3

649 56 5
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*INA GODIYA SOSAI DA COMMENTS DINKU💃🏻💃🏻💃🏻 K'arangiya tana gaisheku🤣*

*Lamba ta 3*

Bafade rik'e da wuyanshi yake fad'in,.  "Akwai kan bisa wuyan ko ta yi sa'ar rabashi da gangar jikin??"

Gaba d'aya wurin yayi shiru wasu Kam basu daina yin dariya k'asa k'asa ba, Baffah jikinshi yana rawa ya k'araso wurin Dije zai tab'ata ta yi saurin fad'in

"Aljani danduna rik'e man hannunshi kar ka bari ya tabamu idan ya tabamu hannunshi zai k'one zai k'one kurmus tamkar yanda wuta take cenye kara"

Aiko da sauri Baffah ya ja baya Maigari yace da Liman ya matso ya yi mata addu'a da nufin a samu aljanun su kwanta ta karb'i hukuncinta, Aiko Liman yana matsowa kusa da ita ta yi wata zabura ba mutanen da ke wurin suna kallo ba har shi kanshi Liman sai da yaji tsoro, hannunshi yana rawa ya d'ora hannunshi akan goshin Dije ya fara tofa mata addu'a, Aiko Dije ta kurma kuwwa ta fara surutai tana cewa

"Ba zamu fita ba kama daina addu'ar nan  ko'ina ba zamu je ba muna nan har sai Maigari ya janye kudurinshi na son d'aukar hukunci akan god'iyarmu, akanta zamu tada garin nan akanta zamu mayar da garin nan toka"

Liman dai sai zuba addu'a yake yi sai cen Dije tace

"Ayi hak'uri zamu yi magana za muyi magana nace"

Maigarin ya yi Liman alamu da Ido akan ya dakata aiko Dije ta fara fad'in

"Mune muka zama kura mune muka fito a siffar kura muka biyosu, kuma a gaban idonta muka kashe mutum biyar a farkon gari amman ba mutanenku bane mutanenmu ne, tunda ta take muna 'ya'ya muka biyosu ita da kawayenta, don yanzu haka abokan fadan nawa ya jiman raunuka saboda fad'an da muka yi da junanmu Ni da yan uwana aljanu don haka Bari in fito a siffata ku gani nasan zaku tausaya man"

Kowa na wajen yace

"A'a kar ka fito"

Wasu suka ce "ALLAH ya baka lafiya ka ja Yan uwanka ku tafi kawai mun yafe mata"

Dije ta sake cewa

"Idan na tafi kuka daketa fa ko kuka d'auki wani mataki kanta fa zan gayyato Yan uwana mu sake zama kuraye mu zo garin nan sai mun kashe kowa don kowa ma ba zai tsira ba"

Aiko cikinsu ya duri ruwa Maigari yace, 

"Ba za'a tab'ata ba amman don ALLAH in kuna wa ALLAH ku yi nesa da garin nan, Kuma ku yi alk'awali akan ba zaku sake shiga shirginmu ba"

Dije tace   "zamu tafi amman har sai mun mayarwa da sarkin fadawa kanshi da muka tsige"

Bafaden ya shafo kanshi da yasha mola sol! sol!  yace,  "Ranka ya dad'e ai ya koma da kanshi ma gashi a saman wuyan ina jinshi"

DIJE ta mike tsaye cikin zabura ta katsa masa wata uwar harara da idanuwanta da suka jajawur! Tace

"Wa ya Gaya maka kanka ne a sama to bari ka ji ku kuke ganinshi kamar Kai irin naku to wannan Yar karamar dabbarmu ce dake bacci a saman kanka, naka kan yana cen bangon duniya bakin kogin zumburbur an fara had'a kayan dafuwarshi da ka yi sake nan da safiya zaka rasa ranka da an jefashi cikin tunkunyar dafuwar"

Bafaden ya zabura dafe kan yace

"A cire man dabbar a maidoman kaina don ALLAH ka taimakeni"

