HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE TWENTY- NINE

852 59 5
                                    

WELLCARE,Kano!

Ups! Gambar ini tidak mengikuti Pedoman Konten kami. Untuk melanjutkan publikasi, hapuslah gambar ini atau unggah gambar lain.

WELLCARE,Kano!

Bansan ta yanda akai mukai wannan tafiyar ba naji kawai Mami na cewa a biya ta gidan Alhaji Rabo aminin Abba(mahaifina) mu gaishe shi! ban ankara ba ashe anyi parking zamu koma motarsu Ya Mahmud domin Driver Inna zai tafi dauko yara a Islamiyya! Faisal ne yake tukin Ya Mahmud na gefensa! kamar a saman iska haka nake jina lokacin da na balle murfin motar na futo! muka shiga cikin bakar Jeep din muka zauna kaina yayi masifar nauyi yana ragargaza kamar zai tsage! ban ankara ba naji mun iso gidan wanda shima din yake cikin GRA!

Duk da na rufe wayar na gaza dauke hoton da na gani kan screen din wayar cikin kwakwalwata da zuciyata! bakina ya gaza daina furta kalmar "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun" i can't believe this! wallahi i never thought bakin halin Imam zai iya kaiwa haka! Na shiga uku! He is my fiance for heaven sake!! Ya Rabb! take me out of this horrible situation!

Mami ce ta dafani tace "lafiyarki? anzo bude mu futa! cikin tsananin dauriya na dago kai ina runtse jajayen idanuna nace "Mami i can't go in! kaina kamar zai tarwatse wallahi!" Gani nayi duka su hudun sun juyo da idanunsu kaina! babu tantama yanayina ya bayyanar da tsantar halin da nake ciki. Akan goshina Mami ta dora hannunta taji kuwa zafi rauu don tuni temperature dina yayi sama! "all of a sudden?" inji Ya Mahmud! Mami tace "lafayarta kalau fa da ta tashi! har ma muna gidansu Safna! Sannu suka shiga yimun Ya Mahmud yace "kinga Mami ku shiga bari mu samu pharmacy a samar mata magani! Faisal ina zamu samu pharmacy mai kyau?" cewa yayi "muje Wellcare" Mami ce tace ita zasu shiga da Ya Nuratu muje mu siyo maganin mu dawo! sai da suka shiga Faisal ya juya akalar motar muka tafi Welcare!
Bayan mun hau titi ne Ya Mahmud yace "ina ganin ma ya kamata ki fara blood test, in ban manta kwanaki ma haka kikayi!" ni dai shiru kawai nayi ina binsu da toh domin ni nasan ainihin ciwona ba maganin asibiti ko allura ne zai warkar dashi ba! sai da muka biya wani Lab a Bomfai sukamun gwajin muka tsaya result ya futo muka karba! duka abubuwan da yake tunanin suna damuna negative! Na lura daga lokacin ya dan shiga tunani don sai jefi jefi suke magana da Faisal har mukazo Wellcare!
Su biyu suka futa don cewa nayi bazan iya shiga ba! na gyara zamana a bayan motar ina rike kaina da ke mugun sarawa! ga wani amai da yake tasomun na musamman! waya na ciro na kira Ya Mahmud nace masa ya hadomun da maganin amai don nasan idan na fara babu sassauci! tana shiga na soma jin ringing a motar, ya manta wayar! kawai yanke shawara nayi na shiga na gaya masa duk da ban taba zuwa wajen ba amma nasan bazan kasa gano su ba!
A hankali na bude motar na futo na maida lock sannan na rufe! dakyar nake takawa don tsananin ciwon da kaina yake mun! murda kofar da zanyi na shiga wani tattausan sanyi da kamshi suka daki hancina! "wajen yana da kyau sosai!" tambayar da gefen da zanbi nayi naje wajen maganin nayi! daya daga cikin ma'aikatan ya nuna mun. har na soma tafiya na tsaya cak! a dalilin kamshin da ya cika mun hanci, kamshin Tomford! kuma kamshin Imamu a koda yaushe! Daga idanun da zanyi naci karo da wata santaleliyar budurwa cikin wata irin shiga mara sha'awa wadda bata boye komai na halittar ta ba. what! Jidda? wannan Jidda ce! kawar Aisha! kan na sake cigaba da wani tunanin sai ga Imamu ya rufo mata baya da da uwar siyayyar da suka lodo! Ya hayyu ya qayyum! da sauri nayi kwana na labe ina fidda wani nannauyan numfashi! mintina biyar na sake lekawa suna ficewa daga wajen fuskokinsu cikin annuri da walwala!
Take na tuna hoton da aka turomun dazu a wayata! it is the same girl! wallahi itace!Jidda kawar Aisha wadda ta yarda da ita! Jidda ce a hoton! dimaucewar da nayi ne ya sanyani gaza tsayawa duba fuskar wadda nagani tare da Imamun sosai!
what on earth is happening to me????
Dai dai lokacin Ya Mahmud da Faisal suke tahowa amma me? blurry nake ganin hotunansu a kwayar idona, da sauri Ya Mahmud ya karaso yana cewa "lafiya? meyasa kika shigo?" bude baki nayi ina kokarin yi mishi magana amma ina......wasu manyan taurari nagani suna tartsatsi kafin tunanina ya dauke diff!

HAUSA ARAB PART 1Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang