57

328 25 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*


*Because of you ƙanwata Leemart pinkey MHiss purple ALLAHU ya bar zumunci ta hannun damata🖐🏻*

*Lamba ta 57*

Jiki ba kuzari yake driving har ya isa Yola cikin amincin ALLAH, sai dai yawan faɗuwar da gabanshi yake yi yasa ya ji baya sha'awar zuwa gida, sai da ya biya wajen Mubarak suka tattauna sosai akan matsalar sannan ya nufo gidan.

Jiki a sanyaye ya yi parking ya daɗe zaune cikin motar yana nazarin ta ina zai fara?, wurin Hajiya Mama ko wurin Khadijarshi?, a ƙarshe dai ya yanke shawarar fara tunkarar Hajiyar saboda ta fi khadija matsala a wurinshi, don ita da ya kanainayeta da daɗin baki zata bi ba tare da yasha wahala ba, cikin ƙarfin gwiwar da zuciyarshi take ba shi ne ya fito ya nufi cikin gidan, sai ko ya taki sa'a ya taradda Hajiyar da Fiddo a babban falo suna kallo, ya shigo da sallamarshi ya ƙaraso ya zauna tare da faɗin

"Wash! ALLAH Hajiyarmu gani na dawo lafiya"

Idonta akan tv tace "masha Allah sannu da dawowa"

Fiddo ta gayar da shi cikin ladabi sannan ta ce, ,"big bros ya jikin Aunty Zee ɗin? da fatar taji sauƙi sosai?"

Ya shafo sumar kanshi da take cike da gashi kwance baƙi ƙirin a saman kan nashi, sannan ya ce

"Ta sami lafiya khadija fa?"

Fiddo ta yi saurin kallon Hajiya Mama sannan ta ce  "Tana ɗaki maybe bacci take yi"

Cikin jin nauyin idon Hajiyar ya ce "je ki ce ta kawo man abinci"

Fiddo ta daburce ta miƙe tana sosa kai tace "tun ɗazu fa kamar bata gidan nan don ban ga ko wulgawarta ba"

Cikin faɗuwar gaba ya zaro ido waje "me kike nufin sanar da ni? Ba ta nan to ina ta je ne ba tare da izinina ba??, Hajiyarmu ko ke kika aiketa ne don nasan Khadija ko ƙawa bata da a cikin garin nan bale ace ta je cen, ko dai tana gidan Surayya ne?"

Hajiya Mama cikin ko in kula ta ce,  "mi ye damuwarka da ita ne? Ni fa bana son takura, saboda haka ka bar yarinya ta sha iska"

Safwan ya marairece fuska yace , "matata ce fa Hajiya ko ba komi akwai haƙƙin aurena a kanta"

Hajiya ta maka masa harara ta ce  "don kana aurenta ai har yanzu bata zama kamar sauran matan aure ba, don cikin haƙƙoƙanta da Allah ya rataya a wuyanka nawa ka sauke faɗa man cinka? ko shanka? Ko kuma suturarka?, To bana son zaƙewa da yawa don ni nake da ikonta tunda kai da kanka ka saka muna ita cikin ƴan aikinmu, to yanzu kuma ka ke son zuwa ka kawo mani wani zancen banza cen"

Safwan ya yi saurin faɗin "to na tuba a gafarceni Hajiya yanzu ina ta je in je in ɗaukota",

Cikin basarwa Hajiyar ta ce  "to Khadija dai bata gidan nan na turata aikatau wani gari, saboda naga mu nan ƴan aikin ma sun yi muna yawa, shine na ga da a barta haka kawai zaune ba wani moruwarta da muke yi, shine na ga gara kawai na turata cen ɗin, insha ALLAHu duk kuɗinta na wata wata idan an aiko mani zan je da kaina har ƙauyensu in kai wa iyayenta"

Firgici tashin hankali tare da ruɗewa duka suka ziyarto wa Safwan ba tare da ya shiryawa zuwansu ba, cike da wani tsantsar tsagwaron tashin hankalin da ya bayyana a kan fuskarshi ya ce

"WALLAHI ina sonta Hajiya don ALLAH ki dawo man da matata hannuna, na yi maki alk'awali zan riƙeta in mata gata fiye da kowace mace mai gata a gidan Mijinta"

Ya ƙare maganar cikin muryar kuka tare da zuwa gaban Hajiyar ya durƙusa gwiwa bibbiyu ya haɗa hannu biyu waje ɗaya alamun roƙo ya sake cewa

"Na tuba Hajiyarmu ki yafe mani WALLAHIL'AZIM yanzu da gaske ina sonta, kuma a shirye nike da in zauna da ita a inuwa ɗaya a matsayin matar aurena"

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now