LONDON
-----------------------------------------------------------
Zaune yake kan lallausar kujeran da ke falonshi ya mike zara zaran kafafunshi akan center table yana karkada su a hankali. kallo daya zakai masa ka gano tarin damuwar da ke kwance acikin zuciyarsa wadda kyakykyawar fuskarsa ta bayyana.
Idanunsa a lumshe suke yayinda zuciyarsa ke tunkushe da tunani da bacin rai da damuwa marasa adadi.
a hankali ya soma tari yana danne kirjinsa don azabar da yake ji daga saitin kirjin nashi na hagu. sai wani bugawa yake yi kamar zai ballo waje.
Tun yana tarin a hankali har ya soma cin karfinshi. a galabaice yake karanto kalmar shahada cikin saduda da rayuwa da duk wani abunda yake cikinta. cikin mintina kalilan ya birkice numfashi ya soma gagararsa idanunsa suka soma kakkafewa yayinda ya dora duka hannayensa akan kirjinsa. a hankali jini ke futowa ta bakinsa yana gangarawa kunnensa da habarsa har fara sol din shirt din jikinsa ta soma rinewa da jinin.
cikin wannan hali Safna tayi sallama ko nace tayi knocking a kofar kitchen. Sharifa da bata san abinda yake faruwa a gidan ba ita ta tsame hannunta Daga cikin girkinta ta bude kofar. harara safna ta zabga mata ta wuce cikin gidan kai tsaye ba tare da ta amsa gaisuwar yarinyar ba.
tana saka kafarta a parlour taci karo da tashin hankalin da ya sanyata zunduma ihu ta ruga a guje tana girgiza Mahmud. ina! tuni hankalinsa ya gushe ba ya fahimtar komai sai kokawa suke da numfashi.
Ihun Safna ne ya janyo hankalin Sharifa da ke kitchen ta shigo falon a guje! itama ihun ta kurma ganin halin da ubangidan nata yake ciki.
cikin azama ta dauko waya ta nemi asibiti. mintina kalilan kuwa ambulance ta iso aka kinkime Mahmud akai asibiti dashi. tun daga motar suka sanya masa robar taimakawa numfashi Safna na rike da hannunshi tana faman kuka har suka isa Liverpool hospital wato asibitin da yake aiki. nan da nan likitoci suka karbe shi tare da rufuwa akansa don ceto rayuwarsa.!!
-----------------------------------------------------------
NIGERIA
Na kai awa daya a zaune a wajen ina kuka kafin na tashi na shiga toilet. ruwa na hada na shiga na zauna naci gaba da tunani dakyar nayi wankan da alwala na futo nazo nayi sallar isha'i na kwanta. ranar ko abincin dare bansa a bakina ba. haka na dinga juyi a gado sai wajen asuba bacci ya daukeni. ko da na tashi da safe idona yayi lunkuma lunkuma saboda kuka da rashin bacci. Wayar Ihsan ce ta tasheni da sai na makara magiya take mun na taho da wuri mu wuce tare flight daya. don haka nayi maza nayi wanka na shirya cikin sabuwar Sheraton Super olive green mai ratshin purple. make up din dole na zauna nayi don kar a gane nayi kuka.
bayan munyi sallama da Dada Na shiga mota na wuce gidan Mami inda na sameta tana cikin motarta tana jirana. cewa tayi da kanta zata kaini gidansu Ihsan ta danka amanata a hannun Mamansu lolz!(Mami is overprotective) jakar kayana na ciro daga booth din motata wadda zan bari anan gidan Mami zuwa motarta.
muna tafiya muna hira har muka isa gidansu Ihsan. Da matukar murna da jindadi Mamansu Ihsan da yan'uwanta suka karbi Mami abinda yasa ta kara jin dadi kenan. Anty Batulu kanwar maman su Ihsan ita tace wa Mami "kinga ni zan karbi amanar Zara. kafata kafarta harmuje mu dawo lafiya insha Allah kamar tana hannunki ko kuda bazan bari ya taba ta ba" aka kwashe da dariya. cikin mutunta juna aka rako Mami har wajen mota sannan suka juya. kallonta ta dawo dashi kaina tace "Toh Zara ki kula da kanki! ki kula da kanki don Allah in bana ganinki Allah yana ganinki. banason shirmen banza banason yawo banason shige shige ki rike mutuncinki don wallahi ba don ina ganin mutuncin Ihsan ba bazan taba lamunta ki tafi wani gari buki babu ni ba don haka ina jan kunnenki da ki nutsu." cikin murmushi nace "duka na rike wannan Mami Insha Allah zan kiyaye bazanyi abinda nasan bakyaso ba" tace "good" sannan ta bude jakarta ta ciro rafar yan dari biyu ta bani. na amsa nayi mata godiya sannan mukai sallama.
muna hanyar Airport naga kiran Aisha. kamar bazan dauka ba dai na daure na daga! "hello besty kuna ina?" bata san yanda in ta kirani besty din nan yanzu nakeji ba da ta daina. "muna hanyar Airport" na bata amsa a takaice! ta sake cewa "banji dadin yanda Abba ya hanani bukin nan ba wallahi Zara ki baiwa Ihsan hakuri" cewa nayi "babu komai zan gaya mata. na kira ki jiya ai naji yanda kuka yi dashi Iky ta dauka tace kinyi bako" sai da ta danyi jim sannan tace "eh wallahi bama bako bane don dai yana sauri ne bai shigo cikin gida ba" tabe baki nayi a raina nace "ya shigo daki ma wannan matsalarku ce macuta kawai" a fili kuwa cewa nayi "ok! ki gaida Umma sai anjima" mukai sallama! Ihsan da ke gefena ta kalleni tayi murmushi nima na mayar mata "take it easy please kada kiyi wani abu da zamu dawo muna da munsani bamuyi ba. har yanzu fa bamu da hujja kuma in mukabi komai a sannu a hankali sai munfi samun nasara" nace "hakane ina matukar kokari Ihsan abun is not as easy as you think amma ina addu'a" dafani tayi tace "yess! addu'a ce kadai abun yi. so please kiyi chasing duk wata damuwa daga ranki it's your girl's wedding" ta kare maganar tana dage gira! dariya nayi sosai a raina ina tunanin yanda muke da Aisha da shakuwarmu! hooo duniya gidan rikici!
kafin azahar muna cikin garin kano inda muka tarar da convoy din bakaken luxury cars suna jiranmu.
kyakykywar tafiyar awa biyu babu gajiya ko gargada balle tsalle tsallen hanya saboda ingancin motocin suka kaimu Fadar Gumel.
inda ya kaure da kade kade da bushe bushe da guda na isowar amarya.
YOU ARE READING
HAUSA ARAB PART 1
General FictionAlqalamin qaddara yana aiki akan kowa ba tare da zabin wance ko wane ba. Kowanne bawa da irin na shi salon rubutun, na wani ba irin na wani bane.