*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*BAK'ON YANAYI BOOK NE MAI ZAFI HAR KUNA YAKE YI A HANNU SABODA TSABAR TSANANIN ZAK'INSHI BOOK D'IN BAK'ON YANAYI SALONSHI DABAN NE DA KOWANE BOOK DA KA TAB'A KARANTAWA A DUNIYAR LITTAFAI, ZAKU SAMESHI A ARHA DA FARASHIN NERA D'ARI UKU KACAL KUMA ZAKU SAMESHI A COMPLETE DINSHI CIKAKKE MAI B'UKATA TA NEMENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 SAYEN NA GARI MAYAR DA KUD'I GIDA SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI👍🏻 DOMIN KUWA BAK'ON YANAYI DAUKE YAKE DA NASHI KALAR SALO KALA KALA KUMA MABANBANTA MASU BURGE MAI KARATU DA SAKASHI SHIGA CIKIN SHAUKI YAYIN KARANTAWA💃🏻*
*Lamba ta 7*
Aiko Dije har safe ko motsin kirki bata sake yi ba saboda ta tsorata da jan kunnen da Inna ta yi mata, don hasali ma har mafalki ta yi wai gasunan sun bayyana da siffarsu sun zo wurinta zasu kasheta, cikin firgici ta falka a zabure tana fad'in
"Don ALLAH kuyi hakuri bazan sake ba na tuba nabi ALLAH da manzonshi, amman in har kunga na sake to ku d'auki mataki"
Inna da ke shigowa d'akin ta d'auro arwallar sallahr Asuba da nufin ta tada ita sai gashi ta taradda ita zaune tsakiyar gado tana sambatu, Inna ta kalleta da kyau tace
"Lafiyarki tun da safe kike yiwa mutane soki burutsun zance?"
Dije ta waiga gefe da gefenta sannan ta fara saukowa gadon tace,. 'ba komi"
INNA ta bita da kallo har ta fice d'akin ta girgiza kai sannan ta shimfida wata sabuwar tabarmar kaba da suke sallah akai ta tada sallahrta.
Dije kam har ta k'are arwallar ta dawo d'akin tunanin mafalkin take yi, jikinta a sanyaye ta yi sallah ta gayar da Inna sannan ta fara bitar karatunta na allo, Inna cikin jin dad'in ganin sauyin Dije ta bita da addu'ar ALLAH yasa abun ya dore a haka, don dai ita jikinta yana bata ko dai da gaske Dijen akwai wasu k'wank'wammai akanta masu sakata jidali da yawan fad'ace fad'ace kullum?, Ta fice zuciyarta cike da jin dad'i ta yi madafi domin ta d'ind'ima masu tuwon da zasu karyawa dashi.
Dije Kam tana k'are bitar karatunta ta jingine allonta ta nufi d'akin Baffah domin ta yi mashi Ina kwana, aiko sai gashi sunyi kicib'is da Usman ta ja baya ya shige d'akin sannan ta bi bayanshi da harara ta shige d'akin itama, Baffah yana kishingide da carbi a hannunshi yana ja yana gyangyadi, jin sallamar Usman yasa ya yi saurin tashi zaune yana amsa masa sallamar fuska a d'aure, ganin Dije a bayanshi yasa ya saki fuskarshi da fara'a tana shirin zama nesa dashi yayi saurin fad'in,. "Matso nan kusa da ni Dijengalata ya jikin naki?"
Dije ta zunburo Baki tace,. "Naji sauk'i sai dai dukan da Yaya Usman yayi mani ashe duk ya farfasa man jikina kallo ka gani Baffah"
Ta k'are maganar tare da zubowar wasu kwallah tana nuna masa tsintsiyar hannunta inda shatin bulalar ya fito rad'am.
Baffah ranshi ya K'ara b'aci cikin d'aure fuska yace da Usman da ke k'ok'arin gayar dashi yace,. "Ajiye gaisuwarka bana so tunda har baka ji kunyar saka bulala ka yiwa Dije irin wannan dukan ba, don tsabar rashin imani Innarku ta daketa da dare ace wai kaima ka bita tsakar dare da dukan kawo wuk'a, to bari kaji muddin ka sake yi mata irin wannan dukan WALLAHI sai na sab'a maka, don nafi son Ni in illataka da hannuna da dai ace Yariman Aljanu ya kawo maka farmaki, don ko Hasiya ALLAH ne ya tsareta da yau bata tashi da idanuwanta ba, duk kuma akan dukan da tayiwa Dijen, Kai ma ka kiyayi kanka da tsokano fushin d'an Gidan mai martaba"
Usman yayi saurin toshe dariyarshi yace,. "WALLAHI Baffah k'arya take yi ba wasu aljanu don da idona na ganta jiya tana rera waka tana dukan rufin madafinmu"
Baffah ya galla masa wata jar harara yace,. "To ka godewa ALLAH da har siffarta ka gani a jiki ba siffarsu ba, to bari kaji Kai kanka zasu iya yin siffarka suje inda suke so bale ta Dijen"

YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
Tiểu Thuyết ChungLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.