61

329 26 2
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Ina alfakhari da ku my fans saboda ku ne ƙashin goyon bayan duk wata ɗaukaka da zan samu, ina yinku all a ko'ina kuke kuma a duk inda kuka kasance, tsakanina da ku sai son so fisabilillah😅*

*Lamba ta 61*

Sai da ta ci kukanta ta ƙoshi sannan ta baiwa kanta haƙuri dolenta, don bai dawo gidan ba har sai da ya tabbatar da ta yi bacci sannan ya shigo, saboda baya son haɗa ido da ita akan nauyin dukan da ta janyo ya yi mata, duk da wani sashe na zuciyarshi yana ba shi cewa ko kaɗan bai yi laifi, don yanda ya ƙagu da yasan inda Khadijarshi take komi zai iya aikatawa akan wanda ya ke so ya toshe masa ƙofofin da da zasu sadashi da farin cikinshi.

Sannu a hankali ya ƙaraso wajen wayarshi da ke tarwatse har lokacin, ya duƙa ya ɗauki kangalwar wayar ya zare sim cards ɗinshi sannan ya saka cikin wata sabuwar wayar da ya siyo, sai dai baƙin cikin rashin saving ɗin numbar Dijen da bai yi ba tun farko yasa ya dannawa Hajiyarshi kira, bayan sun gaisa ya marairece murya ya ce

"Haba Hajiyarmu plss don ALLAH ki sanar da ni inda aka kai Khadija, saboda jikina yana bani cewa ba aikatau Khadija ta je ba, don ALLAH ki tausaya man Hajiyarmu ki bani matata WALLAhi ina sonta sosai"

Hajiya Mama ta yi shiru sannan ta ce

"Ka kwantar da hankalinka duk lokacin da ka dawo ƙasar nan insha ALLAHu zaka taradda kHadija a gidanka zaune tana jiran dawowarka"

Cike da tsananin jin daɗi ya ce "in dai haka ne to ni ai sai in tattaro kayana kawai in dawo gida Hajiyarmu"

Ta ɓata fuska kamar tana ganinshi ta ce "shi karatun na ka idan ka dawo wa zai ƙarasa maka shi ne?bayan saura lokaci kaɗan ka kammala"

Safwan ya sosa kanshi yana murmushin jin daɗi ya ce "to Hajiyarmu me zai hana ayi mata viza kawai ta samemu anan ɗin ta tayamu zaman, kin ga in mun kammala sai mu dawo gida tare gaba ɗayanmu?"

Hajiyar ta yi ƴar dariya sannan ta ce "ita kuma karatun nata fa? Sai ta ajiye ta zo ta tayaku naku karatun kenan? to bari ka ji idan ka kawo wasa ko ka dawo bazan bari ka ganta ba, matuƙar baka natsu ka ƙare karatunka da ya rage saura ɗan lokaci ba"

Safwan ya durƙusa ƙasa kamar a gabanta  ya ce "plss Hajiyarmu don ALLAH ko numbar da zan sameta ne a bani plss sai mu dinga gaisawa, don wallahi rashin jinta zai iya janyo inyi asarar duka shekarun da na ɓata a baya wajen karatun"

Hajiya ta yi shiru sannan ta ce "zan baka numbar khadija amman da sharaɗin bazaka tambayeta inda take ba har sai ka jira na sanar da kai da kaina, kuma ko da ka gano daga baya ba zaka ga laifin wadda take wurinta ba don Ni na bata khadija da hannuna"

Cikin zumuɗi ya ce "bani numbar kawai Hajiyarmu wannan duk mai sauƙi ne in dai har na sami number'rta"

Ba ɓata lokaci Hajiyar ta saka Fiddo ta yi masa sending number'r ta whassapp cike da zumuɗi ya yi Saving ɗinta a cikin wayarshi sannan ya danna mata kira.

Dije kam kasancewar bata nan tana school saboda lokaci ba ɗaya ba, kuma ga wayar ma a kashe take shiyasa ya yi kira ya kai hamsin amman bai sameta ba, cike da jin zafin hakan da takaici ya yi kwanciyarshi akan kujera ya ƙi zuwa wurin Zee da tunda suka yi aure basu taɓa raba wurin kwanciya ba sai ranar, haka wanibacci mara daɗi  ya fisgeshi mai ɗauke da mafalkin khadijar saboda tunaninta ne a zuciyarshi har baccin ya yi awon gaba da shi.

Zee cikin bacci ta shafo gadon ta ji wayam ba kamar kullum yanda ta saba shigewa jikinshi tana shagwaɓa ba, ta yi saurin buɗe idonta tare da kaiwa kan gadon kallo sai gata da miƙewa zaune ba shiri, cikin mamakin sababbin halayen da ya tsiro mata ta sauko gadon ta fito falon, in da ta hangoshi kwance da alamu ma baccin yake yi, nan take wani kuka ya zo mata ta janyo ƙafafuwanta ta ƙaraso bakin kujerar ta yi duƙuso, sannan ta ɗora kanta saman ƙirjinshi ta fara kuka ƙasa ƙasa, cikin bacci ya jiyo sautin kukanta ba shiri ya buɗe ido tare da shafo kanta da ke saman jikinshi, ya yi shiru yana sauraren kukan nata ba tare da ya ce da ita ƙanzil ba, ganin ta ƙi daina kukan ne ya yi dubarar cire kanta ya miƙe zai bar wajen ta yi saurin riƙo ƙafarshi ta ce

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now