1

347 30 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Duniya Rawar ƴanmata na gaba sai ya yo baya zamani adon tafiya ne baya ɓoye baiwata aha💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*

*Sonki a jinin jikina yake my Hannah ina yinki sosai har cikin ɓargona alkhairin ALLAH ya kai maki har gadon baccinki my besty💋*

*Lamba ta 35*

Cikin zafin nama ta kaiwa Dije wani bahagon mari, Dije ta dafe gefen fuskar tare buɗe baki tana faɗin

"Laaa! Laaa! Laaa! Mu kika mara? Ashe ko yau zamu yi luguden dafuwar kanki a kogin burunduƙusuru zunbukur, ayyihuhu kibiyarmu zama daram iso ta hannun damana"

Ta ɗaga hannunta sama kanta ƙasa tana wani surutai kafin kace me sai ga Dije ta yi tsalle ta ɗale prefect d'in tare da cafko gashin kanta da ƙarfi cikin ikon Allah sai ga tsoron prefect ɗaya a hannun Dijen ta raboshi daga cikin ƴan'uwanshi ta jefar, ta sake komawa ta cafko fuskarta iya ƙarfinta ta fara yakuceta ta ko'ina cikin wasu irin surutai da ita kaɗai tasan ma'anarsu, cikin ƙanƙanin lokaci sai ga jini ya  fara saukowa tun daga cikin kan prefect d'in yana gangarowa zuwa jikinta, saboda tsoro ɗaya da Dije ta cire mata aiko jini ta ko'ina sai zubowa yakeyi, azabar hakan tasa prefect ɗin ƙwacewa ta arce da gudun bala'i tana faɗin a taimaketa  saboda ganin ya firgitata gashi bai daina saukowa ba, Dijen ma haka bata daina biyarta ba aguje  itama tana faɗin

"Ai billahillazi yau sai mun kasheki dole ne ma sai mun sha romon kanki a cikin daren yau"

Prefect kam tana gudun ceton rai tana faɗin,.  "Ku rabani da ita tun kafin takasheni jini jini  ku taimakeni zata kasheni"

Mutane kam kowa ya hango Dije sai ya dare shi ma ya nemi maɓoya saboda ganin abunda ta yiwa Prefect ɗin wanda a duba ɗaya za'a ce aikin baƙaƙen aljanu ne, duba  da yanda Dijen take ƴar firit da ita amman ta ci galabar Prefect ɗin da take ƙatotuwa.

Aiko saboda ganin kowa yaƙi yarda ya tunkari Dijen a riƙeta yasa Prefect ta ƙara ƙarfin gudunta ta nufi bakin Gate wurin Baba maigadin Hostel ɗinsu, tana kaiwa ta yi Bayan maigadin tana kururuwar ya taimaketa, Dijen ma itama tana isa ta yi wata irin arniyar ƙara cikin ƙaraji tace

"Murkutus riƙe muna ita a cire shegen kan nan!!!!"

Tayi cikin Baba maigadin da nufin ta cafkota aiko ba shiri Prefect ta some saboda tsananin tsabar tsoron da taji, Maigadin cike da jin haushi ya cira wata ƙatuwar bulalarshi ta doki ya sakarwa Dije har sau biyu,  Dije jin azabar saukar bulalar yasa  itama ta yi wani tsalle ta faɗi ƙasa tana surutan faɗin

"Ku tafi da ruhinta ga mu nan zuwa ku je ku je  fa yanzu a fara dafuwar tarugu da tattasai duka a saka kar a saka gishiri a saka sugar ihu wayyo ALLAHna WALLAHI sai mun kashe duk wanda ya sake taɓa muna goɗiya"

Tana ƙare faɗar haka ta yi ɗif sai yawu take fitowa a bakinta tana furzarwa suna sauka kan fuskarta tana gurnani, ganin haka yasa wasu Prefect suka nufi ƴar'uwarsu suna zuba mata ruwa ta farfaɗo  amman duk da hakan jinin da ke fita cikin kanta yasa ya sake bugeta ta tafi luuuu suka rirriƙeta suna kiran sunanta, inda wasu kuma suka nufi Dijen anata ƙoƙarin talallabarta tana ihu tana botsarewa.

Kai tsaye wasu da yawa suma aljanunsu suka fara tashi kafin ka ce me Makarantar ta hautsine da tashe tashen aljanu, sai yarinya tana tsaye sai dai aga ta heta kuwwa ta faɗi ƙasa tana sambatu aiko makaranta ta rikice ko ta ina sai ihu ake yi.

Ana cikin hakan sai ga  wani Malami da vice principal sun shigo bakin Gate ɗin Hostel ɗinsu saboda labari yaje garesu cewa makarantar ba lafiya, sai ko gashi sun taradda abunda ya firgitasu agurguje aka ɗauki Prefect ɗin mai suna Rukayya aka nufi clinic da ita don har lokacin cikin mayen bugun jinin take sai mashalo take yi, Dije kam malamin yasa aka kawo masa ruwa a kofi yayi mata addu'a ya tofa mata  ta yi firgigit ta miƙe kamar wata mahaukaciya sabon kamu tana waige waigen faɗin

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now