50

396 29 0
                                        

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*DOMIN JIN DAƊINKU MASOYANA ku natsu tsaf ku ci gaba da kwasar ganima😂😝*

*Lamba ta 50*

Safwan kam firgicin da yake ciki ne yasa ya baje ƙasa cikin kiɗimewa yana ta sambatun kiran sunan Dijen, tare da faɗin

"Ina kika shiga ne don ALLAH ki dawo wallahi ina sonki ke ma kinsani ai"

Har dare ya raba yana ta abu ɗaya zuwa lokacin mutane sun fara taruwa kanshi ana tambayarshi mafari, da dai ya fahimci ya tarawa kanshi ƴan kallo ne ya tashi ya faɗa Motarshi ya nufi gidansu wani ɗan uwansu kuma abokinshi, cike da tsantsar tashin hankali yake yi masa bayanin duk  abunda yake faruwa, Abokin nashi ya jinjina abun a ranshi sannan ya ce

"A gaskiya Abokina ka yi kuskure babba yanzu mafita ɗaya ce ka je ka baiwa Hajiyar Haƙuri kafin ka kama hanyar zuwa garinsu yarinyar, saboda jikina yana bani ta yi gida don ta gaji da abunda kake yi mata ne shiyasa ta gudu" 

Sannan Safwan ya tuno da wayarshi ya ɗaukota da nufin kiran Hajiyar sai ga kiran Lawi da Kamal ya fi ashirin a wayar, cikin sauri ya kira Lawin da rawar baki yake faɗin

"An ganta?"

Lawi murya mai cike da damuwa yace "WALLAHi ba'a ganta ba ni na fara zargin ko ta yi garinsu"

Safwan ya dafe kanshi cikin wani sabon firgici yace,. "Don Allah Abokina ka roƙar mani Hajiya in dawo gidan in bata haƙuri WALLAHi gobe tun da sassafe zan kama hanyar garinsu Khadija in dawo da ita"

Lawi yace "kayi haƙuri Abokina WALLAHi Hajiya ta shiga damuwa sosai akan ɓatan khadija yanzu haka ma da ƙyar na lallasheta ta daina kuka, ga gidan gaba ɗaya hankalinsu ya tashi madadin farin ciki gida ya koma na jimami"

Safwan a kiɗime ya kashe wayar tare da furta "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un Allahumma la sahla illa maja'altahu sahla, ALLAH ka tsare yarinyar nan a duk inda take, Ubangiji ka bani ƙarfin gwiwar tunkarar wannan mummunar ƙaddara da ta faɗowa rayuwata"

Ya kalli Abokin nashi da jajayen idanuwanshi yace, "bari inje Mubarak banga ta zama ba tunda har nine na janyo komi"

Mubarak cike da tausayinshi yace, "ba dai yanzu kake nufin zaka bi bayanta ba?"

A zafafe ya faɗa motarshi yana faɗin "banga ta zama ba ai kuma matuƙar ba ganin yarinyar nan nayi ba....."

Kiran wayarshi ne ya katse maganar da yake yi cikin sauri ya ɗaga saboda ganin numbar Hajiyarshi ce, kafin ma yayi magana yaji muryarta cikin muryar kuka tace

"WALLAHi matuƙar baka dawo man da yarinyata ba to kada ka kuskura ka tako ƙafarka cikin gidan nan"

Cikin rawar murya yace, "ki bini da addu'ar tsari kawai Hajiyata, nayi maki alkƙawali bazaki ganni ba sai tare da Khadija insha ALLAHu"

Kittt! Hajiyar ta kashe wayar saboda wani kukan tausayin kansu da ya kamata, Surayya dake ta bata haƙuri ta yi saurin faɗin

"Don girman ALLAH Hajiyarmu ki yi haƙuri Insha ALLAHu ba abunda zai sami Khadijah ALLAH zai kareta a duk inda take"

Hajiya ta miƙe ta nufi toilet Surayya da Fiddo da yayyensu biyu mata da wasu ƴanuwasu da ke ɗakin suka bita da kallon tausayi, saboda yanda ta ɗaga hankalinta sosai akan rashin ganin Dijen, kowa sai faɗin albarkacin bakinshi yake yi akan lamarin.

Wannan shine abunda ya faru kafin Hajiya ta kira garinsu Dijen ta ji labarin cewa tana cen, don ko shi Safwan ɗin yana kan hanyarshi ne ya sami labarin cewa tana garinsu a bakin Surayya, saboda ƙoƙarinta na son rage masa damuwar da yake ciki.

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now