1

358 31 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻*

*Lamba ta 21*

Gaba d'aya jikin kowa na wurin ya yi sanyi sai cen Maigarin ya yi jarumtar fad'in,. "A komi ALLAH Ubangiji yasa hakan shine alkhairin"

Ya yunkura ya mike tsaye yana saka talkaminshi yace da abokan tafiyarshi,. "Ki tashi muje sai mu yi masa bayani idan har ALLAH zai sa ya fahimcemu"

Haka suka bar k'ofar gidan kowa jiki ba kuzari saboda ganin duk girman Maigarin ya zo neman abu wajen Baffah amman ya rufe idonshi ya kasa yi masa wannan alfarma, shi Kam Baffah ko a jikinshi hasali ma hankalinshi kwance ya nad'e tabamar ya shige cikin gida, inda kai tsaye ya kira Usman ya ce ya je ya kira masa Balan Duduwar, sannan ya shige d'aki abunshi Inna ta bishi da kallon mamaki jin aiken da ya yi na neman Bala, cikin sanyin jiki ta bishi d'akin tace

"Malam ALLAH dai yasa lafiya?? Naga Maigari ya zo wajenka kuma ga shi na ji yanzu ka ce a kira Bala"

Baffah ya yi saurin fadada fuskarshi da murmushin yace,. "Abunda kike so ne za'a yi maki tunda na hango hakan shine mafita akan matsalolin da suke son kunno man kai cikin gida"

Inna ta bishi da kallo Baki sake tace,. "Ka yi man bayani yanda Zan gane Malam"

Baffah ya fito d'akin tare da d'auko buta ya fara sabuwar arwallah har ya k'are ba tare da yace kanzil ba, sannan ya mike ya kalleta yace

"Wata mai kamawa Zan yiwa Dije aure da Balan Duduwa tunda har yana sonta"

Inna ta zaro ido waje tace,.  "A'a Malam gaggawa fa aikin shedan ce, ka bari abi komi a hankali kar a zo ayi abu don neman mafita wata sabuwar matsalar ta bullo"

Baffah ya kalli Inna shekeke sannan ya nufi hanyar fita yace,. "Alkhairi muke fata kuma shi zamu gani"

Ya fice ranshi a b'ace Dije da ke k'ofar Inna ta k'araso wajen da Innar take tsaye cikin kokwanto tace,. "INNA naji Baffah yana zancen aurena da Balan Duduwa da gaske yake yi ko wasa???"

Inna ta maka mata wata Uwar harara ta nufi madafi tace,. "Ki jira idan har ya dawo sai ya amsa maki tambayar da bakinshi tunda ai ba Ni kika ji na fad'a ba"

Dije ta ja buta ta yi bayi tana gungunin cewa,.  "Ai na rantse da ALLAH ni Malam Danbirni zan aura cabd'i! Haka kawai in aureshi ya hanani zuwa Makarantar koyon Likitanci hum! lalle ma ko"

**

Baffah Kam tare da Bala da Usman suka yi sallahr Isha sannan suka garzayo gida, Baffah yasa Usman ya shimfida masu tabarma a zauren gidan, sannan yasa aka kawo masa tuwonshi ya yi wa Bala tayi Bala cike da jin nauyin surukuta yace,. "Alhmdllh"

Baffah ya kalli Balan yace,. "Naji labarin cewa kana son Dije ko?"

Bala ya sunne kai cike da jin kunyarshi, Baffah ya ce

"Magana zamu yi mai Muhimmanci saboda auradda ita nike son yi idan har kashirya aurenta to ka fito da karfinka Ni zan aura maka Dije duk lokacin da ka shirya"

Cike da tsananin farin ciki yace

"Na gode Baffah" Balan kam bakinshi ya kasa rufuwa saboda tsabar murnar ganin nesa ta zo masa kusa, cikin jin nauyi ya nunawa Baffah amincewarshi tare da godiya akan wannan karamci da ya yi masa, sannan ya yi masa alk'awalin zai turo iyayenshi kurkusa ayi komi a gama cikin kankanin lokaci.

Haka suka rabu zuciyarshi cike da farin ciki uwa uba ma da Baffah'n ya bashi damar ya fara zuwa zance wajen Dijen don su fahimci juna kafin lokacin auren ya zo.

Baffah kam bai shigo Gida ba har sai da ya tabbatar Dije ta yi bacci don ba ya son ta janyo abunda zai sa ya jibgeta a banza, don tunda ya dawo masallacin ya ga yanda ta makure jikin gini tana sharar hawaye yasan akwai magana, don baya raba d'aya biyu yasan taji zancen aurenta Balan shiyasa, sai dai a mamakinshi ko da ya shiga cikin Gidan ya taradda ita idonta biyu jikin ginin har lokacin tana gyangyadi, jin shigowarshi yasa ta yi saurin mik'ewa ta nufoshi tana fad'in

"WALLAHI Ni Baffah ban son Bala ba zan aureshi ba"

Baffahn ya yi mata wani kallo yace,. "Baki sonshi wa kike so??"

