58

332 22 6
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Mutanen Dije ina baku haƙuri🙏🏻dangane da auren Zee da Safwan ya yi, amman ina son ku sani ana yin book ne don faɗakarwa tare da wa'azantarwa sannan da kwatanta abunda ke faruwa a cikin al'ummarmu, saboda haka ku natsu tsaf ku bini sannu a hankali zan warware maku komi cikin tsarinshi😉*

*Lamba ta 58*

Har ƙuryar ɗakin Hajiya Mama aka kai Zee da ke ta rufe fuska tana ta wasar baki saboda daɗin da ya kasa ɓoyuwa a kan fuskarta, gaban kowa da mutanen da suka yi mata rakiya Hajiya Mama ta ce da Zee

"ALLAH ya baku haƙurin zama,
kuma albarkaci aurenku tare da zuri'a ɗayyaba gaba ɗaya, sannan da fatar zaman lafiya ke da abokiyar zamanki"

Dirim! dum! Shine bugun da zuciyar da Zee ta yi amman ta wayance tare da noƙe fuskarta tace "Ameen" Hajiya Mama ta ƙara da cewa

"Ki yi haƙuri nasan zaki ga abokiyar zamanki bata sami halarta bikin ba, to hakan ya faru ne a sanadin hidimar karatun da ya sha kanta, amman ina fatar a duk lokacin da zama ya haɗaku ki yi ƙoƙari ki baiwa Mijinki haɗin kai wajen yi maku adalci a tsakaninku, ALLAH ya baku zaman lafiya a tsakaninku duka ya kawar da sheɗan cikin  gidanku gaba ɗaya"

Kowa sai "Ameen Ameen" yake faɗa sannan ta kawo dunƙulalliyar kyauta ta bata, aka fito da Zee mutane da yawa sai yaba kirkin Hajiyar yake yi, inda kai tsaye aka wuce da Zee katafaren gidan Safwan wanda ya laƙume maƙudan kuɗi wajen haɗashi ta ko'ina, inda itama kanta Zee iyayenta suka zuba ta su bajintar wajen ƙawatashi da kayan ƙarau lungu da saƙo, abun dai masha ALLAH sai wanda ya gani don tsayawa misalta haɗuwarshi ma ɓata baki ne, saboda haka masu karatu na baku wannan aikin wajen misalta gidan da kanku.

Har ɗakinta aka kaita iyaye da ƴan uwa da ƙawayenta sai addu'ar zaman lafiya su ke yi mata, saboda ganin yanda ta haye wajen samun kyakkyawan Miji da kyakkyawan muhallinta gwani burgewa, uwa uba itama gata  kyakkyawar farar mace kuma ga su da hannu da shuni ta ko'ina suka motsa  nera kukan wahala ta ke yi, saboda akwai kuma an tara babu abunda zai gagaresu nema matuƙar da kuɗi ake sakawa a nemi abun.

Abokan Safwan sun shirya dinner wadda za'a yi a wani katafaren hall, sai dai shi ango ya ce sam shi kam ba wata dinner da zai je, shagugulan da aka yi ma sun wadatar ALLAH ya sawa aure albarka, ba magiyar da Zee ba ta yi masa ba akan ya yi haƙuri su je ko da rage lokacin da aka ɗiba ne za'a yi sai ayi komi cikin lokuta ƙalilan, amman ya buga kanshi a ƙasa ya ce shi bai san da wannan zance ba, cike da jin haushi Zee ta fashe masa da kuka dole ya koma aikin lallashinta, ganin yanda ta dami kanta akan son zuwan ne ya shirya suka je, amman har cikin zuciyarshi ba ya wani murna da duk wani shagali,  aure dai ne anyi to tsirfin na mi ne kuma?.

Har aka yi dinner aka watse Safwan fuskarshi ba yabo ba fallasa sai dariyar yaƙe da yake yi wa mutane, Amarya da ango sun fito sun yi rawa sun sha liƙi ta ko'ina kuɗi ne ake zuba masu, bayan sun ƙare ne suka yanka cake tare da ciyar da junansu mutane sai ɗaukarsu photuna da videos ake yi, saboda  shagalin ya ƙayatar da rai sosai ba tare da jan lokaci ba aka watse koma ya kama gabanshi, inda Ango ya ɗauko Amaryarshi zuwa gida tare da rakiyar abokai da ƙawayen Zee ɗin da za su kwana da safe su kama gabansu.

Kasancewar part ɗinshi daban shiyasa kai tsaye ya nufi sashenshi ya barta tare da zugar ƙawayenta suka nufi sashenta, cike da tsananin gajiya ya faɗa kan gadonshi tare da dafe kanshi idonshi a sama yana kallon seilling yana hasko Dijen Baffah cikin idanuwanshi, musamman lokacin da ya sami sa'ar rabata da abunda har lokacin idan ya tuna sai ya ji shi cikin wani yanayin buƙatuwa da son komawa cikin tafkinta mai ɓulɓulo da ruwan kogin ni'ima, waɗanda ko a misali ba zai taɓa kwatanta irin abunda ya ji a jikinta ba, don duk abunda zai faɗa ganin yake yi kamar ya fi hakan, saboda shi kanshi ya yi matuƙar mamakin yarinya kamarta ace itace da wannan tarin albarkatun ni'imar a jikinta, sai dai idan ya yi nazarin cewa ance ko wace mace da kalar ni'imarta sai ya ajiye mamakin don yasan ALLAHn da ya raba ya baiwa kowa ce mace haka itama ya raba ya bata tata, don ikon ALLAH ya fi gaban a yi mamakinshi illah kawai mu ce Alhmdllh a kowane hali a kuma kowane yanayi.

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now