Ouip*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻*
*Lamba ta 8*
Mune ganin yayanta yana kuwwa yasa ta sake zundumawa da gudu ta yi gida da nufin taje ta fadowa Innarsu, Dije kam karbar Allonta ta yi ta kalli su Hansai tace
"Ku muje in kuma anan zaku tsaya sai in tafiyata"
Yayan Mune sai tsine mata yake yi Dije ta waigo tace,. "Ni bani da lokacinka tunda ALLAH ya saka man akanka, saura kuma idan ka tashi fad'i kace nice na ji maka ciyon a hannu"
Yanata surfa mata zagi tana masa dariya taja kawayenta suka tafi suka barshi anan, kowa idan aka kai gidansu ya shige masu ratsewa su yi hanyar da zata sadasu gidajensu kuma su ratse su tafi, suka bar Dije ita kad'ai tana tafe tana Yar wakarta zuciyarta cike da jin dad'in abunda ta yiwa Tambari, aiko sai gashi ta had'u da Bala wanda tun daga nesa da ya hangota fuskarshi a washe ya k'araso idonshi akanta yace,.
"A'ah su Dije Makaranta aka fito ne??"
Ta Kai kallonta gareshi ta bata fuska tace,. "Eh cen na fito"
Tana maganar tana ci gaba da tafiya abunta, Bala ya biyota a baya yace,. "Dije ki tsaya akwai maganar da nike son muyi Ni da ke"
Dije ta waigo ta rik'e kugunta tana yi masa wani kallon reni tace,. "Magana kuma? Bayan wadda muke yi da Kai yanzu?"
Ya gyara tsayuwarshi yana fesheta da wani arnen murmushi yace,. "Wannan ta musamman ce ai don WALLAHI na dad'e da abun cikin Raina sai dai tsoro yasa na yi ta b'oye abuta a cikin zuciyata"
Dije tana yi masa kallon Ido cikin Ido tace,. "Toh kace abun babba ne Bala? ALLAH yasa dai ba cewa za'a yi nayi wani abun ba kuma?"
Bala ya yi saurin fad'in,. "Ba kiyi komi ba na aibi Dije illah ni da kika sakani shiga damuwa da zullumi kullum safiya"
Dije cikin k'ulle kai da rashin gano inda zantukan Bala Suka nufa tace,. "To ai sai ka fad'a Kai tsaye basai ka tsaya zagaye zagaye ba"
Bala ya kafeta da kallo cikin tsananin kaunarta da ta cika masa zuciya yace,. "WALLAHI Dije sonki dai Nikeyi tun da dad'ewa, ammman na kasa furta maki ina jin tsoro"
Dije ta yi saurin dafe k'irji tace,. "Yanzu Kai Bala duk mutuncin da nake ganinka dashi ashe daman cen dan iska ne Kai ban sani ba??"
Balan ya zaro Ido waje yace,. "Iskanci kamar yaya Dije don nace Ina sonki shine nayi iskancin??"
Dije ta maka masa wata jar harara tace,. "Yo in ba iskanci ba me ya kawo zancen kana Sona? Ko ka d'auka Ni Yar iska ce kamar kai to WALLAHI wurin Duduwa zan kaika in sanar da ita don ta ja maka kunne tun kafin ka janyo Baffahna ya kasheni a garin nan"
Aiko ta juya ta nufi gidansu Bala, Bala ya bita yana magiya akan kar ta Fado ta rufa masa asiri ba zai sake yi mata maganar ba, amman Dije ta Kai wuya shiyasa bata fasa nufar gidan ba cikin fushi kamar wata zakanya, aiko tana shiga ta fara kwallawa Duduwa kira waton Kakar Bala ta wajen Uba da bayan rasuwar Mahaifiyarshi ya dawo hannunta.
Sai ko ga Duduwa ta fito d'aki tana gyara daurin zanenta tace, "lafiya kike kirana? injin dai ba bashinki naci ba?"
Dije ta k'araso ta kantare k'ugu tana wani cije Baki tana murgudashi tace,. "Aiko dole ki ganni tunda har Bala yake so ya maidani Yar iska kamarshi"
Tsohuwa Duduwa ta zaro Ido waje tace, "ke dakata Dije ki fita idona in rufe kada ki kuskura ki yiwa Balana sharri"
Dije ta yi mata wani kallo ta waiga bayanta inda Balan yake shigowa Gidan tace,. "Ai gashinan ki tambayeshi in har zai fadi tsakaninshi da ALLAH me ya fad'a mani yanzu?"

YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
Ficción GeneralLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.