Dije ta yi saurin kamo gefen dankwalinta tana wasa dashi tace,. "Ni Baffah ba wanda nike so WALLAHI Ni gurina kawai inje Makarantar gaba in zama likita"

Baffah ya zaro Ido waje yace,. "Au shirmen ya kitsa maki kenan ko? To ai kwanan nan zanyi maganin abun, ai WALLAHI ko bani so dole ne in auradda ke cikin gaggawa tun kafin su kaini ga maganar banza"

Yana kare maganar ya shige d'akinshi zuciyarshi cike da jin tsoron sharrin wad'annan bak'in Yan bokon ga Yar guda gudar yarshi Dije, wadda ko kuda baya so ya tab'a masa ita matuk'ar yana da ikon hakan.

Dije kam ranar kwana ta yi tana sharbar hawayenta saboda sam sam ita bata son auren kacakam ballantana auren Balan, idan son damunta ne ace ta yi karatu mai zurfi ta zamo abar alfakhari cikin kauyensu, amman ina kash tasan gurint sam bazai tab'a cika ba muddin ta auri Bala, don dama ace Lawi ne da zata sakawa ranta cewa gurinta zai cika komi daren dad'ewa.

Ko da Safiya ta waye da d'ar d'ar ta shirya don ta zaci Baffah'n ya hanata zuwa Makaranta, amman sai gashi bai hanata ba  har da yi mata ALLAH ya kiyaye, saboda yasan Shirin da yake yi akan auradda ita d'in cikin kankanin lokaci.

Dije sukuku ta zo Makarantar Lawi ya so ya yi mata magana amman tuno irin gargadin da Maigarin ya yi masa akanta yasa ya yi k'ok'arin kawar da kanshi gareta, don ko da aka tashi ma sai da kowa ya watse Makarantar sannan shi ya nufo masaukinsu, don gaba d'aya ma shi zaman garin ya gundureshi jin yake yi kamar a saman kaya yake, Alla Alla yake yi su kammala service dinsu su bar Garin, don akan hakan ma har abokin nashi ma sun fara zaman doya da manja dashi, gashi shi ma Maigarin yace ya zame hannunshi idan shi zai iya ga fili ga mai doki.

**

Cikin wata d'aya aka kammala neman auren Bala da Dije inda aka kawo komi na auren Rana kawai ake jira ta zo a sha shagali, izuwa lokacin Dije ta saduda dolenta saboda ba tirjiyar da bata yi ba akan auren amman Baffah'n kam ya kafe ba gudu ba ja da baya, don ita kanta Innar ganin akan auren Dije zasu samu matsala da Baffah'n shiyasa ta zubar da makamanta ta fara shirye shiryen auren Dijenta.

Ana saura sati d'aya bikin Dije suka zana jarabawar kammala primary, kowa sai murna yake yi inda shi Kuma Lawi yake cike da bak'in cikin rasa Dijen da yayi, Safwan kam ko kad'an bazaka gano yanayin da yake ciki ba, asali ma shi hankalinshi kwance yake ta d'aukar photuna da su Dije da sauran yaran Makarantar, Dijen ma ba wata walwala akan fuskarta don kuwa a kallo d'aya zaka gano sauyawar da ta yi, don kuwa gaba d'aya ra zabge sai Ido da karan hanci don izuwa lokacin har wata natsuwar dole ta ziyartota, duk nacin da Lawi ya yi akan yana so ya yi sallama da Dije bai sami wannan damar ba, saboda ganin yanda Safwan ya keta hidimar d'aukar pic's d'inshi da su Dijen.

Sai da aka gama ne ya samu ya yi wa Dije sallama tare da mika mata wata envelope idonshi jawur tamkar ya yi kuka, don shi ya kuduri aniyar ba zai jira ayi auren Dijen da shi ba, da nufin tun da sassafe ya had'a inashi inashi ya bar garin, don shi Safwan ya ce ba ranar zai tafi ba ya yi gaba shi zai biyoshi ta baya.

Dije tana kuka suka yi sallama da Lawi ta tura envelope d'in da ya bata a jaka ta nufi gida,. Kai tsaye ta shige toilet ta bud'a envelope d'in saboda ta matsu taga me ke ciki gashi  bata son Inna ta gani.

Aiko sai gashi tana budawa taga wasu Yan hannu da zobe masu bala'in kyau sannan da bandur d'in kud'i sababbi kal yan d'ari bibbiyu, Dije ta zaro ido tare da goge hawayenta cikin sauri ta rungume kud'in da sauran kayan ta fashe da kuka gwanin ban tausayi, sai dai ita bata san duk abunda take yi Inna tana hankalce da ita, shiyasa lokacin da taga ta dad'e bayin ta biyo sawunta sai ko gashi ta ganta durk'ushe kasan bayin tana ta kuka, cikin tausayawa ta isa wurinta ta tadata Dije ta yi saurin yunkurin b'oye kud'in sai ga takardar kud'in ta yage kud'in sun zubo shaaaa! A k'asa.

Ku yi hakuri da kuskuren da kuka gani yau ban yi editing ba🤦🏻‍♀️

Akafta😉





D/AUTA CE✍🏻

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now