1

592 51 2
                                    

*💣DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*WAI! WAI! WAI RIGIJI GABJI WANI KAYA SAI AMALI LALLE DIJE K'ARANGIYA TAYI FARIN JINI BA KAD'AN BA INA GODIYA SOSAI MASOYA BOOK D'IN ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU A DUK INDA KUKE👍🏻*

*Lamba ta 4*

Ko da suka je gida suka taradda Inna  tana tankaden garin masara tana yi tana sharar hawaye, Dije da gudu ta isa wurinta ta fad'a jikinta har sai da tiren garin yayi tsalle rabi ya zube rabi ciki, Inna ta saka hannu ta Kai mata wani mugun dunku a baya har sai da ta gantsara, a zabure Dije ta mike tana sosa wajen tana zunburo Baki alamar taji haushin dukan,  Inna ta nunata da dan yatsa tace

"WALLAHI ki fita idona in rufe Dije na fara gajiya da rashin hankalinki,  ke kenan kullum janyowa kanki abunda za'a saka ki a bakin duniya muma ki ja muna zagi a gari, to bari kiji WALLAHI kwanan nan zan sa Delu ta tafi dake birni kamar yanda kullum take rokata akan in bata ke ta kaiki aikatau, kije cen ki had'u da masu horaki da kyau tunda Ni kin renani"

Dije ta fara dire diren kafa tana kuka tana fadin,  "ai WALLAHI Inna ko an kaini sai na dawo don ban zuwa birni a yanke mani Kai, Ni dai kiyi hak'uri don ALLAH na yi maki rantsuwa idan na sake ki dakeni"

Inna ta yi banza da ita ta makure jikin gina tana zunburar Baki tana mui mui da Baki tana sharar hawaye, sai ga Baffah ya fito bayi yana fad'in

"Wai ke Hasiya me yasa kullum kike tsangwamar yarinyar nan, to WALLAHI ahir dinki wannan karon don kuwa Dije dan sarkin aljanu ne a saman kanta, yanzu haka shi ya zo ya hana a d'auki mataki kanta Kan abunda ta aikata,  kuma yayi gargadin ko harara wani yayi mata za su dawo su sake hargitsa garin nan,  idan ke kinga ke zaki iya taron aradu da ka to karki fasa"

Ya kalli Dije yace

"Tafi ki dibi ruwa ki yi wanka ko da zakiji dad'in jikinki akan wannan sukuwar hawan dokin da aljanu suka yi akanki"

INNA Hasiya ta rik'e baki tace,   "yanzu Kai Malam har ka yarda da shirmen Dije? Lalle kam, to Ni dai ina baka shawara WALLAHI ka daina goya mata baya tana k'ara zama girtsatstsa, don wannan shirmen nata ba zai hanani jibgarta ba idan tayi laifi ko da ko tsamiya ce akanta Ni babu ruwana"

Baffah zai shiga dakinshi ya waigo yace,   "Kurar da kike tsoron zuwanta garin nan  to ko nan gidan ma zata dira idan ta zo wannan karon, sai ki je kiyi gaggawar yin rame a karkashin gadonki kinga idan ta zo sai ki shige kawai, don kuwa ba fashi zaki janyo fushin Dan Sarkin aljanu"

Yana K'are maganar ya shige d'aki abunshi domin a matse yake da yada hakarkarinshi ya huta ya samu natsuwarshi ta dawo.

Dije ta dibi ruwa cike fam da farin bokin fenti ta kinkimeshi tana nishi ta yi bayi tana ta gunguni, don taci alwashin sai ta debe haushinta da ruwan gidan don kuwa sai ta yi wacakarta son ranta dasu tunda Innar ta yi mata fad'a.

  Gashi sai sun zagaya bayan gidan suka debo ruwan ga wata rijiyar k'ofar gidansu Ladiyo kawarta, ta yi wankanta mai cike da barna sannan ta fito tana rawar sanyi daga ita sai siket a k'irji tana tsallen sanyi, Inna ta kalleta tace

"In dai takamarki mugunta kanki zaki yiwa in mura ta kamaki sai ki bidi mai ce maki sannu, sannan ruwa ma idan sun k'are ai kece zaki debosu don kinfi kowa sanin halin yayanki"

Dije ta zunburo Baki tace,.  "WALLAHI Inna kar ki janyo fushin murkustus barakus bn muruddika, yanzu ya sanar dani in fad'a maki suna jin nauyinki don ke kika haifeni sunce in sanar dake daga yau kar ki koma yiman fad'a, da kyar na basu hakuri suka ce sun yafe amman kar a k'ara "

