44

347 27 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*SPECIAL THANKS FOR YOU MY OMEESHER, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKI HAR GADON BACCINKI, HAƘIƘA MARYAM OMEE KE ƊIN TA DABAN CE A WURINA,KI SANI INA YINKI HAR ABADAN ABADE, ALLAH YA BAR ZUMUNCINMU HAR ALJANNAH, ALLAH YA KAREKI DA SHARRIN MUTUM DA NA ALJAN DA DUK WANI ABU MAI CUTARWA A DORON DUNIYA, UBANGIJI YA ƘARA DAFA LAMURRANKI YA ƘARA KAWO MAKI HASKE CIKIN RAYUWARKI, TABBAS NI DA KE AKWAI ƘAUNA IRINTA FISABILILLAH.*



*Lamba ta 44*

Cike da jin daɗi Dije ta koma ɗakinsu ta wanke fuskarta sama sama a gurguje, saboda kwalliyar da aka yi mata tana nan raɗam, ƙara gyarata kawai ta yi tare da sassaita ɗaurin ɗankwalin sai gata ta fito shar! da ita masha ALLAH, idonta kawai zaka kalla ka gano kukan da ta sha saboda jan da suka yi, amman a hakan ma ta fito ɗagwas ɗagwas abunta, ta ƙara feshe jikinta da turaruka ta ɗauki jakarta ta fito falo, zamanta bai kai na minti huɗu ba sai ga sallamarshi ya shigo yana wani ɓata fuska yana cin magani, ba tare da ya ma kalli inda take ba ya nufi ɗakin Hajiya Mama, daga nan inda take tana jiyo shi yana faɗin

"Don Allah Hajiyarmu ki bar yarinyar nan renani take so ta yi fa, kuma ke kin zo kina goya mata baya  ta je ta yi abunda bai dace acen, ki barni da ita don ALLAH ɗazu fa a gaban kowa ta nuna cewa ita bata da aure to a hakan za'a dinga barinta tana shiga ko'ina duk inda taso?"

Hajiya Mama ta maka masa wata jar harara tace, "to Ina ruwanka don tace bata da aure? Auren ne da ita to? ka ga Safwan kar fa ka nemi takura man yarinya, ka barta ta yi abunda take so don kai ma an barka ka je ka yi abunda kake so ko?, To itama tana da ƴanci abarta ta sakata ta wala tunda kai baka so ALLAH zai bata rabonta a gaba, kuma umurni na baka ka ɗauketa yanzu ka je ka kaita cikin ƴan uwanta"

Tana ƙare faɗar haka ta koma ɗaki abunta ta barshi a tsaye zuciyarshi kamar ta tarwatse saboda baƙin cikin da kalaman Hajiya suka sakashi, ya fito fuu yayi waje Dije ta bishi da kallo ganin bai ce da ita ta taso ba yasa ta ƙi binshi, amman sai ga ƙarar tada Motarshi tare da uban horn da ta ji ya fara bugawa iya karfinshi wani bayan wani, cikin sauri ta miƙe ta fito ba tare da ma ta damu da yawan horn ɗin ba ta fara tafiyarta a yangace tana wani basarwa itama fuskarta a haɗe,  cike da masifar jin haushinta ya yo kanta da motar kamar zai kaɗeta, amman kasancewar itama zuciyarta a wuya take ko ɗar bata ji ba, asalima tsaye ta yi tana kallon gefe tare da riƙe ƙugu tana girgizar ƙafa, a zuciye ya fito cikin masifa ya ɗaga hannu da nufin sharara mata mari, kallon da ta yi masa yasa ya yi saurin dunƙule hannunshi, sai dai ya yi jarumtar nunata da yatsa yace

"Don kin ga Hajiya tana ɗauke maki shine zaki kawo man ƙananan iskanci ko?, To WALLAHi da kin cikani ɗaukarki zan yi in mayar da ke garinku, don ni aure zanyi bazan juri zama gwauro ba akanki baƙar baƙauyiyar banza, wawuya kawai wadda bata san darajar aure ba in banda ƙaddara ma ni me zai sa in rasa matar da zan aura sai ke?"

Ya nunata a wulaƙance sama da ƙasa sannan ya buga wani uban tsaki ya juya ya shige motarshi tare da rufo ƙofar da ƙarfin bala'i, ganin ko motsi ta kasa yi illa kallonshi da take yi fuskarta a haɗe tana wassafa irin abunda zata yi masa ta huce, yasa ya leƙo da kanshi yace

"WALLAHI idan baki zo ba tafiyata zan yi sai dai aga laifina"

Dije ta yi masa wani mugun kallo sannan ta tako ta buɗe bayan motar ta zauna itama ta jawo Kofar da ƙarfi har sai da tayi ƙara tace garam!, Ba shiri ya waigo baya yace

"Uban wa kika ajiye ya zamo direbanki?"

Ta yi banza da shi ya sake maimaita maganar nan ma ta sake yin banza da shi illa gefe da take kallo tana wani cin magani, aiko a zafafe ya fito ya buɗe murfin ya fisgota iya karfinshi sai gata da faɗowa jikinshi, ba kunya ya saka hannu ya rungumota gaba ɗaya tsantsan don ya kasa controlling ɗin kanshi, cikin zafin nama ta tureshi tare da nunashi da hannu tace

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now