HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE THIRTY-SIX

916 71 22
                                    

THE HOTEL @ fifth avenue,
Manhattan, New York.
_______________________________
A hankali Mahmud ke takowa cikin dakin da mahaifin na shi yayi masauki a garin New York din amurika bakinsa dauke da sallama. cikin farin ciki mahaifin nashi yake amsawa tare da jin wani alfahari na kasancewar wannan halitta matsayin da a wayenshi! Musamman yanda ya futo a tantagaryar dangayen nashi a yau. futowarsa kenan daga  dakin taron karawa juna sani na manyan likitocin duniya! Dogon gayen yafi kama da kyawawan bakaken turawa a yau fiye da balarabenshi na kullum! Yana sanye cikin rantsatstsun suit yan gidan "Saint Laurent" Navy blue daga ciki farar shirt ce wadda ta fiddo da tsarin kwalliyar tashi keeping everything classy and professional! gashinsa ya wani kifo kamar kwando, dagani ya samu extra care ta musamman a wannan safiyar! Ga wani rikitaccen kamshin turarukan Ralph Lauren da suka cakude suka bada wani kayataccen kamshi mai rikitarwa! a yau kam bai yi amfani da turarensa kwalli daya da ya saba ba!
A nutse ya soma sabule bakaken covers din da ke kafarsa samfurin Calvin Klein ya jerasu inda suka dace sannan ya karaso cikin dakin yana murmushi!

"Daddy barka da yamma" ya  soma gayar da mahaifin nashi cikin girmamawa da duka guiwoyinshi a gaban farar sallayar da Daddyn yake zaune da alama sallah ya idar! cikin murmushi Daddy ya amsa kafin su soma maganar da ya hadasu a wannan waje! tiryan tiryan Mahmud ya soma koro mishi jawabi game da IMAMU da muggan boyayyun halinsa wadanda kalilan din mutane suka sani.
"Daddy bama wannan kadai ba, har yara ne dashi twins yan maza wadanda suke zaune a Paris da matar da bai taba aura ba. ba'a san wacece mahaifiyar yaran ba amma da na bincika sosai an tabbatar mun yarinyar balarabiyar Egypt ce wadda ya hurewa kunne tun suna karatu a America! a dalilinshi ta bar iyayenta kuma a garin haihuwar yaran ta rasa rayuwarta! Daddy Imam ba karamun Shaidanin mutum bane me badda kama, wanda bai san shi ba bazai taba kawo wani abu mara kyau game da shi ba balle yayi tunanin mugu ne! Tun ranar da na samu labarin shine aka sakawa rana da zara hankalina bai kwanta ba, nine bin kowacce hanya ta diddigi don hado duk wata hujja da zan gamsar da ku munin dabi'unsa da halayensa! kai tsaye bani da daman kushe shi a wajenku don ya gama siye zuciyoyinku da yaudararshi sannan ita yarinyar tayi zurfi a kaunarshi ta inda raba su lokaci guda zai zama abu mai matukar wahala, banso lokaci har ya kure haka ba, amma duk da haka nagode Allah da ba'a kai ga daura aure ba"

Shiru Daddy yayi na wasu mintina baice komai ba! Amma fuskarsa ta bayyana matukar bacin rai da disappointment mai yawa! Ta wani bangaren kuma yana ji kamar ya gaza wajen zamewa Zara uba na gari, domin gashi yana shirin kulla aurenta da gurbataccen mutum irin Imam ba tare da ya sani ba, iya bakin kokarinsa yayi bincike akan iyayen Imamu da shi kansa amma bai samu wani abu wanda bai gamsu da shi ba!

Cikin tausayi Mahmud ke kallon Daddy yana karanta zuciyarsa da yanayin fuskarsa filla filla! ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya tausasa sauti cikin ladabi yaci gaba da magana!
"Daddy kada ka damu, ba laifinka bane, kuma ba gazawa kayi ba wajen yin bincike, ba kowanne bincike ne zai gano wannan biyayyun sirrin ba sai idan an soma binciken ne cikin zargi tare da hadin guiwar wadanda Imamu yayi rayuwa da su a kasar Paris da America! Nima din nasamu duka wadannan bayanan ne a dalilin sanin wasu abokansa da nayi shekaru da dadewa da kuma wani likita Dr. Philip anan Newyork yake! ba don haka ba, da wallahi sai bayan an yi auren rayuwar Zara zata fada cikin garari! Domin Imam mutum ne mai hadarin gaske!"
Ajiyar zuciya Daddy ya sauke sannan ya waiwaya gefen drower gado yana neman ruwa don gabadaya makoshinsa ya bushe ya tsatstsage! Dasauri Mahmud ya mike ya dauko goran ruwan da cup yazo gabanshi ya tsiyaya masa ruwan rabin cup din ya bashi! Bai bar tsugunon ba har Daddy ya shanye ruwan yayi hamdala sannan ya karbi cup din ya hada da robar ya mayar! kafin ya dawo wajen da ya tashi ya zauna!

Sun dauki lokaci mai tsayi suna tattauna wannan magana da hanyoyin da za'abi wajen daukar mataki da warware matsalar! daganan Mahmud yayi wa Daddy sallama don shi a safiyar gobe zai bar kasar America ya wuce South Africa! Lokacin da ya futa daga dakin binsa Daddy yayi da ido yana jin wani irin feelings mara misaltuwa akan shi,  Tun yana yaro Mahmud mai kaifin basira da hankali ne, mai sanin ya kamata ne, mai gaskiya ne, mai jin kai ne kuma me tausayi ne! Yana da halaye wadanda za'ai alfahari da su. A koda yaushe yakan dora bukatun dan'uwansa akan nashi, ya shige gaba akan farincikin wani ya manta da nashi, koda yaushe burinsa ya faranta ran mahaifinshi!

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now