INNA ta rik'e baki tace

"Au abun har ya kai cen? To ki fad'a masu ba k'ari ba har da k'are k'are sai na yi idan sun tashi su yi kuli kulin kubura dani"

Kafin Dije ta yi magana sai ga Usmanu ya shigo Dije tana ganinshi ta yi sum sum ta sassada ta shige dakin Inna kudum, Usmanu ya bita da harara yace

"Wai Inna yaushe yarinyar zata yi hankali ne? Yanzu abunda ta janyo kenan a garin nan? WALLAHI taci sa'a bani nan da sai na kakkaryata bak'ar jidalalla, sannan wannan siket d'in da na hanata sakawa ta fito tsakar gida dashi hakanan shi kad'ai bata bari, to duk abunda na yi wa yarinyar cen Inna kar ki ga laifina tunda ta nuna cewa ban isa ba, to Ni sai na nuna mata na fita kangarewa"

INNA tace "Halin Dije sai ita abita da addu'a kawai ko za'a ci nasarar abun, amman duka yau aka Saba?"

Baffah ya fito yana saka talkaminshi yace

"Ka dai yi a hankali in har ba so kake yi garin nan ya dawo toka ba, don kuwa Dije ba ita kad'ai bace idan ka janyo aka maidaka dan duk'usurun bak'in jakki ko bunsuru shikenan Kai ka janyowa kanka"

Ya fice abinshi Usmanu yaso yayi dariya ya mazge ya nufi randar ruwa Yana lek'awa ya hango ba komi duka tukanen duk ta kwashe ta yi wanka, aiko ya fara kwalla mata kira sai gata da kwandon kayan kwalliyarta tana shafa jar hodarta, cike da bacin ran da ke kwance akan fuskarshi yace

"Uban mi kike cikin Gidan da ba zaki je ki debo ruwa ba?"

Dije ta zunburo Baki tace,. "Yanzu na fito wanka fa Yaya sannan ace inje in debo ruwa? lalle ma!"

Usmanu yayo kanta zai daketa ta yi bayan Inna ta b'oye, cikin gargadi yace da ita WALLAHI muddin bata debo ruwan nan ba sai jikinta ya gaya mata yau.

A gurguje ta gama dige digen bak'in kwallinta ta danbara janbakinta ja fam da Baki sannan ta fisgi bokitin karfensu ta fita tana gunguni.

Ko da taje rijiyar makil take da mutane wad'anda wasu da yawa duka tsararta ne, tun daga nesa suna hangota wata ta yafito wata da ke kusa da ita tace

"Ga fa K'arangiya Nan Wai ashe aljanu ne da ita shiyasa ma masifarta kullum take gaba gaba"

Kafin Yar uwar ta bada amsa Dije ta k'araso ta ajiye bokitinta ta rik'e kugu, Kai tsaye ta matsa jikin rijiyar ta ce da wata mai suna Bintalo ta bata guga ta cika bokitinta, Bintalo ta yi mata kallon banza tace

"Kina so ki cika da wuri me ya hana ki zo da taki gugar?"

Dije tace,. "Taki nike ra'ayin dibar ruwan da ita zaki bani ko sai na janyo maki asara?"

Bintalo ta dafe gugarta da k'afa ta rik'e kugu tace,. "Me zaki iya yi ko an Gaya maki Ni ina tsoronki ne kamar kowa? To WALLAHI kika kawon wasa sai na maki danbanzan duka a wurinn...."

Kafin ta Kai k'arshe sai  ko taji saukar mari akan fuskarta, Bintalo ta zabura zata rama gugarta ta sub'uce ta fad'a rijiyar, cike da takaici taci kwalar Dije ta shaketa saboda tafi Dije girma nesa, kafin kace me idon DIJE sun yi ja cikin tsananin fushi tace

"Sakeni Bintalo"

Bintalo ta zakalkalo tace,. "Anki a sakeki ba za'a sake kin ba kiyi abunda zaki iya"

Dije tace   "nace ki sakeni Bintalo"

Bintalo ta k'ara shaketa cikin masifa  tace,    "Sai kin fiddo man gugata da kika sa ta fad'a ko ina sakinki, WALLAHI yau sai na ga k'arshen rashin kunyarki ba aljanu ba ko iccen kuka ne akanki sai na ci Ubanki..... "

Karaf! Sai jin k'arar saukar bokitin k'arfe aka yi a goshin Bintalo Dije ta kwad'a mata kasan bokitin, Aiko Bintalo ta fasa k'ara kafin kace me jini ya fara wanke mata fuska.



😳na yi nan🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️wlh Babu ruwana kar ace Ina nan aka yi 🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️

Akafta🤣🙌🏻




D/AUTA ce✍🏻

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now