*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*BAK'ON YANAYI LITTAFI NE MAI ZAFI 300 KACAL ZA TA MALLAKA MAKI SHI MAI BUKATA TA TUNTUB'E NI TA WANNAN NUMBER 09032685442*
*Lamba ta 15*
Tun daga Ranar Dije ta yi sukuku da ita don daga Baffah har Inna sun daina sakewa da ita, daman cen shi Usman ba wani shiri suke yi da ita Sosai ba, Dije cikin dabara ta dinga makalewa gidan Inna Gambo, don wani zubin ma dawowarta Makarantar bokon ke da wuya take tafiyarta gidanta ko Makarantar allonsu daga cen ta ke zuwa, INNA kanta ta fi sha'awar zuwanta Gidan da dai ace taje ta yi ta janyo masu abun magana, duk da ko ita Inna Gambon ana nuna mata halin watarana, saboda muddin ta kawo mata Abinci bata bata nera biyar d'in da take bata kullum ta kawo mata tuwon ba, to ko ko da ta ajiye tuwon sai ta dawo tace
"Inna Gambo kinji Innata tace in babu biyar d'in to a bada tuwon"
Wani zubin ta hanata d'aukar tuwon watarana kuma tace da ita,. "D'auki tuwonku ki kaiwa duk wanda kike so tunda daman cen ba don ALLAH kike kawo man ba"
Watarana kuma ta jefa mata nera biyar d'in tace,. " D'auki gata nan amman ki sani gobe kar ma ki kawo man tuwon don bana so "
Dije sai ta d'auke biyar d'in sannan ta dawo tana kalailameta da dad'in baki, Sabida gyaran hanya har shara da wanke wanke sai ta yi mata, sannan ta dinga debo mata ruwa tana cika mata tukanenta da tulunanta na ruwa.
Inna Gambo da Dije in sun had'u wajibi ne ma sai ka yi dariya saboda yanda suke tsarguwar junansu, musamman dai ita Gambo da kullum ta ke yiwa Dije kirari da cewa
"Alhudahuda Sarkin karatu sillen kara ta Ummaru Sanda, sarka mai rikicin gan gan, in kin so ayi ta morarki in kuma kin k'i ki fad'i ki rikice a rasa gano kanki, Dijengala ta megari Dije ba auren talaka ba talaka noma da sassabe, ALLAH ya kai mu inga aurenki ko don in baiwa Mijinki gudunmuwar bulala"
Dije kam in Gambo tana yi mata kirarin har wani tsallen jin dad'i take yi tana rufe ido wai ita kunya, to dai kam wannan karon ko ita Gambon ta gano damuwar da Dijen take ciki, saboda zaunenta ta ke yi ta yi ta karatunta duk wata kiriniya ajiyeta ta yi ta koma sukuku da ita.
Hankalinta bai kwanta ba sai ranar da ta je Makarantar ta hango Malam Safwan, cikin sanyin jiki ta isa wurinshi ta gayar da shi ta wuce ajinsu, duk da bai amsa ba amman ta ji dad'in ganin ya mirmije daga ciyon dolen da ta sakashi.
SAFWAN kam binta yayi da kallon tsana tamkar ya janyota yayi ta jibga yake ji, amman tsoron sharrin da zata sake kulla masa yasashi yin alk'awalin ba zai sake biyeta ba, ballantana har watarana ta janyo masa bala'in da bai san ta inda zai taroshi ba, karatu dai ne ya zama dole to zai yi masu amman kam yasa a ranshi ba zai sake shiga shirginta ba.
Ta bangarenta ne da kawayenta suka yanke shawarar kai kararshi wajen shugaban Makarantar, saboda basu fahimtar karatunshi sabida tsagwaron turancin da yake ta zuba masu, har za su fita Dije wani tunani ya zo mata a rai tace da su
"Ku tsaya kuji wata shawara in kun amince mu ma mu dinga buga masa turancinmu na hauka ko da ba dai dai muka yi ba, ya fi dai da ace mu kai kararshi ya zo ya kara renamu"
Ladiyo ta rik'e hab'a tace,. "Ke Dije to in ke kin iya turancin mu ai bamu iya komi ba"
Dijen ta kyalkyale da wata dariya sannan tace,. "In kun amince Littafin da nake dubawa ina hardace sunayen abubuwa zan fara koya maku shi ku ma, ko don mu dinga haukatashi da turancinmu saboda if you had'a turanci da Hausa to no body kan k'ureka da shi"

YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
Fiksi UmumLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.