayi a kwance Safna kullum tana cikin zaryar asibiti. duk da basa bukatar mai jinya a asibitin yake wuni ta dawo gidanshi ta kwana.shi dai Eng ya zubawa sarautar Allah ido yana mata addu'ar samun shiga a wajen burin nata.

   A ranar da ya cika kwana goma a ranar aka sallamo shi. tare da Safna suka shigo gidanshi. Ita ta tsaya a kitchen ta samar masa dan abinda zai ci shikuma ya wuce dakinsa.
wayarsa ya dauka ya kira Faisal a karo na goma bai dauka ba. lallai Faisal yayi fushi da shi tunda har yayi kwanaki uku yana kiransa bai dauka ba. kuma da alama yana da niyyar cika alkawarin da yayi ikirarin dauka akansa idan har ya kasa halartar bikinshi. gashi yau Thursday tuni anyi daurin aure babu shi. "Ya salam" ya dafe kansa yana tunanin abunyi. da azama ya janyo laptop dinshi ya soma booking din jirgi zuwa Nigeria cikin rashin sa'a bai samu jirgin yau ba sai dai gobe da daddare. sai da ya kammala sannan ya samu nutsuwar shiga toilet yayo wanka da alwala.
bayan ya idar da sallah ne yana shirin kimtsawa Safna ta turo kofa ta shigo.
da mamaki ya kalleta fuskarsa daure!
ganin tana shirin zama yayi gyaran murya yace "Ahm Safna wannan ba tarbiyya bane  ki dinga shigomun daki anyhow ko knocking babu! kin manta ni ba muharramunki bane ko? in kin manta na tuna miki! banason wadannan al'adun aron daga addinin da ba namu ba. please ki dinga kiyayewa!"
jikinta  ne yayi mugun sanyi bata ce komai  ba ta mike ta futa. yayi gajeran tsaki yana la'antar rayuwar da musulmai suka daukarwa kansu a dalilin zama cikin turawa. shi kansa Eng din ya rasa sakaran ina ne da zai bar 'ya kamar wannan ta taho wajen saurayi kwanaki sama da goma don lalacewa! yana shafa man yana tsaki har ya kammala. shigar bakaken kaya yayi na bacci ya futo ya same ta a falon.
kamar yanda ya saba ledar cin abinci ta shimfida masa a kasa ta jera abincin da tayi masa. Minced meat macaroni da soup din kaza. sai kunun tsamiya a gefe. kasancewar baya jin dadin jikinsa ya sanya kunun kadai yayi shan kirki sannan yasha magungunansa. yana kammalawa ya dauko key din daya dakin ya bude ya nuna mata ta shiga ta kwanta ya dora da cewa "gobe ki tashi da wuri tare zamu shiga London. inason zuwa 7 mun futa" cikin mamaki take kallonsa. a ranta tana so tace masa jikinsa bai gama kwari ba da zai soma futa saidai yanda ya daure fuska tamau kwarjininshi ya hanata cewa komai bayan toh. ya juya ya koma dakinsa ya kwanta.
   washe gari kuwa ana idar da asuba Mahmud bai koma ba. parking din dakinsa yayi ya adana duka muhimman abubuwan adanawa ya hada jakar tafiyarsa guda daya sannan ya shiga wanka. cikin minti arba'in ya kammala shiri cikin bakin jeans da farar shirt. Da wuya kiga turawan London da kalar kayan da ya wuce black and white. zama cikinsu ya sabar masa da hakan shima. jibgegiyar jacket ya dora akan kayan nasa ruwan toka yayi amfani da scarve din Lv kalar rigar sanyin ya nade wuyansa. Idan da akwai wani abu da yake sa ka gane mutum kana ganinsa ba tare da saninshi ba shine kwatance. to idan kanaso ka kwatantawa wani mutum Mahmud zaka ce masa a kullum wuyansa na rataye da mayafi ne designer. idan yaga dama ya rataya idan yaga dama ya nade wuyan idan kuma yaso nishadi sai ya daura shi sosai akansa kamar rawani. wannan shine irin nashi style din da anan gaba zamuji yanda ya samo shi.

