66

341 22 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Don Allah masu neman book ɗin Ƙarangiya daga farko ku yi haƙuri idan an kammala za ku sameshi a complete ɗinshi, plss ku yi haƙuri kunji😢saboda anyi nisa sosai kuma bana son kuna tambaya baku samu ba😆*

*Lamba 66*

Zee durƙushe ƙasa tana kukan fitar hankali gaban gadon da Mahaifinta yake kwance gorar ruwa saƙale a hannunshi, ya yi shiru yana sauraren sautin kukan nata, zuciyarshi cike fal da wata sabuwar damuwa don abunda ta aikata da saƙon da Safwan ya isar masa ba ƙaramin dukan zuciyarshi suka yi ba, duk da ko an sanar da shi cewa ya mayar da ita a matsayin matarshi, amman har wannan lokacin bai dawo cikin natsuwarshi ba,  wata ƙanwar Mahaifinta ce mai suna Baabaah Asabe ta katsa mata wata uwar tsawa ta ce

"Zaki ta shi ki bar ɗakin nan ko sai kin iyar da kashe muna ɗan'uwa ne?"

Zee ta miƙe jikinta yana rawa dafe da bakinta tana toshe kukan da yake fitowa tana kallon Daddynta bata son fita, cikin wata sabuwar tsawar Baabah Asabe ta sake cewa

"Ki fita na ce ko sai na fiddaki da ƙarfi ne?"

Zee ta dinga ja da baya tana gunjin kuka za ta fice Daddyn ya ɗaga hannu ya yafitota alamun ta zo wurinshi, da sauri ta dawo jikin gadon ta tsaya tare da riƙe kan gadon tana toshe kukan da ke ta fitowa a bakinta ta ce

"Don Allah Daddy ka yafe mani nasan na yi kuskure ka yafe man......."

Ya riƙo hannunta hawaye suna zuba akan fuskarshi ya ce, "me yasa kika aikata abinda zai janyo muna surutu a bakin mutane?" 

Zee ta riƙe hannunshi gam ta durƙushe ƙasa ta ce "plss Daddy ka yafe mani abun kunyar da na janyo maku don ALLAH"

Baabaah Asabe ta fisgota da ƙarfi ta fiddata ɗakin sai da ta yi nesa da ɗakin Daddyn sannan ta wurgar da ita cikin fushi ta ce

"Na ƙara ganinki a ɗakin nan sai na baki mamaki WALLAHI, abun kunya kuma da kike so ayi haƙuri kanshi ke me ya hana ki yi haƙurin a lokacin da kika ji ɓacin ran da ya janyo kika yi wannan rashin hankalin?, Yanzu in Banda ALLAH ya taƙaita wahala kinsan iya adadin rayuka nawa zaki saka cikin ƙunci?? Bayan waɗanda zaki yi sanadin barinsu duniya? Ko ko an faɗa maki cewa idan kin kashesu ke ƙyaleki za'a yi?, To buɗe kunnuwanki da kyau ki ji gidana zaki dawo da zama daga yau har zuwa lokacin da Mijin naki ya ga dama ya nemeki, tunda don kinga Yaya Mani ya sake maki da yawa ne shiyasa kike ganin dai dai kike da kowa, to har abada na gaba yana gaban kuma ba zai taɓa dawowa baya ba, don gashi cen yanzu kin baro mata gidan tana jin daɗinta da mijinta ke kuma ga ki nan kunci zai kasheki tare da Iyayenki, to Ni dai WALLAHI wannan karon bazan zuba mako ido kina yin abunda kika ga dama ba, dole ne a nuna maki cewa ƴa ce ke kuma haifarki aka yi akwai na gaba da ke har gobe"

Tana ƙare faɗar maganar ta koma ɗakin Daddyn inda ta taraddashi sai shar ƙwallah yake yi, da ban baki da lallami ta samu ta shawo kanshi da ƙyar ya yi shiru, cikin nadamar irin damar da ya baiwa Zee a farko yake ta baiwa yar uwarshi haƙuri akan abunda ya aika akan Aminu, don itama tana cikin mutanen da suka yi fushi da shi akan auren sai dai don ance hannunka baya ruɓewa ka yanke ka cire inji hausawa fa, don kam a wannan zamani da muke ciki  sau nawa aka yanke hannun aka jefar? ALLAH dai yasa mu fi ƙarfin zuciyarmu.

Zee ta daɗe durƙushe anan tana kuka har sai  da Ruma ta zo ta ɗagata suka shiga ciki, inda suka taradda mahaifiyarta itama sai kukan take cisga gwanin ban tausayi, saboda takaicin abinda Zee ta aikata wanda tuntuni take nusar da Daddynta akan sangarcin da ya yi mata don ko kaɗan baya so a kyareta bale a nuna mata laifin da ta aikata ta gyara, to ga irinta nan yanzu ta janyo masu abun gori wurin mutane, Zee ta je ta rungume Mahaifiyarta tana wani irin kuka mai cike da ban tausayi, Mahaifiyar ta tureta har sai da ta faɗi ƙasa, sannan ta miƙe tsaye tare da nunata da yatsa ta ce

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now