*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*GA KIRA DA BABBAR MURYA BAN YARDA BA KUMA BAN AMINCE BA BAN LAMUNTA BA DA A SAKE CANZA KO A SAKE SARRAFA MANI LITTAFAINA BA TA KOWACE SIGA*
*TARTSATSI.*
*RUWA DA. KANKARA.*
*DIJE K'ARANGIYA*
*NI HADIZA D/AUTA BAN LAMUNTA BA AKAN KOWA DA YA SAKE SARRAFA MANI LITTAFAINA BA TA KO WACE HANYA DA KO WANE YANAYI BA TARE DA IZININA BA AKASIN HAKAN KUWA WALLAHIL'AZIM ZAMU GAURAYA DA KOMA WACEE DON SAI NA JA HAKKINA AKAN KOMA WA YE A BI DOKA A ZAUNA LAFIYA🤝🏻*
BAN AMINTA BA!
BAN AMINTA BA!
KAR A SAKE!
KAR A SAKE!*Lamba ta 25*
DIJE kam duk Wanda ta sani sai ta tashi tsaye ta fito da kanta tana d'agawa mutane hannu, tun Safwan yana jin takaicin abun a ranshi har sai da ya kai ya katsa mata wata arniyar tsawa yace
"Wai ke wace irin bak'auya ce ke? Wannan abu da kike yi tamkar wata zararra fa?"
Dije kam bata daina gaisawa da mutanen k'auyensu ba, cike da jin haushin abin ya ciyo kugunta ya janyo zanenta da k'arfi ta dawo dab'as ta zauna, kanta ya bugu da bayan seat d'in tace
"Wash! ALLAH kaina"
Cikin masifa yace,. ,"Ya dad'e bai cire ba shi kan naki tunda ke ba kya ji WALLAHI ba zan lamunci hakan ba"
Dije ta makure ta sha jinin jikinta tana yi masa hararar gefe tana mui mui, mata biyu yan rakiyar Dijen da suke tare da su cikin motar suka had'a baki wajen fad'in cewa
"Don ALLAH ka yi hak'uri k'urciya ce"
Safwan ya yi banza da su tamkar ma bai ji su ba, ba shiri su ma suka yi gum motar ta yi shiru na d'an lokaci aikuwa cen Dije ta hango wata 'yar Makarantarsu ta Allo ta yi saurin yin wani zillo tamkar biranya ta dale saman seat d'in da kafafunta ta tashi tsaye ta fito da jikinta suka tana fad'in
"Ladidi kin ganni nan cikin mota anyi mani aure birni zan je, me kike so idan zan dawo in kawo maki?"
Ladidin ta washe Baki tace,. "Burodi nike so Dije don ALLAH fa kar ki mance kinji??"
Dije tace, "bazan mance ba Ladidi Sha kuruminki kinji ai kud'i zan yi idan naje, ke karatun Likitancin fa zan yo a cen fa ki ce da Malam Mainasara ya ci gaba da yi man addu'a sai na dawo"
Haka Dije ta yi ta zuba shirmenta da Ladidi har suka daina ganin juna, sannan ta dawo ta zauna tana washe Baki tace
"ALLAH sarki garinmu shikenan zan barka kar ka yi kuka ka ji sai na dawo"
Safwan dai zuciyarshi ta kai wuya ya k'ufula sosai Shiyasa bai biyeta ba don matuk'ar ya kulata ba k'aramar jibga zai yi mata ba, gashi tare yake da Baffah'nta da yan uwanta yasan dole ne sai sunji ba dad'i, shiyasa ya yi kwafa kawai ya yi sannan ya ci gaba da tuk'inshi sannu a hankali har suka shiga babban birnin k'auyen su Dijen, aiko tana hango wani mai shayi da biredi motar tana gudu ta fara yunkurin tsallakewa ta tagar da nufin ta fita, Safwan ya yi nisa da tunani sai gashi ya dawo hankalinshi ba shiri saboda fahimtar abunda take so ta yi, aiko ba shiri ya fisgota ta dawo ciki tare da yin sauri ya zuge glass d'in ya rufe ruf, ta yi saurin kallonshi tace
"Don girman ALLAH ka barni in sha shayi da burodin cen WALLAHI raina ya biya sosai, ka ga yawuna ma har sun tsinke gaba d'aya WALLAHI"
Ta k'are maganar tare da had'iye wasu yawun suka wuce a makoshinta kutt! Safwan ya yi banza da ita, Dije ta tashi ta fara dukan gilas d'in tana fad'in
"Wayyo ALLAH ga wani kifi cen za'a gasa daga ganinshi zai yi dad'i WALLAHI"
Cen kuma ta sake cewa "ji matar cen tana soya kosai gaskiya daga ji zai yi dad'i WALLAHI, har da wani Abu gashi cen ina ma zan samu in ci shi inji?"

YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
General FictionLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.