5

595 50 3
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*


*COMMENTERS INA MAKU JINJINAR BAN GIRMA🤣👍🏻*


*Lamba ta 5*


Bintalo tana shafo goshinta ta ga jini ta fad'i k'asa tana kururuwa, gaba d'aya mutanen da ke wurin hankali a tashe suka fara salati, a cikin matasan 'yanmatan da ke wurin wata ta zo da gudu ta cire dankwalin Bintalon ta d'aure mata goshin jabau! Bintalo Kam sai ihu take wasu suka rikata zuwa gidansu.

DIJE kam ganin an bar gugunan d'ibar ruwa an nufi wajen Bintalo ana sallallami yasa ta cika bokitinta dam! Ta d'ora akai har ta fara tafiya, hankalin mutanen da ke wajen  ya dawo kanta aiko wasu da yawa suka fara jifarta da miyagun kalamai suna aibatata, ita kam ko juyowa bata yi ba ta ci gaba da tafiyarta don ita kanta ganin jinin da ke fita a goshin Bintalon ya tsoratata, sai dai ta mazge kawai don kada a gano taji tsoro ace za'a ci zarafinta a banza.

Ko da ta shigo gidan da sanyin jiki ta juye ruwan ta ajiye bokitin zata shige d'aki, Inna Hasiya ta bita da kallo tace

"Ke lafiyarki na ganki wata sukuku haka? Ko karyar ciyon ne ya tashi don ba kyason komawa debo ruwan?"

Dije ta zumburo Baki tace,. "Ba Bintalo ba ce ta jani muka yi fad'a, kuma WALLAHI sai da nace ta kyaleni ta kyaleni taki to ai gashi nan yanzu ta janyo goshinta ya fashe jini sai tsiyaya yake yi"

INNA ta zaro Ido waje dafe da kirji tace,. "Goshinta ya fashe ko dai kin fasa mata? Na shiga Ukuna Ni Hasiya wai Dije kasheni kike so kiyi ne? kulluma da sabuwar masifar da zaki jajibo muna kisa mutane su yi ta ganin kamar bama tsawatar maki, to bari kiji WALLAHI Wannan karon sai dai in kasheki za'ayi a kasheki amman Ni Kam ba hannuna ba k'afata tunda ke kunnuwan Kashi ne da ke"

Tana k'are maganar cikin k'unar Rai tayi madafi inda taci gaba da tuka tuwon masararta, tana yi tana fad'a Dije ta shige d'aki sum sum tana matsar kwallah.

Aiko minti biyar a tsakani sai ga tashin muryar Iya Mero Uwar Bintalo, tun daga farkon shigowa Gidan take zazzaga ruwan bala'i har ta shigo Gidan rik'e da hannun Bintalo tare da wasu Yan bani na'iya masu zuwa ganin k'wam.

Iya Mero tana shigowa ta fara fad'in,  

"Ina Hasiya fito kiga abunda tsinanniyar 'yarki ta yiwa Bintalo, WALLAHI Ni Kam bazan tab'a lamunta da rashin mutuncin da take yiwa mutane ba, don in kowa ya kyaleta Ni bazan kyaleta ba Dole ne sai na ramawa Bintalo itama in fasa mata goshin ta ji inda dad'i"

INNA ta fito daga madafi tana sharce majina saboda hayakin da ya turnuke d'akin madafin yasa idonta sunyi jawur,  ta goge fuskarta da gefen zanenta ta k'araso wajen tace

"Don ALLAH Mero kiyi hakuri WALLAHI d'a ne ka haifeshi baka haifi halinshi ba, don da ta Ni Dije take bi to ko hannu aka saka mata a baki bazata ciza ba"

Ta nufo wurin Bintalo ta rik'ota da nufin taga yanayin raunin, aiko Iya Mero ta tureta da k'arfi ta shiga gaban Bintalo tare da cire mayafinta ta sha d'amara a masifance tace

"Ba wani dad'in bakinki da zai yi tasiri a wurina don yau dole ne sai na ramawa Bintalo abunda 'yarki ta yi mata don d'a baifi d'a ba da zaki wani kalallameni da dad'in baki to bazan hak'ura din ba sai na rama mata"

INNA cikin b'acin Rai ta shiga d'aki ta janyo Dije da ke makure Kan gadon bonon Innar suka fito d'akin, Inna janye da ita har sai da ta Kai Dije gaban Iya Meron ta saketa, sannan ta d'auko bokitin karfen ta ajiye gabanta tace,

"Ga ki gata nan Mero don ALLAH ki kasheta kar ki barta da ranta"

Cikin borin kunya Mero ta d'aga hannu ta zabgawa Dije wani Uban mari har sai da ta hantsila, aiko dukawar da Dije zata yi bata taso ba sai da kafafuwan Iya Mero sai gata ko tim! A k'asa tana salati zane ya wancakale gefe, sai fad'in take yi

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now