1

363 25 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Masu buk'atar Littafaina ga su kamar haka:*

*TARTSATSI*

*RUWA DA K'ANK'ARA*

*BAKAN GIZO*

*DIJE K'ARANGIYA*

*BAK'ON YANAYI sai dai shi na kud'i ne da d'ari uku kacal zaki sameshi a complete d'inshi😇*

*Lamba ta 28*

Haka Baffah ya shashantar da zancen aka yi ta fira har aka yi magrib suna tare da Safwan sunata fira duk da ba wani sabawa ya yi da su ba amman ba laifi sun d'an tab'a fira, kiran sallah'r yasa Dije ta yi cikin Gidan tare da matan biyu domin su yi SALLAH, su Baffah kuwa suka yi masallacin da ke k'ofar gidan.

Ko da dare ya yi Hajiya Mama ta saka Dije ta yi wanka da kanta ta nuna mata yanda zata yi kwalliya ba irinta haukarta da ta saba ba, ta d'auko  wasu sababbin kayan bacci masu shegen kyau tace ta saka, Dije kam saboda hud'ubar da Baffah'nta ya yi mata sannan da kashedin da Safwan d'in ya yi mata shi yasa ta rage shirme in taga wani abu da bata sani ba sai ta yi shiru ba zata yi ta surutu ba, bakinta alekum ta saka kayan tare da fessesa mata turaren da Hajiya Mama ta yi sannan ta kira Surry tace da ita ta je ta Kai Dije d'akin Safwan, Dije ta zaro Ido waje tace

"Hajiya me zanyi wajenshi Sabida ALLAH Ni kam cikin daren nan yanzu??"

Hajiya ta dafe goshinta tace,. "Ki je ki yi kwanciyarki a cen kafin da safe sai a kaiki gidanki in da zaku zauna da Mijin naki"

Dije ta zaro Ido waje tace,. "Kina nufin gidan nan zan bari???, WALLAHI idan na barshi an cuceni wa zai bani irin abincin da na ci d'azu mai d'an karen dad'i?"

Hajiya Mama ta dafa kafad'arta tace,. "Ki kwantar da hankalinki insha ALLAHu abincin da zaki ci a cen har sai ya fi na wannan Gidan dad'i, yanzu dai ki je da safe idan kika zo zan yi maki bayanin komi"

Dije ta marairece cikin kuka tace,. "Yanzu tsakaninki da ALLAH d'akin Namiji zaki kaini inje in kwana???bayan nasan ke ma kanki kinsan cewa hakan bai dace ba amman kike k'ok'arin turani???"

Hajiya Mama ta dafe goshinta ba shiri ta kai zaune tace da Surry da ke sunne kai tana k'umshe dariya da ta je, sannan ta janyo hannun Dijen ta zaunar da ita kan gadon ta yi shiru na d'an lokaci sannan tace

"Ai dai kinsan cewa an yi maki aure da shi ko?"

Dije ta d'aga kanta, Hajiya Mama tace

"Masha ALLAH to ai kinga shi baya cikin jerin mazan da aka haramta ki je d'akinsu ko?"

Dije ta yi shiru na d'an lokaci tana tunani tace,. "To Ni dai tsakani da ALLAH Innata ta hanani ko magana in dinga tsayawa ina yi da maza sosai, kuma yanzu idan Baffahna ya ji ai WALLAHI dole ma ne ya dakeni, Ni dai don hasken da ALLAH ya yi wa Qur'ani kada ki bari ya sake yi man ciki na uku"

Hajiya Mama ta zaro ido waje tace,. "Ciki na Uku?????"

Dije tace, "Eh ya yi man d'aya a k'auyenmu yanzu gashi d'azu lokacin da ya zo kirana muje wurinku sai da ya yi man d'aya yanzu haka Ina jin macizai sun fara taruwa a cikina kin gani WALLAHI cikina ya k'ara yin k'ato"

Hajiya Mama ta yi shiru tana nazarin maganganun Dijen sai cen ta nisa tace,. "To ta yaya yake yi maki cikin halan don inji in yi masa fad'a ya daina kada ya sake??"

Dije ta b'ata fuska tare da ciro hannunta duka biyu ta nunawa Hajiya Mamar tace,.  "Duba ki gani kowane hannu nawa da kike gani akwai cikinshi d'auke a ciki, gashi ina jin tsoron macizai da yawa idan na haifosu bansan ya zanyi da su ba"

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now