      A  gaggauce sukai breakfast din da Safna ta tashi tun bayan assalatu ta girka shi da hannunta. wannan ke sake shigar da ita zuciyar Mahmud cikin sauki. dubanta yayi a tsanake yace "ki hada jakarki zan mayar da ke gida nayi wa Eng godiyar barinki da yayi kizo jinyata" wani murmushi taji ya kubuce mata na jindadin kalaman Mahmud ba tare da la'akari da in tayi tunanin mai zurfi fa magana ya caba mata! rashin gane hakan ya sanya shi me maganar murmusawa.
Jirgin kasa suka bi zuwa garin London daga nan suka dau taxi. amma a maimakon taji ya fadi sunan unguwarsu sai taji yana cewa Driver ya kaisu SELFRIDGES. take kuwa annurin fuskarta ya karu.
     Yana gaba tana biye da shi suka shiga cikin katon shopping department stores din. kana ganinshi kasan yayi sabo ainun da zuwa wajen domin babu waige waige ko jeka ka dawo ya nutsa ciki har ya iso wajen brand din "Louis Vuitton" wata baturiya ta taso tana mishi gaisuwar sani da kuma sabo! sannan ta basu wajen zama. jakunkunan mata take dauko mishi yana dubawa a take ya siya guda uku. sannan ya dubi Safna yace "ki dauki duk abinda kike so".
daga nan wajen Chanel ya nufa ya kwashi kayan kwalliya na mata masu yawa. ita dai Safna tana kallon ikon Allah! hakana ya matsa kantin "Dior" ya kwashi turaruka. Ita dai Safna banda lissafin abinda yake kashewa babu abinda takeyi. ta gagara daukan komai ta zama kamar wata yar kauye!
tunaninta menene mutumin nan ya taka? ta tabbatar ba da likitanci ya ta'allaka ba! to wanene shi?
shikuwa ya lura da yanayinta tsab wani zubin yayi murmushi wani lokacin ya share ta kamar bai gane komai ba.
sai da ya kusa kammalawa yace "Safna kinsan bazan jiraki ba idan nagama? baki dauki komai ba time yana tafiya kuma ni sauri nake" kawai tsyawa tayi gabanshi tana blushing! kasa daure dariyanshi yayi ya soma zabar mata da kansa.  cikin lokaci kalilan suka kammala suka futo.
kanta yayi masifar nauyi domin idan lissafinta yayi daidai to abinda Mahmud ya kashe ya kai 12.5M lokaci daya siyayya daya a rana daya! Dankari. daya tunanin kuwa ya tafi ne akan me zaiyi da kayan matan da yake ta jibga kamar baisan darajar kudin ba? gashi ta gagara yi masa ko da tambaya daya domin harshenta a sarke yake da mamaki!
Mahmud kam rabuwa yayi da wata Safna ya shiga turawa Maminsa sako ta email akan tahowarsa da lokacin saukarsa!
lokacin da suka iso unguwarsu la'asar ce ga kuma himilin kaya don haka a gidansu Mahmud suka sauka ta tayashi shiga da kayan. Anan ma wani shock din ta samu ganin yanayin gidan da yaci uban nasu a tsaruwa da shiryuwa. sallah kadai sukayi ya rakata gidansu inda sukai sabani da Eng sai waya Mahmud yayi masa ya mishi godiya. Mamansu Safna kuwa bakinta har kunne kamar zata zube a wajen saboda dadin ganin alakar Mahmud da diyarsu ta soma karfi.
shidai ya lallaba ya baro gidan cikinsa kulle da dariya. Yana ganin ko dan maganin ciwonsa ya kamata ya karbi Safna don bata gajiya amusing dinshi.

                 wajejen Assalatu tayoyin Jirgin British Airways suka dira a Nnamdi Azikiwe Airport na garin Abuja. Mahmud na daya daga cikin fasinjojin da jirgin ya kwaso daga garin london a kujera mai daraja ta farko wato first class!cikin wannan lokaci babu abinda zuciyar Mahmud take sai dokawa. yayinda jikinsa yayi sanyi kalau kamar mara laka. hankalinsa yayi mugun tashi tunaninsa ya birkice. cikin azama ya soma kiran suna Allah da ya kawo mishi dauki da nutsuwa da ingantaccen Confidence din da zai fuskanci kasarshi ta gado bayan gudunta da yayi bai sake waiwayowa ba tsayin shekaru goma da watanni uku cif.
  lokacin da aka baiwa fasinjojin damar futa dakyar yake daga kafafunshi don tsananin sanyin jiki. yana tafiya yana rangaji ya futo terminal din inda Ya hango kyakykyawar uwar da bata tsufa saidai karin kamala da haiba da nutsuwa cikin fara kal din laffaya tana ta murmushin da kana ganinta zaka tabbatar yana tahowa ne tun daga karkashin zuciyarta.
Yaron nata is not a kid anymore. don ya wuce mukamin da zata kirashi Hausa Arab, dan saurayin da ta rako airport tana kuka yana kuka mai shekaru ashirin da bakwai. wannan yafi dacewa ta kirashi  Dr.Mahmud Ahmad Lamido kwararren gyanecology consultant din da ake alfahari da Shi a kasar turai. har yanzu kyawunsa da farinsa da gayunsa na nan tare da shi sai dai wata suma da ta lullube fuskarsa a yanzu wadda ta karo masa haiba da kamala da kwarjini da kuma nutsuwa ta musamman. shekaru goma cif da suka wuce wannan sauyin ya tabbata!
duk iya girman nashi da kamalar tashi da jinkai da takama bai hana shi yar da jakar hannunsa ya runtumo a guje ba lokacin da ya hango Uwar tashi abar alfaharinshi!
cikin hawaye ta rungume Mahmud da wata irin murna mara misaltuwa dukansu suka rushe da kuka mai tsanani kai bakace a tsakiyar jama'a scene din yake faruwa ba.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now