43

361 27 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Domin farin cikinku kawai mutanena😅*

*Lamba ta 43*

Dije dunƙule kan gado tana kuka ta ji an dafa kanta cikin sauri ta goge hawayenta ta ɗago fuskata, aiko caraf ta yi ido huɗu da Hajiya Mama fuskarta ƙumshe da damuwa, ta yi jarumtar washe bakinta guntayen hawayenta da suka maƙale suka faɗo, cikin basarwa tace

"Me aka yi maki Hajiyata?"

Hajiya ta sake dafa kanta ta shafo dogon gashinta tace,. "Naji komi Surayya ta faɗa man ki yi haƙuri ki barni da shi ai zai zo garin ya sameni ina jiranshi"

Dije ta yi saurin faɗin

"Ki ƙyaleshi kawai Hajiya Ni na haƙura da duk abunda ALLAH ya ƙaddaro man, haka kuma ma zan yi biyayya ga duk abunda kika umurceni"

Hajiya Mama cike da jin daɗin canjin da Dijen ta samu a wurinsu tace,. "Ki yi ƙoƙari ki nuna masa cewa fa ke ma mace ce duk runtsi kada ki bada wata ƙofa da shi ko yarinyar zasu renaki"

Dije ta ɗaga kanta alamun gamsuwa Hajiyar ta riƙo hannunta tace, " saki jikinki ki koma ku je kuci gaba da shirye shiryenku, ki yi kamar daman cen komai bai faru ba"

Sai da tasata ta je toilet ta wanko fuskarta sannan suka fito tare.

Haka aka ci gaba da hada hadar tare da Dijen duk da zuciyarta ba daɗi amman hakan bai hanata nuna annushuwa kan fuskarta ba, sai dai kuma Fiddo tasha jinin jikinta saboda faɗan da Hajiya Mama ta yi mata akan abinda ta yi a gaban Dijen, duk da ta ci alwashin bazata fasa nuna ƙaunar budurwar Safwan ba ko don Dijen ta ji haushi.

Ana saura kwana huɗu bikin ne Safwan ya diro Nageria tare da budurwarshi, sai dai ita ta yi garinsu sai taga gida sannan ta zo bikin daga baya, a ranar da ya diro gidan da marece za'a je yin wani event mai suna tea party, duka Amarya da ƙawayenta da ma ita kanta Dijen da Fiddo duka sunyi shigar wani yadi milk da kalar cofee, kowacensu ta sha makeup irin na classic ladys masha ALLAH gwanin burgewa, har sun shishiga motoci ne aka manta da agogon Amarya akan stool ɗakinsu, shine Dijen ta fito ta koma cikin sauri da nufin ta ɗauko ta dawo ana jiranta su tafi.

Ta ɗauko agogon ta fito kenan a tsakiyar babban falon suka yi karo har tana ƙoƙarin faɗuwa, cikin sauri ya riƙota ta faɗo jikinshi tare da riƙeta ƙam ƙam don kar ta faɗin, jikinta yana ɓari ta yi saurin kai kallonta gareshi saboda turaren da ta ji ya tabbatar mata da cewa shi ne, ido cikin ido suka kalli juna dukansu a lokaci ɗaya gabansu ya faɗi ras! ras!, Cikin sauri ya saketa duk da bai tabbatar da cewa ita ɗin ce ko ba ita ba, itama kanta ta aro wata jarumta ta yi kamar ma bata taɓa ganinshi ba ta duƙa ta ɗauki agogon da faɗi  ta fara taku a hankali cikin wani salon da ita kanta batasan ta iya irinshi ba ta fice, Safwan ya bi bayanta da kallo har ta ɓacewa ganinshi amman bai daina kallon ƙofar ba, cikin wani hargitsatstsen yanayi  ya ja jakarshi ya nufi ɗakin Hajiya Mama, don gidan shiru saboda mutane da yawa sun tafi partyn.

Dije kam har ta shiga motar suka tafi ƙirjinta bai daina bugawa ba, saboda ganin bazatan da ta yi masa duk da daman cen tasan da zuwan nashi a ranar.

Sun gudanar da bikinsu masha ALLAH ansha rawa  Amarya da Angonta sun gwangwaje tare da abokan ta da yan uwa da abokan arziƙi, Dije ma ba'a barta a baya baya bayan photunan da aka sha kala kala kowace da kalar nata salo ba ƙarya.

Bayan an watse taron ne wani ya biyo Dije har gida saboda tun a cen wajen ta ɗauki hankalinshi sosai, yana biye da komi nata har suka dawo gidan, suna ƙoƙarin kwasar wasu kaya ne a bayan boot ya yi mata sallama.

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now