Dije ta kyalkyale da wata mahaukaciyar  dariya sannan ta yi shiru tana tare da Kara kunnenta a iska kamar mai sauraren wani abu sai cen  tace,.  "Ranka ya dad'e Sarki gani nan zuwa yanzu a yi man afuwa yanzu zan kawo maka"

Tana k'are surutan tace,  "Babana Sarkin aljanu yace da Ni in tattaroku yanzun nan dukanku mu had'u a bakin Ruwa ayi shari'ar a cen"

Kowa ya gwalalo Ido waje Aiko cikin sauri ta fara fad'in

"Ya zajisu ya zurmukus banbaradusa ya zamburkusadduna ya......."

Kafin kace me duk wuri ya hautsine da k'ura saboda dan neman gudun famfalakin da mutane suke yi, Bafade dafe da kanshi yana gudu yana fad'in

"Ki tashi daga baccin nan don girman ALLAH ki dauko mani kaina, tun kafin a fara dafuwarshi a bangon duniya"

Ganin mutane da yawa sun watse sai Yan gani kasheni ciki kuwa har da Maigari da Liman sannan da Baffanta da ke nesa da su yana haki, ta k'ara keta kuwwa tace

"Ku saurareni zamu tafi amman ko harara aka yiwa god'iyarmu Dije sai mun dawo tare da gayyar rundunar Yan uwana aljanu, mun tafi Sarkin fadawa ga kanka Nan gobe ka k'ara dan gidan marasa tausayi amman ka sani za mu zo mu tafi da kai da ka kuskura ka fito fitsarin dare, mun tafi zo muje ke kuma sarkin bacci"

Sai kawai aka ga Dije ta fad'i yaraf tana fisge fisge tana wani Abu da kai ta gwalo Ido sai cen ta yi luf kamar Mai bacci.

Liman ya sake tofa mata addu'ar ya fara Kiran sunanta, Dije ta yi wukil da Ido d'aya suna had'a Ido da Liman ta zabura ta mike zaune tace

"Don Allah ka yi hak'uri WALLAHI da gaske naga Kura Ni da su Ladiyo, a tambayesu aji ai ko su zasu fadi gaskiya don ba Ni kad'ai na ganta ba har dasu, a gaban idona taci mutum biyar a farkon gari"

Maigarin yayi shiru yana nazari sannan yace,.  "Ai kinci sa'a komi ya wuce tunda an wankeki tashi kije gida amman kar ki sake zuwa daji debo ciyawa"

Dije ta zaro Ido tace

"Na shiga Uku ita akuyar tawa me zata ci idan na daina fita daji?"

Maigarin ya yi Yar dariya yace

"Ni Zan sa akawo maki Ciyawar kullum ki dinga bata saboda baki da isashiyar lafiya tashi kije gida ki kwanta ki huta ALLAH ya baki lafiya"

Dije ta washe baki tace,.  " Harda dussa?"

Yace  "har da ita tafi gidan kawai"

Dije ta Mik'e tana tsallen jin dad'i tace

"Na gode Maigari ALLAH ya ja da nisan bacci kuma ya baka lafiya ya tsare gaba kuma yasa kar ka mance watarana kaki aikowa"

Maigari sai Ameeen yake fad'i don a matse yake da ta bar wurin tun kafin shima yayi sanadin abunda zai janyo ta k'ara kassarashi.

Dije ta nufi wajen Baffahnta tana dariya tace, "Na huta da zuwa Daji akuyata zata sami ciyawa kullum"

Baffah ya fisgo hannunta suka nufi gida, Mutane da sun hangota su yi ta darewa suna gudu Dije kam sai tsallen cin nasara take yi, Liman kam binta yayi da kallo yayi dariya don shi tsaf ya gano ba wani aljani da ke kanta tsabar iya shege ne ke damunta, amman ko ba komi ya jinjina mata tunda har ta samowa kanta hanyar kwatar kai, daga wannan gangamin jidalin data hadowa mutane  a cikin gari.


Akafta😅




D/AUTA CE✍🏻

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now