*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻*
*Lamba ta 24*
Safwan ya zaro ido waje yace,. "Ci me...??"
Dije ta bata fuska ta bar wajen tana ta yarfa hannun alamun k'yama ta nufi wurin Baffanta tace,. "Ka kwantar da hankalinka Baffah duk bayan kwana biyu Ni zan dinga zuwa ina dubaku kaji?"
Ta k'are maganar tare da langab'e kai, Baffahn ya yi mata wani kallo sannan yace,. "Za ki yi man shiru ko sai na mazgeki?? k'iri k'iri kin sa komi ya lalace muna saboda bak'in sakarcinki, to ni Kinga tafiyata idan kin tashi ki bisu ku je bangon duniya ma in kina so"
Yana kare fad'ar maganar ya mike fuuu! Yana kakkab'e riga ya nufi hanyar Gida, Maigarin ya kalli Dijen yace
"Kin amince zaki bi Mijinki?"
Dije ta d'aga kai tana yarfa hannunta da Safwan ya rik'e fuskarta a yamutse hawaye suna sauka tana saka d'ayan hannu tana sharewa, Maigarin yace
"Alhmdllh"
Sannan ya kalli IYAYEN Safwan yace,.
"Ku yi hakuri bayin ALLAH daga yanzu zuwa gobe za mu shawo kan matsalar, insha ALLAHu tun da sassafe sai ku kama hanya,saboda haka na wakilici MALAM Sanda na amice idan kun tashi ku je da Dije amman da rakiyar mutum Uku zuwa hudu ta gefenmu, saboda mu ga muhallinku kuma mu san inda za'a kai 'yarmu Dije"
Gaba d'aya suka amince da hakan, Maigarin ya kalli Bala ya ce, "Kai kuma sai ka nemi matar da duk kake so a garin nan ka aura tunda har hakan ta riga da ta kasance"
K'anen Mahaifin Bala ya fito da kud'i ya nufi wurin Baban Ladiyo ya ajiye kud'i tare da rusunawa yace,. "A matsayina na k'anen Mahaifin Bala ina nemarwa Bala auren yarka Ladiyo, idan ka amince yanzun nan sai a shafa fatiha kowa ya shaida"
Baban Ladiyo ya daburce ya kalli sauran d'inbin jama'ar da ke wajen yace,
"Ni Malam Shehu na amince da na baiwa Bala auren 'yata Ladiyo jama'a ku
sheda"Ladiyo ta zaro ido tare da barin wajen aguje ta nufi gida Mutane sai dariya suke yi mata, daga nan ba b'ata lokaci aka rarraba goro cikin dan kankanin lokaci aka d'aura auren Ladiyo da Bala, Baffah Kuma aka kai k'arshe akan za'a kwaso masa kayan d'akin Dije da aka jera gidan Bala a dawo masa da abunshi.
Sannan cikin mutuntawa Maigarin ya sa aka shigar da Iyayen Safwan d'akinsu Safwaan d'in, tare da yi masu tarba da abinci mai rai da lafiya wanda Safwan ya sa aka tanadar masu tun kafin su shigo garin.
Bayan sun kimtsa ne Safwan ya yi masu jagora har babban birnin garin ya sama masu masauki sannan ya juyo ya dawo k'auyen.
Dije kam cikin firgici ta koma gida tana yarfa hannu saboda ganin take yi ta hakan ne macizan zasu zube ba za su yi nasarar shiga jikinta su taru ba balle cikinta ya yi k'ato, su Jummala suka biyota d'ii! a baya sunata jin ina ma su ne suka sami irin wannan damar, ta auren mutum d'anboko irin Safwan ga shi fari mai kyau da shi.
Shigarta Gidan ke da wuya ta fara jiyo sautin Baffanta da ya ke ta zuba fad'a cikin d'aga murya, jiki a sanyaye ta isa d'akin nashi tare da rakubewa gefe tace
"Baffahna don ALLAH ka yi hak'uri ka barni in je birnin nan, ka ga idan na yi kud'i na zama likita shikenan zan zo in ta fi da kai mu zauna da ku kai da Inna inda nake"
Baffah ya maka mata wata Uwar harara da jajayen idanuwanshi yace,. "Ke dad'ina da ke sakarci shikenan tunda ya jaki gefe ya karanta Maki k'arya tare da yi maki wayon ya cusa maki ra'ayin biyarshi Ni ma hakan za ki yi man kenan ko?, To bari kiji aure dai an riga da d'aura ba kuma yanda Zan yi in kwanceshi da hannuna amman ki sani ba zaki tab'a biyarshi ba, na fi son abarman ke da igiyar auren saman kanki a gabana har k'arshe duniya aga in.........."
YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
Aktuelle LiteraturLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.